Sanusi II Ya Yabi CBN da Tinubu, Ya Kawo Hujjojin Fitowa daga Kangin Tattalin Arziki
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya yaba da matakan da gwamnatin Bola Tinubu ke ɗauka don farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa
- Khalifa Sanusi II, wanda tsohon Gwamnan CBN ne ya ce cire tallafin mai da daidaita farashin Dala da Naira sun taimaka wa Najeriya
- Mai Martaban ya bayyana cewa tattalin arziki na nuna alamun farfaɗowa, duk da buƙatar ƙarin gyare-gyare da ba za a rasa ba a yanzu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sarkin Kano, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, ya jinjinawa matakan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke ɗauka wajen farfaɗo da tattalin arziki.
Mai martaba ya bayyana cewa matakai kamar cire tallafin man fetur da daidaita farashin Dala da Naira sun ceci Najeriya daga durkushewar tattalin arziki da aka fuskanta a baya.

Kara karanta wannan
"Tinubu ya yi abin da muke ta kira," Sarki Sanusi II ya hango goben tattalin arziki

Source: Twitter
Khalifa Muhammadu Sanusi II ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da News Central a ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025.
Sarki Sanusi II ya yaba wa Tinubu da CBN
A bidiyon da Masarautar Kano ta wallafa a shafinta na X, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa da kansa ya bayar da shawarwari a kan cire tallafin man fetur.
Ya bayyana cewa:
“A kan manufofin tattalin arziki, ba abin da zan ce sai yabo ga Babban Bankin Ƙasa (CBN). Mun baro yanayi mai haɗari na durkushewar tattalin arziki yayin da kuɗin ƙasar nan ke zurarewa.”
“Duk da har yanzu kuɗin ruwa ya yi yawa, amma ya sauko idan aka kwatanta da yadda yake a baya. Yanzu an daidaita canjin kuɗin ƙasashen waje, mun samu farfaɗowa daga rugujewar tattalin arziki baki ɗaya.”
“Hauhawar farashi yana sauka – 20% ake da shi na hauhawar farashi. Duk da cewa hakan yana da yawa, amma sauƙi ne idan aka kwatanta da yadda lamarin yake a ‘yan shekarun baya.”
'Tattalin arziki na habaka' Inji Sanusi II
Mai martaba Sarkin Kano ya bayyana cewa alamu sun tabbata, Najeriya ta fara barin wuri mafi hadari saboda ci gaban tattalin arziki da aka samu a jere.

Source: Facebook
A kalamansa:
“Mun samu ƙaruwa a kuɗin asusun ajiya na ƙasar da kusan $40bn. Tattalin arziki ya habaka a rubu’in farko na shekara da sama da 3%, a na biyu kuma da sama da 4%. Wannan shi ne karon farko da tattalin arzikin ƙasa ya fi yawan mutanen ƙasar habaka a cikin shekaru masu yawa.”
“A shekarun baya, karuwar mutanen ƙasar ta fi karfin habakar tattalin arziki gudu.”
Ya ce duk da akwai gyare-gyare da ake da buƙatar gwamnati ta yi, amma a halin yanzu tana kokari matuƙa wajen dawo da tattalin arziki kan turba.
Sarki Sanusi II ya kare Dangote
A baya, mun wallafa cewa Sarkin Kano Sanusi II da wasu fitattun ‘yan Najeriya sun fito fili don nuna goyon bayansu ga matatar Dangote a rikicinta da PENGASSAN, DAPPMAN da NUPENG.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II da wasu fitattun 'yan Najeriya sun shiga rikicin Dangote da PENGASSAN
A wata sanarwa ta haɗin gwiwa da aka fitar a ranar Talata, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, Rabaran Mathew Kukah da wasu mutum 11 sun soki kungiyoyin kwadago.
Sun ce yajin aiki ko amfani da barazana wajen hana isar da kayayyaki ga matatar ba hanya ce mai kyau ba — duk wata matsala da ake da ita, zai fi kyau a zauna domin kawo karshenta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
