Obasanjo, Shettima, Sarkin Musulmi, Zulum Sun Hadu a Taron Tattalin Arziki a Bauchi
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce yanzu ne lokaci mafi dacewa da zuba jari bayan farfadowar tattalin arziki
- Taron zuba jari na jihar Bauchi ya samu halartar tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, Babagana Zulum da Sarkin Musulmi
- Bala Mohammed ya kaddamar da cibiyar taron Sir Ahmadu Bello ta kasa da kasa wacce ya ce za ta zama hanyar bunkasa jihar
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi — Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta mayar da hankali wajen gyara tsarin tattalin arzikin ƙasa.
Sanata Kashim Shettima ya ce yanzu ne lokacin da ya dace da masu saka jari su zabi Najeriya a matsayin wajen hada hada.

Source: Facebook
Shettima ya bayyana haka ne yayin bude taron zuba jari na Bauchi na shekarar 2025, kamar yadda ya wallafa a X.
Taron ya samu halartar tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, Sarkin Musulmi da sauran manyan baki.
Bayanin Kashim Shettima a taron zuba jari
A jawabinsa, Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ta karɓi mulki a shekarar 2023 lokacin da tattalin arzikin ƙasa ke dab da durƙushewa.
Ya ce a lokacin, biyan bashin da gwamnatin tarayya ke yi na lakume kusan kashi 100 na kudin shigar kasar.
Sai dai, a cewar sa, yanzu an rage wannan matsalar zuwa ƙasa da kashi 50, yayin da ci gaban tattalin arziki ya karu da kashi 4.23 a watan da ya gabata.
Ya ce wannan nasara ta tabbata ne sakamakon kawar da kalubalen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta yi domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Bayanin gwamnan jihar Bauchi a taron
Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana jin daɗinsa da zuwan manyan baki ciki har da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.
A sakon da ya wallafa a Facebook, gwamnan ya yaba wa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima kan halartar kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello a Bauchi.

Source: Facebook
Gwamnan ya bayyana cewa cibiyar za ta zama ginshiƙin cigaban Bauchi da ba jiha damar karɓar manyan taruka na ƙasa da ƙetare, tare da haɓaka zuba jari da bunƙasa tattalin arzikin yankin.
Obasanjo, Sarkin Musulmi sun halarta
Yayin kaddamar da cibiyar, tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana aikin a matsayin abin yabawa da aka yi da hangen nesa.
Obasanjo ya yi magana yana mai cewa cibiyar za ta ƙara ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma samar da daman bunkasa kasuwanci da tattalin arziki.
Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da gwamnan Borno, Babagana Zulum, sun yabawa gwamnatin Bauchi bisa shirya taron.
Taron, wanda zai gudana na tsawon kwana biyu, ya tattaro masana tattalin arziki, ‘yan kasuwa, da jami’an gwamnati domin tattauna hanyoyin jawo zuba jari da bunƙasa tattalin arzikin Bauchi.
An yi taron tattalin arziki a Taraba
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar taraba ta shirya taron tattalin arziki domin jawo hankalin masu zuba jari.
Gwamnatin jihar Taraba ta bayyana cewa a shirye ta ke da ta karbi masu zuba jari daga ko ina a fadin duniya.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Atiku Abubakar, Aliko Dangote Mai Alfarma Sarkin Musulmi sun halarci taron.
Asali: Legit.ng


