PENGASSAN Ta Jawo Wa Kanta, Tinubu Ya Dauki Zafi kan Rigimarta da Matatar Dangote

PENGASSAN Ta Jawo Wa Kanta, Tinubu Ya Dauki Zafi kan Rigimarta da Matatar Dangote

  • Shugaba Tinubu ya ja kunnen kungiyar PENGASSAN kan takun sakar da ta yi da matatar Alhaji Aliko Dangote da ke jihar Legas
  • Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta sa kafar wando daya da duk wanda ya nemi gurgunta matatar wacce ta lakume Dala biliyan 20
  • Shugaban kasar ya ce bai kamata a jefa kasa gaba daya cikin mawuyacin hali kan abin da za a iya warwarewa a teburin sulhu ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna bacin ransa kan yajin aikin da kungiyar ma'aikatan fetur da gas (PENGASSAN) ta yi a baya-bayan nan.

PENGASSAN ta shiga yajin aiki tare da dakatar da duk wasu ayyukanta a rigimar da ta shiga tsakaninta da matatar Dangote, lamarin da ake ganin ya taba tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun bayyana matsayarsu kan zaben 2027, ta fadi kalan dan takararta

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana magana a wurin taro. Hoto: @SundayDare
Source: Twitter

Bola Tinubu ya soki kungiyar PENGASSAN

Shugaba Tinubu ya soki kungiyar tare da gargadinta da ta guji duk wani yajin aiki da zai kawo tangarda ga tattalin arzikin kasar nan, kamar yadda The Nation ta kawo.

“Ba zai yiwu mu jefa kasa gaba daya cikin matsala ba saboda wasu matsalolin da za mu iya warwarewa a teburin tattaunawa,” in ji Shugaba Tinubu.

Wannan shi ne martaninsa na farko kan matakin da kungiyar ta katse iskar gas da ke zuwa matatar Dangote tare da takaita tura danyen mai zuwa tashoshin fitar da shi zuwa kasashen waje.

Shugaban kasa ya yi wannan jawabi ne a taron kungiyar tattalin arzikin Najeriya (NESG) da aka gudanar a Abuja, inda Mataimakinsa, Kashim Shettima ya wakilce shi.

Matsalolin da yajin aikin PENGASSAN ya jawo

Ya bukaci shugabannin kungiyoyin kwadago da su kasance masu kishin kasa da taka-tsantsan, tare da yin la’akari da tsaron kasa yayin da suke fafutukar kare muradun ma’aikata.

Kara karanta wannan

Digirin bogi: An nemi Ministan Tinubu ya yi murabus, ya mika kansa ga hukuma

Shi ma babban shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya tuna babbar asarar da kasar ta yi a kwanakin da yajin aikin ya dauka.

A Legas, an sha fama da karancin iskar gas na girki a karshen mako, lamarin da ya jefa jama’a cikin mawuyacin hali kuma an danganta hakan yajin aikin PENGASSAN.

Shugaba Tinubu ya bayyana matatar mai ta Dangote mai darajar Dala biliyan 20 a matsayin babban kadarar kasa da dole a kare ta domin ci gaban Najeriya.

A wurin taron akwai Ministan Kasafin Kudi da Tsare-TsarenTattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, da sauran manyan jami’an gwamnati.

Gwamnatin Tinubu na tare da matatar Dangote

Tinubu ya ce duk wata barazana ga matatar Dangote da ke da karfin tace ganga 650,000 a rana, za a dauke shi a matsayin cin amanar kasa, in ji rahoton Punch.

Ya kara da cewa gwamnati za ta kare matatar, tare da gargadin cewa bai kamata a bari wani abu ya katse aikin wannan babban gini da ya lashe Dala biliyan 20 ba.

Shugaban Dangote Group, Aliko Dangote.
Hoton shugaban kamfanin Dangote Group, Aliko Dangote da wani bangaren matatarsa. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Shugaban kasar ya bayyana shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, a matsayin “wata muhimmiya cibiyar tattalin arziki.”

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi martani kan zargin Minista na amfani da takardun bogi

Ya bukaci kungiyoyin kwadago da su yi hakuri su kuma nemi hanyar tattaunawa cikin lumana wajen shawo kan matsalolin masana’antu da suka shafi matatar.

Jerin mutane da Dangote ya yiwa godiya

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote ya godewa Shugaba Tinubu bisa sasanta rigimarsa da PENGASSAN.

Dangote ya gode wa duka wadanda suka taimaka wajen kawo karshen wannan matsala a wata sanarwa da matatarsa ta fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce, daga cikin jami’an gwamnati da suka taka rawar gani wajen dakile yunkurin PENGASSAN akwai shugabannin tsaro na kasa da Ministoci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262