Farfesa Mahmoud: Daga Ajiye Aiki, Kotu Ta Bada Umarni a Kamo Tsohon Shugaban INEC

Farfesa Mahmoud: Daga Ajiye Aiki, Kotu Ta Bada Umarni a Kamo Tsohon Shugaban INEC

  • Kotu ta bayar da umarnin a kama tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu
  • Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Ogun ce ta bayar da umarnin, inda ya zargi tsohon Shugaban INEC da kin cika umarnin da ta ba shi
  • Kotu ta ba da wa’adin kwanaki bakwai ga Sufeton ‘Yan sanda na ƙasa da ya kama Farfesa Mahoud Yakubu tare da kai shi gabanta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ogun – Wata babbar kotun tarayya da ke Osogbo, jihar Osun, ta bayar da umarnin a kama tsohon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.

Kotun ta zargi tsohon Shugaban da raina ta, saboda haka tana son Sufeton 'yan sanda na kasa, Kayode Egbetokun ya kamo Farfesa Mahmood a cikin kwanaki bakwai.

Kara karanta wannan

Kano ta dauki sabon kambu, ta zama ta 2 a tara kudin shiga a jihohin Najeriya

Kotu ta zargi Farfesa Mahmoud da raina ta
Tsohon Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu Hoto: INEC
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Mai shari’a Adefunmilola Demi-Ajayi ce ta bayar da wannan umarni a ranar Litinin, 29 ga Satumba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai Shari'ar ta bayar da umarnin ne kafin Farfesa Mahmoud Yakubu ya sauka daga mukaminsa na shugaban INEC bayan kammala wa’adinsa.

Dalilin kotu na neman tsohon Shugaban INEC

Daily Post ta wallafa cewa kotun ta bayyana cewa Farfesa Mahmoud Yakubu da hukumar INEC sun gaza aiwatar da umarnin kotu da ta bayar tun a watan Fabrairu.

A wancan lokaci, kotu ta bayar da umarni a mayar da sunayen shugabannin jam’iyyar AA ƙarƙashin Hon. Adekunle Rufai Omoaje a shafin yanar gizon hukumar.

Kotu ta nemi a a kamo Farfesa Mahmoud
Hoton Farfesa Mahmoud Yakubu Yakubu Hoto: INEC
Source: Twitter

Jam’iyyar AA ce ta shigar da ƙarar mai lamba FHC/OS/194/2024, tana neman kotu ta tilasta INEC da Farfesa Yakubu su maido da sunayen shugabanninta na ƙasa.

Ta yi zargin cewa tun da farko, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta cire sunayenta jagororinta ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Amupitan: Farfesa daga jami'ar Jos na dab da zama sabon shugaban hukumar INEC

INEC: Umarnin kotu ga Sufeton 'yan sanda

Kotu ta kuma umarci Sufeton ‘Yan sanda na ƙasa da ya tabbatar da kama waɗanda ake tuhuma a cikin kwanaki 7 don su fuskanci shari’a a kan zargin raina kotu.

A hukuncin kotu da ta yanke a watan Fabarairu, ta lafta wa INEC da Farfesa Yakubu tara ta N100,000 domin biyan diyyar kuɗi ga waɗanda suka shigar da ƙara.

Ƙarar ta ƙunshi jam’iyyar AA, Farfesa Julius Adebowale, Injiniya Olowookere Alabi, Barista Chinwuba Zulyke, Oladele Sunday, Simon Itokwe da Araoye Oyewole.

INEC da Farfesa Yakubu kuwa an ambace su a matsayinwadanda ake ƙara na farko da na biyu a shari'ar da AA ke ganin an tauye mata hakki.

Farfesa Mahmoud Yakubu ya bar shugabancin INEC

A baya, mun wallafa cewa Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC), ya ajiye aiki bayan ya shafe kusan wa'adi na farko da na biyu a mukamin.

Farfesa Mahmoud Yakubu ya mika ragamar shugabanci ga May Agbamuche, wacce za ta riƙe kujerar a matsayin mukaddashiyar shugabar hukumar har sai an nada sabon shugaban.

Kara karanta wannan

Mai Wushirya: Bayan tsawon lokaci yana bidiyon fitsara da wadarsa, kotu ta dauki mataki

A lokacin ganawar sa da kwamishinonin zabe na jihohi a hedikwatar INEC da ke Abuja, Yakubu ya bukaci ma'aikatan hukumar su ba Agbamuche cikakken goyon baya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng