"Tinubu Ya Yi Abin da Muke Ta Kira," Sarki Sanusi II Ya Hango Goben Tattalin Arziki

"Tinubu Ya Yi Abin da Muke Ta Kira," Sarki Sanusi II Ya Hango Goben Tattalin Arziki

  • Muhammadu Sanusi II ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara daukar matakan da ya jima yana kiran a dauka a Najeriya
  • Mai Martaba Sarkin Kano ya ce tsare-tsaren gyara tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun fara haifar da sakamako mai kyau
  • Tsohon gwamnan bankin CBN ya ce duk da akwai sauran aiki a gaba, amma dai Najeriya ta fara dawowa kan turba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa Gwamnatin Najeriya ta kama hanyar gyara tattalin arzikin kasa.

Sarkin, wanda tsohon gwamnan babban banki, CBN ne ya ce cire tallafin fetur da sauran matakan da gwamnati mai ci ta dauka shi ne daidai, kuma da ma ya jima yana kira kan haka.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya yabi CBN da Tinubu, ya kawo hujjojin fitowa daga kangin tattalin arzik

Muhammadu Sanusi II.
Hoton Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II. Hoto: Masarautar Kano
Source: Twitter

Muhammadu Sanusi II ya fadi haka ne a wata hira da tashar News Central ta yi da shi, wadda masarautar Kano ta wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnatin tarayya ta dauki matakan da ya jima yana kira da a dauka domin saita tattalin arzikin kasar nan.

Sanusi II ya ce Tinubu ya dauko hanya

Sanusi II ya tuna wasu daga cikin abubuwan da ya nemi Najeriya ta yi shekaru sama da 10 da suka wuce, ciki har da sake fasalin tsarin canjin kudi, daidaita hauhawar farashin kaya da sauransu.

"Sun yi mafi yawan abubuwan da tun shekaru 10 da suka wuce muke ta kiran a yi, mu samar da daidaito a tsarin canjin kudi, mu shawo kan hauhawar farashi, mu gina tubalin da zai jawo zuba jari.
"Ba ina nufin mun kai wurin da ya kamata ba ne, akwai sauran aiki, akwai sauran abubuwan da ba a yi ba har yanzu, akwai inda aka yi kura-kurai ko kuma mu ce ba a yi abin da ya dace ba.

Kara karanta wannan

Kano ta dauki sabon kambu, ta zama ta 2 a tara kudin shiga a jihohin Najeriya

"Amma dai game da manyan batutuwa, zan iya cewa an dauko hanyar gyara tattalin arziki, cire tallafin mai da daidaita farashin canji sun zo a lokacin da ya dace."

- Muhammadu Sanusi II.

"Tattalin arziki ya dawo kan hanya" - Sanusi II

Basaraken ya kara da cewa sakamakon matakan da aka dauka, babban bankin Najeriya (CBN) ya fara gano bakin zaren tare da dawo da tattalin raziki kan turba.

Sanusi II ya bayyana yadda tattalin arzikin Najeriya ya fara farfadowa daga kashin farko na shekaran nan, yana mai cewa wannan ne karon farko da ya shiga gaban karuwar jama'ar da ake samu a Najeriya.

Sarki Sanusi II da Shugaba Tinubu.
Hoton Mai Martaba Sarkin Kano a wurin taron tattalin arziki da na Mai Girma Shugaba Tinubu. Hoto: @masarautarkano, @OfficialABAT
Source: Twitter

Sanusi II ya kara da cewa:

"Alkaluma sun nuna, a kashin farko na 2025, idan ban manta ba tattalin arzikin mu ya bunkasa da kaso 3.13, a kashi na biyu ya tabo kaso 4.
"Kuma kamar yadda na fada, wannan ne karo na farko da muka samu bunkasar tattalin arziki fiye da karuwar jama'a a kasar nan. Hakan alama ce da ke nuna muna kan hanya."

Sanusi II ya gano hanyar bunkasa tattalin arziki

Kara karanta wannan

Mai Wushirya: Bayan tsawon lokaci yana bidiyon fitsara da wadarsa, kotu ta dauki mataki

A wani labarin, kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya bukaci a kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da bangaren masu zaman kansu.

Sanusi II ya bayyana cewa kakkarfar alaka tsakanin bangarorin biyu zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

Ya ce jarin masu zaman kansu shi ne ginshiƙin da zai iya buɗe damar tattalin arzikin Najeriya da kuma dorewar sauye-sauyen da ake aiwatarwa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262