Gwamna Zulum Ya Gwangwaje 'Yar Kabilar Igbo da Kyautar Ban Mamaki a Borno

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje 'Yar Kabilar Igbo da Kyautar Ban Mamaki a Borno

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya faranta ran wata ma'aikaciyar lafiya 'yar asalin Anambra
  • Mai girma Zulum ya ba matar gida a jihar Borno tare da ba danta wurin da zai rika aiki ba tare da bata lokaci ba
  • Matar 'yar kabilar Igbo ta yi godiya ga gwamnan inda ta nuna cewa ya saba yi mata abubuwa na alheri

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ba wata ma’aikaciyar lafiya, Mrs. Marbel Ijeoma Duaka, ‘yar asalin jihar Anambra, kyautar gida.

Gwamna Zulum ya ba ta kyuatar gidan ne mai dakuna biyu wanda aka sanyawa kayan daki.

Gwamna Zulum ya bada kyautar gida ga 'yar kabilar Igbo
Gwamna Babagaba Umara Zulum tare da Marbel Ijeoma Duaka. Hoto: Dauda Iliya
Source: Facebook

Gwamna Zulum ya ba Ibo kyautar gida

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakin gwamnan, Dauda Iliya, ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Digirin bogi: An nemi Ministan Tinubu ya yi murabus, ya mika kansa ga hukuma

A cewar sanarwar, Gwamna Zulum ya mika mata makullin gidan ne a ranar Talata, 7 ga watan Oktoban 2025.

Haka kuma, ɗanta Anthony, wanda ya kammala karatu a fannin banki da harkokin kudi, ya samu aiki a jami’ar jihar Borno mai suna Kashim Ibrahim da ke Maiduguri.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa Marbel Ijeoma Duaka ta yi aiki a asibitin ta Mafa fiye da shekaru 20 ba tare da ta taɓa barin garin ba, ko a lokacin da ake tsananin rikicin Boko Haram.

"Ta yi aiki a nan sama da shekaru 24, ba ta bar Mafa ko da na wata guda ba. A lokacin rikicin Boko Haram, mutane da dama sun gudu daga garin, amma ita ta zauna, duk da cewa ba ‘yar asalin jihar bace.”
"Ta taɓa kula da yawancin ‘yan uwana, har ma da mahaifiyata."
"Za a sanya sunanki a jikin takardar mallakar gidan. Kada ki bar Mafa, har bayan kin yi ritaya.”

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya aika da muhimmin sako ga mutanen Borno kan Boko Haram

"Za a ba danki, Anthony, aiki a jami'ar Kashim Ibrahim da ke Maiduguri. Aikinsa zai fara ne nan take."

- Gwamna Babagana Umara Zulum

Marbel Ijeoma Duaka na daga cikin malamai da ma’aikatan lafiya 72 da suka karɓi sababbin gidaje a bikin da aka gudanar a karamar hukumar Mafa a ranar Talata.

Zulum ya bada kyautar gida a Borno
Hoton gidan da Gwamna Zulum ya yi kyautarsa a Borno. Hoto: Dauda Iliya
Source: Facebook

'Yar kabilar Ibon ta yi godiya

Da take mayar da martani, Marbel Ijeoma Duaka ta bayyana cewa wannan rana ita ce mafi farin ciki a rayuwarta.

"Yau rana ce ta farin ciki a gare ni, saboda Mai girma Gwamna ya girmama ni kuma ya yaba da aikina a Mafa. Ya kasance mai kirki a gareni.”
"Ya ba ni gurbin yin karatun digiri na farko, yanzu kuma ya ba ɗana aiki, sannan ya ba ni gida. Ina matukar godiya."

- Marbel Ijeoma Duaka

Gwamnatin Zulum ta raba tallafi a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba tallafin kayan abinci kyauta ga jama'a.

Gwamna Zulum ya bada tallafin ne ga mutum 18,000 a garin Dikwa da ke yankin tsakiyar jihar Borno.

Kara karanta wannan

An taso gwamna a Arewa a gaba ya koma APC, Tinubu zai iya karasa aikin da Buhari ya watsar

Zulum ya ce matakin raba kayan tallafin ya zama dole domin guje wa kalubalen yunwa da wadanda suka rasa amfanin gona ka iya shiga nan gaba a yankin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng