Ana Sa Ran Tinubu Ya Fadi Sabon Shugaban INEC a Zaman Majalisar Koli

Ana Sa Ran Tinubu Ya Fadi Sabon Shugaban INEC a Zaman Majalisar Koli

  • A yau Alhamis, 9 ga watan Oktoba, 2025 ne Shugaban Kasa, Bola Tinubu zai jagoranci zaman majalisa da za a gudanar a Abuja
  • Ana sa ran a zaman na yau, Shugaba Tinubu zai bayyana magajin Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin Shugaban INEC ta kasa
  • Rahotanni sun bayyana cewa matukar komai ya tafi yadda aka tsara, Shugaban Kasa na da wanda zai bayar da sunansa, a tantance shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Ana sa ran Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da sunan wanda zai zama sabon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Rahotanni sun bayyana cewa Shugaban zai jagoranci zaman Majalisar Koli ta Ƙasa a yau, Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025, a Fadar Shugaban Ƙasa, Aso Rock, Abuja.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

Shugaban Kasa zai jagoranci zaman Majalisar Koli a yau
Hoton Shugaba Bola Tinubu, Farfesa Amupitan Hoto: @OfficialABAT, @unijos / X
Source: UGC

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wannan matakin na zuwa ne yayin da wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC na yanzu, ya kare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin shugaban kasa na farar hula da na mulkin soja, tsofaffin alkalin alkalai suna cikin wadanda za a yi zaman majalisar kolin da su a yau.

Tsohon Shugaban INEC ya ajiye aiki

Kafar Arise ta wallafa cewa a ranar Talata, 7 ga Oktoba, Farfesa Mahmood Yakubu ya mika ragamar aiki ga Dame May Agbamuche-Mbu, babbar kwamishina mafi girma a hukumar.

Daga cikin wadanda ake gani za su iya maye gurbinsa, sunan Farfesa Joash Ojo Amupitan ne aka fi zama wanda ake ganin zai 'dare kujerar.

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai bayyana sunan sabon Shugaban INEC
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Majiyar fadar shugaban ƙasa ta shaida wa jaridar cewa an riga an yi wa Farfesa Amupitan tantancewar tsaro gabanin bayyana sunansa.

Kuma a halin yanzu, shi ne Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos (UNIJOS) mai kula da harkokin gudanarwa.

INEC: Waye Farfesa Joash Ojo Amupitan?

Kara karanta wannan

Farfesa Mahmood: Daga ajiye aiki, kotu ta bada umarni a kamo mata tsohon shugaban INEC

Farfesa Joash Ojo Amupitan ya fito ne daga Aiyetoro-Gbede da ke cikin Karamar Hukumar Ijumu ta Jihar Kogi.

An haife shi a ranar 25 ga Afrilu, 1967, kuma ya shahara a fannin shari’ar da gudanarwa da dokar kasuwanci da sauransu.

Ya shafe shekaru da dama yana koyarwa a jami’a, kuma yana da ƙwarewa a fannoni da dama na dokar kasa, kamar yadda ya samu horo.

Dokar kasa ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima, ta tsara yadda aka kafa hukumar INEC da yadda za a nada jami'anta.

Daga cikin sharuddan, dole ne a samu tattaunawa da Majalisar Koli ta Ƙasa kafin gabatar da sunaye, sannan Majalisar Dattawa za ta tabbatar da su.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood ya ajiye aiki

A baya, mun wallafa cewa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi murabus daga kujerarsa bayan ya kammala wa’adinsa.

A ranar Talata, 7 ga watan Oktoba 2025, Yakubu ya mika ragamar jagoranci ga Dame May Agbamuche‑Mbu, wadda ta zama mace ta farko da ta taba rike wannan kujera.

Kara karanta wannan

'Jonathan, Atiku da Peter Obi ba za su iya doke Shugaba Tinubu a zaben 2027 ba'

ayin mika aikin, ya jaddada cewa wannan lamari zai bai wa wanda zai gaje shi damar fara shirye-shiryen gudanar da zaɓukan ƙasa cikin nutsuwa da tsari kafin 2027.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng