IBB, Abdulsalami Sun Halarci Taron Majalisar Koli, Karon Farko babu Buhari
- Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci zaman majalisar kolin Najeriya a fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025
- Wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da taron majalisar ba tare da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, tun daga 2015
- Majalisar ta amince da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A yau Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025, Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci zaman majalisar kolin Najeriya, a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Wannan ne karon farko da aka gudanar da taron majalisar kolin ba tare da Shugaba Muhammadu Buhari ba, tun bayan fara mulkinsa a 2015.

Source: Facebook
Shugabannin da suka halarci taron majalisar koli
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an fara wannan taron ne da misalin karfe 1:29 na rana, a zauren majalisar zartarwa ta kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin kusoshin Najeriya da suka halarci taron akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Hakazalika, akwai tsofaffin shugabannin kasa, Abdulsalami Abubakar da Ibrahim Badamasi Babangida da suka halarci taron ta yanar gizo.
Amma daga cikin wadanda suka halarta kai tsaye, akwai sakatarin gwamnatin tarayya, George Akume; mai ba Tinubu shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu; Antonji Janar na kasa, Lateef Fagbemi (SAN) da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamilla.
Akwai kuma shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas da wasu gwamnoni da dama, yayin da wasu gwamnoni suka samu wakilcin mataimakansu.
Majalisar koli ta zabi sabon shugaban INEC
A yayin taron ne majalisar kolin ta amince da nadin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) a matsayin sabon shugaban hukumar INEC.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan
'Babban dalilin da ya sa na zabi Amupitan, shugaban INEC': Tinubu ya fadi hikimarsa
Shugaba Tinubu ya gabatar da sunan Amupitan ga majalisar, domin ya maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya cika wa'adinsa na shekara 10.
Shugaban kasar ya sanar da majalisar cewa Amupitan, dan shekara 58, ya kasance farfesa a fannin dokoki a jihar Kogi, kuma shi ne jihohin Arewa ta Tsakiya suka gabatar.

Source: Twitter
Taron majalisar koli ba tare da Buhari ba
Wannan taro na yau Alhamis, shi ne taron da aka gudanar na farko ba tare da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, wanda ya rasu a watanni baya.
Tsohon Shugaba Buhari ya kasance yana halartar taron majalisar a lokacin mulkinsa, kuma ya kasance yana halartar taron ko bayan barin mulki.
Kafar watsa labaran BBC ta rahoto cewa Buhari na daga cikin wadanda suka halarci taron majalisar na 2024, kuma halartarsa ta karshe, inda ya yi magana kan muhimmancin bin ka'ida a tsarin kashe kudi.
Taron dai na yau ya nuna yadda gwamnatin Bola Tinubu take kokarin shirya zabukan kasar mai zuwa da kuma kokarin samar da tsaro.
Dalilin Tinubu na ba Amupitan shugabancin INEC
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya bayyana dalilin zabar Farfesa Joash Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar INEC.
Tinubu ya bayyana cewa ya zabi Farfesa Joash Amupitan ne saboda gaskiyarsa, rashin shigar sa cikin siyasa, da kuma kyakkyawan tarihin da yake da shi.
Amupitan shi ne mutum na farko daga Jihar Kogi da aka taba nada wa mukamin shugaban INEC, kuma zai maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

