Ana Bankwana da Damina: Za a Sheka Ruwan Sama a Taraba, Kogi da Jihohin Arewa 9

Ana Bankwana da Damina: Za a Sheka Ruwan Sama a Taraba, Kogi da Jihohin Arewa 9

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama a Taraba Kaduna, Kebbi da wasu jihohin Arewa a ranar Alhamis
  • A cewar sanarwar da ta fitar a daren ranar Laraba, ruwan sama na iya zuwa hade da iska mai karfi, wasu lokutan har da tsawa
  • An shawarci direbobi su yi tuki cikin nutsuwa domin ruwan sama zai iya rage ganinsu, kuma santsin hanya na iya jawo hadurra

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A yayin da ake bankwana da daminar bana, hukumar NiMet ta yi hasashen cewa ruwan sama zai sauka a jihohin Arewa 11 a yau Alhamis.

Tun a Janairun wannan shekarar ne aka fara samun ruwan sama a wasu jihohin Najeriya, har zuwa yanzu da daminar ke shirin karewa.

Hukumar NiMet ta ce za a samu ruwan sama mai karfi hade da tsawa da zai jawo ambaliya
Masu ababen hawa na tafiya a kan babban titi yayin da ake sheka ruwan sama. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Hasashen ruwan sama a jihohin Arewa

Kara karanta wannan

Za a sheka ruwan sama na kwana 3, Kano, Filato da jihohi 4 za su fuskanci ambaliya

A sanarwar hasashen yanayin na ranar Alhamis da NiMet ta fitar a shafinta na X, hukumar ta ce za a samu ruwan sama a jihohin Arewa da kewaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A safiyar Alhamis, NiMet ta ce za a samu hadari ne kawai a mafi yawan jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, sai kuma yayyafi a wasu sassan Taraba.

NiMet ta ce saboda hadarin ba zai yi wani yawa ba, ana sa ran za a samu bullowar rana da wuri, musamman a Arewa ta Tsakiya.

Ruwan sama a yammacin ranar Alhamis

Idan yammaci ta yi kuwa, hukumar NiMet ta ce hadari zai hadu sosai, kuma za a samu ruwan sama marar karfi a wasu sassan Kaduna, Bauchi, Gombe, Kebbi, Adamawa, da Taraba.

Ko a shiyyar Arewa ta Tsakiya, za a samu ruwan sama mai matsakaicin karfi a Abuja da sassan jihohin Plateau, Niger, Benue, Kogi, da Nasarawa.

Hasashen ruwan sama a yankin Kudu

Hukumar NiMet ta ce hadari zai fara taruwa a safiyar Alhamis a yankin Kudancin Najeriya, sannan sai ruwan sama ya biyo baya.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke a Majalisar Wakilai a yunƙurin tsige shugaban marasa rinjaye

Jihohin Kudu da za su samu ruwan sama a safiyar Alhamis sun hada da Imo, Abia, Ebonyi, Enugu, Edo, Cross River, Akwa Ibom, Rivers da Bayelsa.

Hakazalika, a yammacin Alhamis din, za a ci gaba da samun ruwan sama a wasu yankuna na jihohin Ondo, Ekiti, Ebonyi, Enugu, Anambra, Imo, Abia, Delta, Edo, Cross River, Akwa Ibom, Rivers, da Bayelsa.

Hukumar NiMet ta ce akwai yiwuwar a sheka ruwan sama a ranar Alhamis a wasu jihohi
Mutane na kokarin tsallaka titin da ambaliya ta shafe bayan saukar ruwan sama a Legas. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Shawarwari da gargadi daga NiMet

Hukumar NiMet ta fara yin gargadi da cewa ruwan sama na iya zuwa hade da iska mai karfi, wasu lokutan har da tsawa, wanda zai kawo tsaiko ga al'amuran yau da kullum.

An shawarci masu ababen hawa da su yi tuki cikin nutsuwa yayin da ake ruwan sama, domin ganinsu zai ragu, kuma santsin hanya na iya jawo hadurra.

NiMet ta shawarci mutanen da ke zaune a garuruwan da suka saba fuskantar ambaliyar ruwa da su zauna a cikin shiri, su kuma dauki matakan kare rayuka da dukiyoyinsu.

Gidaje, gonaki sun nutse a ambaliya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ambaliyar ruwa ta mamaye gidaje, tituna, gonaki da shaguna a wasu kananan hukumomin jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama matashin da ake zargi da sace basarake a Kano, ya fara kiran sunaye

Mazauna yankunan da ambaliyar ta shafa, sun gaggauta tattara ya-nasu ya-nasu sun fice daga gidajensu don tsira da rayukansu.

Kwamishinan muhalli na jihar, Felix Odimegwu ya bayyana irin matakan da gwamnatin Anambra ta dauka kan ambaliyar da ta afku bayan saukar mamakon ruwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com