Tinubu Ya Gabatar da Manyan Bukatu 5 ga Majalisa, Zai Nada Shugabannin Hukumomi

Tinubu Ya Gabatar da Manyan Bukatu 5 ga Majalisa, Zai Nada Shugabannin Hukumomi

  • Majalisar dattawa ta rantsar da sababbin sanatoci biyu; Joseph Ikpea daga Edo da Emmanuel Nwachukwu daga Anambra
  • A yayin zaman majalisar, an karanta wasiku daga Shugaban Bola Tinubu kan bukatar amincewa da nadin wasu mukamai
  • Muhimman bukatu biyar da Tinubu ya gabatar wa majalisar a ranar Laraba sun hada da nadin shugaban hukumar NPC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A zaman majalisar dattawa na ranar Laraba, 8 ga watan Oktoba, 2025, shugaban majalisa ya rantsar da sababbin mambobi biyu.

Sanata Godswill Akpabio ya rantsar da sababbin mambobin ne da aka zaba a watan Agusta, 2025 zuwa majalisar dattawa ta 10.

Majalisar dattawa ta karanta wasikun da Shugaba Bola Tinubu ya aike mata
Sanata Godswill Akpabio na jagorantar zaman majalisar dattawa a Abuja. Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Sababbin sanatocin sun haɗa da Joseph Ikpea, (Edo ta Tsakiya), da Emmanuel Chibuzor Nwachukwu, (Nnewi ta Kudu), inji rahoton shafin NALTF.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga sahun masu neman fito da shugaban kungiyar ta'addanci da aka kama tun 2021

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya aikewa majalisar dattawa wasiku

An ruwaito cewa sababbin sanatocin za su shiga ayyukan majalisar dattawa kai tsaye bayan kammala shirin karɓar mukami da rantsuwa.

A zaman majalisar, Akpabio ya karanta wasu wasiku daga Shugaba Bola Tinubu da ke neman amincewar majalisar akan wasu muhimman batutuwa:

1. Bukatar karbo rance daga waje

Shugaban kasa ya aiko da buƙata kan karbo rancen kudi daga ƙasashen waje, wanda aka mika ga kwamitin lamunin gida da waje, tare da umarnin kawo rahoto cikin mako guda.

2. Nadin kwamishinoni a hukumar NCC

Wasikar ta gabatar da sunayen kwamishinoni tara na hukumar sadarwa ta kasa (NCC) da ya ke so a tantance tare da amincewa da nadinsu.

Sanata Akpabio ya mika takardar bukatar zuwa ga kwamitin majalisa kan sadarwa, wanda ake sa ran zai bada rahoto cikin mako biyu.

3. Nade-nade a hukumar FSC

Shugaban kasa ya kuma aiko da sunayen mutane biyu domin amincewa da su a matsayin kwamishinonin hukumar ayyuka ta tarayya (FSC).

Kara karanta wannan

Rigimar 'yan adawa ta kori Sanata, ya sanar da komawa APC a Majalisar Dattawa

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an mika wannan bukata ga kwamitin kafa ayyukan gwamnati, tare da wa’adin mako guda na kawo rahoto.

4. Nadin shugaban hukumar kidayar jama’a

Majalisar dattawan ta kuma karanta wasikar da Tinubu ya aika mata, inda ya ke son a tantance tare da amince da nadin Dr. Aminu Yusuf a matsayin shugaban hukumar NPC.

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya mika wannan batun zuwa ga kwamitin shaidar kasa da kidayar jama’a don ba da rahoto nan da mako guda.

5. Nade-nade a hukumar NDIC

Haka kuma, shugaban kasa ya turo sunan mutum daya da yake so a nada shi darakta a hukumar NDIC, kuma an tura bukatar ga kwamitin bankuna da inshora, don ba da rahoto cikin mako guda.

Shugaba Bola Tinubu ya nemi majalisa ta amince da nadin shugabannin hukumar PSC
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi a majalisar hadin gwiwa ta tarayya, Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Sauyin jam’iyya a majalisar dattawa

A wani muhimmin mataki na siyasa, Sanata Kelvin Chukwu, mai wakiltar Enugu ta Gabas, ya sanar da ficewa daga jam’iyyar LP zuwa APC.

Shugaban majalisa ya bayyana cewa ficewar ta kasance bisa yarjejeniya da kiyaye doka, tare da tabbatar da sabuwar mu’amala ta siyasa da jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta rantsar da sababbin sanatoci daga jihohi 2, an jero sunayensu

A ƙarshe, majalisar ta janye sauran batutuwan ranar, domin ta bai wa ‘yan majalisa damar tarbar baki daga Ghana da suka kai ziyara ga majalisar dattawan kasar.

Tinubu ya aika sako ga majalisar wakilai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya roƙi majalisar wakilai ta amince ya karbo sabon rancen $2.84bn, wanda ya kai Naira tiriliyan 4.26.

Shugaban kasar ya ce kuɗin da yake son karbowa zai taimaka wajen rufe gibin kasafin kuɗi da kuma sake biyan tsohon bashi na Eurobond da ya kai dala biliyan 1.118.

Masana tattali sun nuna damuwa, inda suka ce bashin da Gwamnatin Bola Tinubu ke karbowa ya yi yawa, alhalin tattalin arziki bai murmure ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com