Musulunci Ya Yi Rashi: Babban Malami Ya Kwanta Dama a Kano
- Jihar Kano ta shiga cikin alhini bayan tabbatar da rasuwar fitaccen malamin addini, Malam Kabiru Ibrahim Madabo, wanda ya rasu a yau Alhamis
- Sheikh Anas Mahmud Madabo ne ya tabbatar da rasuwar malamin, yana bayyana cewa al’umma sun yi babban rashi a bangaren ilimi
- Majiyoyi sun bayyana lokacin sallar jana’izar Malam Kabiru Madabo da aka shirya yi a fadar Sarkin Kano, kafin a kai shi maqabartar Madabo
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Rahotanni da muka samu yanzu sun tabbatar da cewa duniyar Musulunci ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar malamin addini.
Jihar Kano za ta shiga jimami bayan tabbatar da rasuwar malamin mai suna Kabiru Ibrahim Madabo a yau Alhamis 9 ga watan Oktobar 2025.

Source: Facebook
An sanar da rasuwar Malamin Musulunci a Kano
Shekh Anas Mahmud Madabo shi ya tabbatar da haka a daren yau Alhamis a shafinsa na Facebook inda ya nuna alhini kan rashin da aka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Madabo ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne a yau Alhamis 9 ga watan Oktobar 2025 bayan sallar La'asar a Kano.
A cikin rubutunsa, Sheikh Madabo ya ce:
"Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un, Allah ya yi wa babanmu babban malami Namadabo rasuwa Malam Kabiru Ibrahim Madabo yanzu bayan la'asar, 9 ga watan Oktobar 2025.
"Za a yi sallar jana'izarsa gobe Juma'a 10 ga watan Oktobar 2025 idan Allah ya kaimu da misalin karfe 10:00 na safe a gidan Mai Martaba Sarkin Kano da ke Kofar Kudu.
"Sannan za a kai shi maqabartar kusa da sansanin masaukin alhazai (MAQABARTAR MADABAWA).
"Allah ya jikansa ya yi masa rahama."

Source: Original
Yaushe za a yi jana'izar marigayin?
Shafin Sanusi II Dynasty ma ya tabbatar da rasuwar malamin a shafin Facebook tare da yi masa addu'ar samun rahama a gobe kiyama.
Sanarwar ta tabbatar da cewa za a yi sallar jana'aizar marigayin gobe Juma'a 10 ga watan Oktobar 2025 a kofar Sarkin Kano.
A cewar sanarwar:
"Innā lillāhi wa innā ilaihi rāji‘ūn, Allah Ya yi wa babban malami na Madabo, Malam Kabiru Ibrahim Umar rasuwa.
"Za a gudanar da jana’izarsa gobe da misalin ƙarfe 10:00 na safe a Kofar Kudu, Fadar Sarkin Kano.
"Allah ya jikan sa, ya gafarta masa."
Wannan mutuwa ta gigita al'ummar Kano yayin da mutane da dama ke jimamin rasuwar tasa da kuma yi masa addu'ar samun rahama.
Unguwar Madabo ta yi fice a tarihi da samun manyan malaman musulunci a Kano kuma har yanzu akwai fitattun shehunnai daga yankin.
Wani malamin Musulunci a Kaduna ya rasu
Mun ba ku labarin cewa babban limamin masallacin Juma'a na SMC da ke garin Kaduna, Sheikh Imam Sa'id Abubakar ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 2 ga Oktoba, 2025.
Majalisar Limamai da Malamai ta jihar Kaduna ta tabbatar da rasuwar malamin a wata sanarwa da ta fitar, ta ce ya cika ne da asubah.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni dai aka yi jana'izar marigayin da misalin karfe 1:00 na rana bayan Sallar Azahar kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


