Durkusa wa Wada: Gwamnatin Tinubu Ta Roki ASUU, Ta Dauki Sabon Alkawarin Hana Yajin Aiki
- Gwamnatin tarayya ta roƙi kungiyar malaman jami'o'i ta kasa, ASUU da ta dakatar da yajin aikin da ta ke shirin fara wa a Najeriya
- Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya taushi kungiyar malaman, inda ya ce ana ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin ASUU
- ASUU ta ba gwamnati wa’adin kwana 14, kuma idan ba a biya buƙatunta ba, za a fara yajin aiki na gargadi kafin a dauki mataki na gaba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta roƙi ƙungiyar malaman jami’o'i ta kasa (ASUU) da ta janye shirin fara yajin aikin gargadi da ta ke kan yi yanzu.
Gwamnatin ta baiwa kungiyar tabbacin cewa ana aiki tukuru don warware duk buƙatun da ASUU ta gabatar mata sannu a hankali.

Source: Twitter
Channels TV ta wallafa cewa Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ta ba ASUU hakuri
Tribune Online ta ruwaito cewa Tunji Alausa ya ce gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da matakan sulhu da ƙungiyar domin a taka wa yajin aiki burki.
Ministan ilimin ya kara da cewa ana kuma samun cigaba mai kyau a cikin tattaunawar da ke gudana tsakanin bangarorin biyu.

Source: Facebook
Mista Alausa ya bayyana cewa an sake kafa Kwamitin Mahmud Yayale Ahmed da ke tattaunawa da manyan cibiyoyin ilimi domin a samu mafita.
Ya ce kwamitin zai yi aiki domin saurin shawo kan matsalolin da suka shafi malamai da sauran ma’aikata a jami’o’i, kwalejin ilimi da kuma manyan makarantu na fasaha.
ASUU: Kungiyar malaman jami'a ta fusata
Ministan ilimi a Najeriya, Tunji Alausa ya ce Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarni kai tsaye cewa a yi duk mai yiwuwa domin guje wa sake samun tsaiko a ilimin kasar nan.
A halin yanzu, ASUU ta fara shirye-shiryen cikakken yajin aiki na gargadi, domin wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati zai ƙare ranar Lahadi.
ASUU ta yanke shawarar fara yajin aikin gargadi ne bayan taron majalisar koli ta ƙasa (NEC) da aka gudanar a Jami’ar Abuja ranar Lahadi da ta gabata.
Cikin wata sanarwa da shugaban ƙasa na ƙungiyar, Chris Piwuna, ya sanya wa hannu, ASUU ta zargi gwamnati da watsi da bukatun malamai, an bar su da wahala.
Sanarwar ta ce:
“A watan Agusta 2025, 'yan kungiyar ASUU sun gudanar da zanga-zanga a jami’o’in jihohi da na tarayya domin nuna damuwa kan halin da tsarin ilimi ke ciki, amma ba a dauki wani mataki ba.”
ASUU ta yi wa gwamnati barazana
A baya, mun wallafa cewa ASUU ta yi wata barazana na fara yajin aiki idan har gwamnatin tarayya ta kasa magance bukatunta a cikin wa’adin kwanaki 14 da ta bayar a baya.
Wannan sanarwar ta zo ne bayan taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) da aka gudanar a Jami’ar Abuja a kan bukatun da su ke da shi ga gwamnatin tarayya na tsawon lokaci.
Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Chris Piwuna, ya ce gwamnati tana “yin kunnen uwar shegu” game da matsalolin da su ka dabaibaye kungiyar, duk da ana kai mata koke.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


