2026: An Saki Jerin Jami'o'i 50 Mafi Nagarta a Najeriya, BUK da ABU Sun Fafata
- Rahoto ya ce Jami’ar Ibadan ta zama jami’a mafi nagarta a Najeriya a jadawalin Times Higher Education na shekarar 2026
- Jami’ar ta koma kan gaba daga matsayi na hudu a 2025, inda ta doke jami'ar Covenant da ta yi nasara a 2024 da 2025
- Jadawalin ya nuna cewa jami’o’i 50 ne daga Najeriya da suka shiga cikin jadawalin, ciki har da jami'o'in BUK da ABU Zariya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jami’ar Ibadan (UI) na kan kololuwar jadawalin mujallar Times Higher Education (THE) a 2026, inda ta zama jami’a mafi daraja a Najeriya.
An wallafa rahoton ne a ranar Alhamis, inda aka nuna cewa jami’ar Ibadan ta samu matsayi tsakanin 801 zuwa 1,000 a duniya.

Source: Facebook
A sakon da aka wallafa a shafin mujallar, an bayyana cewa jami'ar BUK da ABU Zariya na cikin wadanda suka taka rawa a bana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matakan tantance jami'o'in duniya
Rahoton ya bayyana cewa jami’ar Ibadan ta samu nasarar zama mafi daraja ne bayan tantance jami’o’i 2,191 daga ƙasashe 115 a fadin duniya.
An kimanta jami’o’in ne bisa fannoni biyar: yanayin koyarwa, muhalli da ingancin kayan bincike, hulɗa da masana’antu da gogayya a duniya.

Source: UGC
Jami’o’in da suka biyo baya a Najeriya
A jadawalin shekarar 2026, Jami’ar Legas (UNILAG) ta zo ta biyu, Jami’ar Bayero (BUK) ta zo ta uku.
BUK ta samu karramawa a matsayin jami’ar da ta fi kwarewa wajen hulɗar ƙasa da ƙasa, yayin da Jami'ar Covenant ta yi fice a fannin hulɗar masana’antu da kasuwanci.
Jerin jami'o'in da suka yi fice a Najeriya:
1. Jami’ar Ibadan
2. Jami’ar Legas
3. Jami’ar Bayero, Kano
4. Jami’ar Covenant
5. Jami’ar Landmark
6. Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya
7. Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Minna
8. Jami’ar Ilorin
9. Jami’ar Jos
10. Jami’ar Najeriya, Nsukka
11. Jami’ar Babcock
12. Jami’ar jihar Delta, Abraka
13. Jami’ar jihar Ekiti
14. Jami’ar Aikin Noma ta Tarayya, Abeokuta
15. Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Akure
16. Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Owerri
17. Jami’ar Tarayya, Oye-Ekiti
18. Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola
19. Jami’ar jihar Legas
20. Jami’ar Nnamdi Azikiwe
21. Jami’ar Obafemi Awolowo
22. Jami’ar Binin
23. Jami’ar Kalaba
24. Jami’ar Fatakwal
25. Jami’ar Admiralty ta Najeriya
26. Jami’ar jihar Akwa Ibom
27. Jami’ar Al-Hikmah
28. Jami’ar Augustine
29. Jami’ar Ilimi, Kimiyya da Fasaha ta Bamidele Olumilua, Ikere-Ekiti
30. Jami’ar jihar Bauchi, Gadau
31. Jami’ar Likitanci ta jihar Bayelsa
32. Jami’ar Baze
33. Jami’ar Fasaha ta Bells
34. Jami’ar Bowen
35. Jami’ar Evangel, Akaeze
36. Jami’ar Tarayya, Lafiya
37. Jami’ar Albarkatun Man Fetur ta Tarayya, Effurun
38. Jami’ar Fountain
39. Jami’ar Godfrey Okoye
40. Jami’ar Igbinedion, Okada
41. Jami’ar jihar Kaduna
42. Jami’ar Ilimi ta jihar Legas
43. Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jihar Legas
44. Jami’ar Lead City
45. Jami’ar Maryam Abacha American ta Najeriya
46. Jami’ar jihar Nasarawa, Keffi
47. Jami’ar Redeemer’s
48. Jami’ar jihar Rivers
49. Jami’ar Thomas Adewumi
50. Jami’ar jihar Cross River
Jami'o'in Najeriya za su fara yajin aiki
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar malaman jami'a a Najeriya, ASUU ta fara shirin tafiya yajin aiki.
Rahotanni sun nuna cewa kungiyar za ta fara yajin aiki ne saboda wasu hakkokinsu da suka ce an gaza biya.
Gwamnatin tarayya ta fara maganar shawo kan malaman domin kaucewa rufe jami'o'i amma suna cewa ba ja da baya idan ba a biya su ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


