Ma'aikatan Jami'o'i Sun Fusata da Tinubu, Za Su Rufe Titunan Najeriya a Ranar Alhamis

Ma'aikatan Jami'o'i Sun Fusata da Tinubu, Za Su Rufe Titunan Najeriya a Ranar Alhamis

  • Kungiyoyin ma'aikatan jami'o'i sun gaji da alkawuran gwamnati kan hakkokinsu da suke bi tun shekaru da suka wuce
  • 'Yan kungiyoyin SSANU da NASU sun shirya gudanar da zanga-zangar kwana ɗaya a Alhamis 9 ga watan Oktobar 2025
  • Hakan ya biyo bayan gwamnati ta kasa cika alkawurran da suka yi mata wanda ya jefa su a matsaloli marar misaltuwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’i, SSANU da NASU, sun yi barazana ga gwamnatin kan hakkokinsu.

Kungiyoyin sun sanar da gudanar da zanga-zangar kwana ɗaya a ranar Alhamis 9 ga watan Oktobar 2025.

Kungiyoyin SSANU, NASU za su gudanar da zanga-zanga
Daruruwan yan Najeriya yayin zanga-zanga a kasar. Hoto: Nigeria Labour Congress, NLC.
Source: Facebook

SSANU, SANU: Musabbabin shirin fara zanga-zanga

Rahoton Punch ya ce kungiyoyin sun yi niyyar hakan ne saboda gwamnatin tarayya ta gaza biya musu bukatunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar da suka fitar, sun umurci rassansu su yi taron gaggawa a ranar Laraba 8 ga watan Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Ecuador: Matasa kusan 500 sun rufe shugaban kasa da jifa da duwatsu

An tabbatar hakan ne don shirya mambobi shiga zanga-zangar da kiran manema labarai domin neman hakkinsu a wurin gwamnati.

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnati ta ki warware batutuwan da suka hada da rashin biyan albashi, karin 35%, da rashin biyan kudaden da ake bin su.

Shugaban SSANU, Kwamred Mohammed Ibrahim, ya gargadi gwamnati cewa idan ba ta biya bukatun ba, “za su dauki mataki mai tsanani fiye da yajin aiki.”

Ya koka da cewa ma’aikatan da ba malaman karatu ba sune “mabukata kuma mafi jin radadin tattalin arziki da walwala a jami’o’in kasar nan.”

SSANU da NASU na shirin gudanar da zanga-zanga a gobe Alhamis
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Matsalolin da ke tsakanin gwamnat da SSANU

Daga cikin batutuwan da ke janyo ce-ce-ku-ce akwai zargin rashin daidaito wajen rabon kudaden alawus-alawus na Naira biliyan 50.

Sai kuma jinkiri wajen sabunta yarjejeniyar 2009 tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin NASU/SSANU; rashin biyan albashin watanni biyu da suka rage.

Sannan akwai bashin karin albashi na kashi 25 da 35 cikin 100; da kuma kin tura wasu kudi a watan Mayu da Yuni 2022.

Kara karanta wannan

Shettima ya ba da mamaki da ya kira Sanusi II da Sarkin Kano a taro a Abuja

Yadda SSANU ta dagawa gwamnati kafa a baya

Kungiyar haɗin gwiwa ta JAC ta taɓa bai wa gwamnati wa’adin kwanaki bakwai a ranar 15 ga Satumba, amma daga baya ta ƙara kwanaki 14, wanda ya ƙare a ranar Litinin, 6 ga Oktobar 2025.

A cikin wata takarda da aka fitar a ranar 6 ga Oktoba mai taken “Fara Zanga-Zangar Lumana”, Babban Sakataren NASU, Prince Peters Adeyemi ya ce ƙungiyoyin sun umurci dukkan mambobinsu da su shiga zanga-zangar.

Gwamnati za ta biya hakkokin SSANU, NASU

A baya, kun ji cewa, Gwamnatin Tarayya ta ce akwai yiwuwar ta biya ma'aikatan ilimi na SSANU da NASU rabin albashisu da suke binta tun 2022

Ministan ilimi na lokacin, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana hakan, inda ya ce suna kokarin biyan ma'aikatan domin sama musu sauki.

Amma za a biya kudin ne idan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da bukatar da suka tura masa na biyan albashin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.