Sarki Sanusi II da Wasu Fitattun 'Yan Najeriya Sun Shiga Rikicin Dangote da PENGASSAN

Sarki Sanusi II da Wasu Fitattun 'Yan Najeriya Sun Shiga Rikicin Dangote da PENGASSAN

  • Wasu fitattun 'yan Najeriya sun nuna goyon bayansu 100% ga matatar Dangote a kan rikicinta da PENGASSAN da wasu kungiyoyin mai
  • Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, Rabaran Mathew Kukah da wasu 'yan kasar nan sun ce lamarin ya nuna matsalar zuba jari
  • Sun bayyana cewa matatar Dangote sauki ce ga Najeriya, saboda haka matakin yajin aiki da aka dauka a baya kuskure ne babba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Wasu fitattun ’yan Najeriya da suka hada da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, da Bishof na cocin Katolika a Sakkwato, Mathew Kukah, sun goyi bayan matatar Dangote.

Sun bayyana goyon baya ga matatar man Dangote, bayan sukar da wasu kungiyoyin kwadago da su ka hada da PENGASSAN, NUPENG da DAPPMAN ke yi mata.

Kara karanta wannan

PENGASSAN ta hukunta rassanta 2 kan rashin hana Dangote gas a yajin aiki

Sarki Sanusi da wasu 'yan Najeriya sun goyi bayan Dangote
Hoton Sarki Muhammadu Sanusi II da matatar mai Hoto: Hoto: @masarautarkano, Nurphoto
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, tawagar ta yi kira da a kwantar da hankali, tare da gargadin cewa irin wadannan hare-hare na iya hana masu zuba jari sha’awa a Najeriya.

Sarki Sanusi, Rabaran Kukah na bayan Dangote

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar a ranar Talata, Sarki Sanusi II, Rabaran Kukah da wasu mutum 11 sun ce lamarin PENGASSAN ya nuna tsoron da ake da shi a kan zuba jari a Najeriya.

Sun ce yajin aiki ko barazana da ke hana isar da kayayyaki ga matata bai kamata ba, kuma duk wata damuwa kan gasa ko danniya ya kamata a magance ta cikin lumana ba yajin aiki ba.

Sanarwar ta jaddada cewa matatar Dangote ta riga ta fara saukaka matsin lamba a kasuwa, inda ake sayar da fetur daga kimanin ₦1,500 zuwa ₦820 a wasu wurare.

A cewarsu, wannan sauyi na rage farashin sufuri da abinci, kuma yana nuna yadda masana’antu na cikin gida za su iya inganta rayuwar yau da kullum.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke a Majalisar Wakilai a yunƙurin tsige shugaban marasa rinjaye

Mutanen da su ka goyi bayan Dangote

Baya ga Sarkin Kano da Rabaran Mathew Kukah, sai kuma babban malami a jami'ar ABU kuma mai bincike, Abubakar Mohammed da Aisha Yesufu (mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam).

Sauran sun hada da Arunma Oteh (masani tattalin arziki), Atedo Peterside (Ma'aikacin bankin zuba jari) da Dr Salamatu Suleiman (Kwamishiniyar ECOWAS).

An yabi matatar Dangote a Najeriya
Hoton Alhaji Aliko Dangote, da gidan mai Hoto: Dangote Industries/NNPC Limited
Source: Facebook

Dudu Mamman Manuga (jagorar mata na LP), Ibrahim Waziri, Barbara Etim James, Opeyemi Adamolekun, Osita Chidoka da Sanata Sola Akinyede duk suna goyon baya ga Dangote.

Sun bayyana cewa, bayan shekaru da dama na gazawar matatun gwamnati da asarar tiriliyoyi a tallafi, da kuma dogaro da shigo da fetur daga waje, matatar Dangote ta zama abar koyi.

Dangote ya rage farashin fetur da gas

A baya, mun wallafa cewa matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin iskar gas din girki (LPG) daga ₦810 zuwa ₦760 a kowanne kilo a kasuwannnin kasar nan.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya kama kansa a kan zarginsa da takardun karatun bogi

Matatar ta bayyana cewa wannan mataki ya zo ne domin saukaka wa ‘yan Najeriya da rage wahalar da ake sha wajen samun isasshen gas a wasu yankunan kasar nan.

Rahotanni su na nuna cewa wasu kamfanoni masu zaman kansu kamar Matrix da Ardova suna sayar da gas a farashin ₦920, yayin da wasu kamfanoni kamar A.Y.M Shafa a kan ₦910.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng