'Yan Bindiga Sun Farmaki Makiyaya a Plateau, an Tafka Barna Mai Girma

'Yan Bindiga Sun Farmaki Makiyaya a Plateau, an Tafka Barna Mai Girma

  • 'Yan bindiga sun yi ta'asa yayin da suka afkawa makiyaya a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Miyagun sun yi kisa tare da yin awon gaba da shanu masu yawa na makiyayan wadanda ke dawowa daga wurin kiwo
  • Shugabannin kungiyar MACBAN a Plateau sun yi zargin cewa 'yan bindigan sun fito ne daga cikin mutanen wata kabila

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - 'Yan bindiga sun kashe wani makiyayi ɗan shekara 13 mai suna Abubakar Wada da shanu 36 a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun yi ta'asar ne lokacin da suke bude wuta kan shanun da ke kiwo a kusa da Inzon, wani kauye da ke gundumar Fan, a karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang. Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kungiyar MACBAN reshen jihar Plateau, Ibrahim Yusuf Babayo, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane yayin da 'yan sanda suka kashe miyagu a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kashe makiyaya da shanu a Plateau

Ibrahim Yusuf Babayo ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da yammacin ranar Talata, lokacin da wasu makiyaya uku ke dawowa daga kiwo.

A cewarsa, ‘yan bindiga sun rika harbin shanun, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar wani makiyayi ɗaya, yayin da sauran mutum biyun suka tsere.

"Lamarin ya faru da yamma. Zuwa yanzu mun kididdige asarar shanu fiye da 80, saboda an kashe 36, sannan kuma ba a san inda guda 49 suke ba. Mutanen kabilar Berom ne daga Fan suka kai harin."
"Wannan abu ne mai ban takaici. Makiyayan da shanunsu suna ne tafiya cikin lumana ba tare da wani rikici ba. Muna kira ga dukkan makiyaya a jihar da su zauna lafiya, su bar jami’an tsaro su gudanar da bincike, kada kowa ya ɗauki doka a hannunsa."

- Ibrahim Yusuf Babayo

An nuna yatsa kan 'yan kabilar Berom

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake ta'addanci a Kwara, an sace basarake da kashe mutane

Sakataren kungiyar MACBAN a Barkin Ladi, ya bayyana cewa ya sanar da dukkan hukumomin tsaro game da lamarin, kuma sun ziyarci wurin da harin ya auku.

Sai dai sakataren ya zargi wasu daga cikin mutanen kabilar Berom da kai harin, yana mai cewa a ranar Lahadi ma, an kashe shanu biyar a yankin.

'Yan bindiga sun farmaki makiyaya a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Mutanen kabilar Berom sun musanta zargin

Sai dai, shugaban kungiyar Berom Youths Moulders Association (BYM), Barrister Solomon Dalyop, ya karyata zargin, yana mai cewa mutanensu mutane ne masu zaman lafiya.

“A matsayina na shugaba, zargin da ake yi kan mutanenmu na Nding da dukkan yankin Fan, wata dabara ce kawai don nemo hujjar kai hari a kan mutanenmu. Mu mutane ne masu son zaman lafiya."

- Barrister Solomon Dalyop

'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci kan bayin Allah a jihar Zamfara.

'Yan bindigan sun kai harin ne a karamar hukumar Bukkuyum inda suka yi awon gaba da mutane 30, wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe shugaban jami'an tsaro da sace mutane a Neja

Jami'an tsaro sun bazama domin ceto mutanen da 'yan bindigan suka tafi da su zuwa cikin daji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng