Tinubu Zai Kinkimo Sabon Bashin Naira Tiriliyan 4.2, Ya Aika Wasiku 2 ga Majalisa
- Shugaba Bola Tinubu ya roƙi majalisar wakilai ta amince ya karbo sabon rancen $2.84bn, wanda ya kai Naira tiriliyan 4.26
- Masana tattali sun nuna damuwa, inda suka ce bashin da ƙasar ke karbowa ya yi yawa, alhalin tattalin arziki bai murmure ba
- An gargadi gwamnatin Bola Tinubu da ta rage cin bashi, kuma a yi amfani da kudin kawai ga walwala da ci gaban 'yan kasa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya aike da buƙatar neman amincewar majalisar wakilai domin karbo bashin $2.347bn daga kasuwannin kuɗi na ƙasashen waje.
A wata wasiku daban daban da ya aika wa kakakin majalisar, Abbas Tajudeen, Shugaba Tinubu ya kuma roƙi izinin fitar da lamunin sukuk na farko har $500m.

Source: Twitter
Bola Tinubu zai karbo bashin $2.84bn
Jimillar lamunin da ake nema ya kai $2.84bn (4.26trn), wanda ya haɗa da bashin waje na $2.347bn da kuma sukuk ɗin $500m, cewar rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar wasikar, wannan lamuni zai zo ne ta hanyar fitar da Eurobond, lamunin 'yan kasuwa ko kai tsaye daga cibiyoyin lamuni na ƙasa da ƙasa.
Ana sa ran kuɗin zai taimaka wajen rufe gibin kasafin kuɗi da kuma sake biyan tsohon bashi na Eurobond da ya kai dala biliyan 1.118.
An fara gargadin Tinubu kan ciwo bashi
Buƙatar sabon lamuni daga shugaban ƙasa ta janyo cece-kuce daga masana tattalin arziki da wasu ‘yan majalisa.
Rahoton Hukumar Lamuni ya nuna cewa, zuwa Maris din 2025, bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39, wanda ya haɗa da Naira tiriliyan 70.63 na waje da kuma Naira tiriliyan 78.76 na cikin gida.
Masu lura da al’amura sun ce, yayin da gwamnati ke neman ƙarin lamuni, ya kamata a kula da yadda bashi ke ƙaruwa fiye da ikon ƙasar wajen biya.

Source: Twitter
Masana sun hango illar ciyo bashin Tinubu
Shugaban cibiyar CPPE, Dr. Muda Yusuf, ya ce dole ne a tantance wannan bukatar cikin tsare-tsaren kashe kuɗi na dogon lokaci da majalisa ta amince da shi.
Jaridar Leadership ta rahoto wani masanin tattalin arziki, Dr. Paul Alaje, ya yi kira ga gwamnati ta rage neman bashi, yana cewa:
“Idan gwamnati ta riga ta cika burin samun kuɗaɗen shiga, bai dace ta ƙara ciwo bashi ba. Idan ya zama dole, to a karbo kuɗin aka san zai shafi rayuwar talakawa ta fuskar wutar lantarki, ilimi, lafiya, hanya da jirgin ƙasa.”
Masana sun kuma gargadi gwamnati da ta kula da daidaiton lamuni da ƙarfin tattalin arziki, domin kada bashin ya hana cigaba ko cin gajiyar kasafin kuɗi a nan gaba.
Tinubu zai karbi rancen $500m daga AfDB
A wani labarin, mun ruwaito cewa, bankin AfDB ya sanar da shirinsa na sake ba Najeriya rancen dala miliyan 500 kafin ƙarshen 2025.
Wannan na cikin rancen tallafin kasafin kuɗi na dala biliyan 1 domin rage tasirin sauye-sauyen tattalin arziki a Najeriya.
Ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Wale Edun, ya bayyana cewa za a yi amfani da kudin a manyan bangarori uku da suka hada da noma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

