Nnamdi Kanu: Ta Yi Tsami har Mamba Ya Yi Wa Shugaban Majalisa Rashin Kunya

Nnamdi Kanu: Ta Yi Tsami har Mamba Ya Yi Wa Shugaban Majalisa Rashin Kunya

  • Rikici ya barke a Majalisar Wakilai tsakanin Obinna Aguocha da Kakakin Majalisa, Rt. Hon. Abbas Tajudeen kan batun lafiyar Nnamdi Kanu
  • Aguocha ya ce ya rubuta wasika tun Agustan 2025 zuwa ga Bola Tinubu, Ministan Shari’a da Kakakin Majalisa domin neman a ba Kanu kulawar likita
  • Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu ya shiga tsakani ya ce za a ba batun lokaci a zauren majalisa domin a tattauna batun

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An samu hatsaniya a Majalisar Wakilai yayin da dan majalisa ya yi takaddama da Kakakin Majalisa kan lafiyar Nnamdi Kanu

An samu dan rigimar ne a Majalisar Wakilan Tarayya, yayin da dan majalisa Obinna Aguocha daga LP, ya samu saban fahimta da Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen.

An yi cacar baki tsakanin shugaban majalisa da mamba a Abuja
Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudden Abbas yayin zamansu a Abuja. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Rahoton Premium Times ya ce lamarin ya faru ne kan kokarinsa na jan hankalin majalisar game da rashin lafiyar shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Yadda shugaban majalisa ya ceto shugaban marasa rinjaye daga yunkurin tsige shi

Lamarin ya faru ne bayan sake komawar majalisar daga hutu, inda Aguocha ya gabatar da bukata ta gaggawa kan matsanancin halin da lafiyar Kanu ke ciki.

Korafin dan Majalisar kan lafiyar Nnamdi Kanu

Aguocha ya bayyana cewa tun ranar 26 ga Agusta, ya rubuta wasiku zuwa ga Shugaban kasa Bola Tinubu, Ministan Shari’a Lateef Fagbemi, da kuma Kakakin Majalisar, yana neman a ba Nnamdi Kanu kulawar gaggawa ta likita.

Ya ce:

“Har yau babu wani amsa da na samu. Rahoton likitocinsa da kuma na kungiyar likitoci ta kasa sun tabbatar da cewa gabobin jikinsa sun fara gajiya kuma yana da matsalar karancin sinadarin potassium a jiki, abin da ke barazanar mutuwa.”

Aguocha ya kuma tuna wa majalisar cewa kotun ta riga ta bayar da umarnin a duba lafiyar Kanu, inda rahotanni uku da aka samu suka tabbatar da cewa halin da yake ciki yana da tsanani.

“Wannan batu na kare hakkin dan adam ne. Kotu ta fada cewa mutum mai rai ne kawai zai iya gurfana a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Akpabio ya yi maganar farko bayan bude majalisa da dawowar Sanata Natasha

Ba a samu Nnamdi Kanu da wani laifi ba, don haka ya cancanci a bar shi ya samu magani kamar yadda aka taba bari wasu su je kasashen waje domin jinya.”

- Obinna Aguocha

An samu hatsaniya a majalisar wakilai a Abuja
Mambobin majalisa wakilai yayin zama a Abuja. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Martanin Kakakin Majalisa ga Obinna Aguocha

Sai dai Kakakin Majalisa, Abbas Tajudeen, ya ce babu hujjar da ke nuna cewa hakkin Aguocha ne ya kawo maganar majalisar don haka ba zai amince da bukatar ba, cewar rahoton TheCable.

Ya ce:

“Idan kana da wasika zuwa ofishina, kana iya zuwa kai tsaye, ko ka kira ni. Wannan ba irin batun da ake kawo nan ba ne.”

Sai dai Aguocha ya dage, yana mai cewa ya mika wasikar da kansa tun ranar 27 ga Agusta, kuma ofishin Kakakin ya karba.

Rigimar ta dauki zafi, inda Aguocha ke cewa wannan batun rayuwa da mutuwa ne, amma Kakakin ya ce “ka tsaya, ba irin batun da za a kawo a haka ba ne”, daga nan aka katse masa makirufo.

Mataimakin Kakakin Majalisa ya shawo kan lamarin

Bayan yanayin ya fara daukar zafi, Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, ya shiga tsakani yana neman kwantar da hankali.

Kara karanta wannan

Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa, ta zauna a kujerar da ta yi rigima da Akpabio

Ya ce:

“Na fahimci damuwar da dan majalisa ke ciki. Mu kawo batun daidai bisa ka’ida domin a ba shi cikakken lokaci a zauren nan.”

Kakakin Majalisar ya amince da hakan, yana cewa matsayinsa na farko bai shafi batun ba kai tsaye, illa tsarin da aka bi ne kawai bai dace ba.

Kakakin majalisa ya ceto shugaban marasa rinjaye

Mun ba ku labarin cewa an bayyana yadda shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya yi nasarar kawo tsaiko a shirin tsige Shugaban Marasa Rinjaye.

A wannan makon nan ne aka fara shirin tsige Kingsley Chinda daga kujerarsa saboda zargin mulkin kama karya da kuma kusanci da Nyesom Wike.

Shirin ya taba 'dan majalisar na Ribas, inda bai tsaya a ko ina ba sai a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja domin a taka wa takwarorinsa burki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.