Kano Ta Dauki Sabon Kambu, Ta zama Ta 2 a Tara Kudin Shiga a Jihohin Najeriya

Kano Ta Dauki Sabon Kambu, Ta zama Ta 2 a Tara Kudin Shiga a Jihohin Najeriya

  • Gwamnatin Jihar Kano ta samu kara kai wa mataki na nasara a yayin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ke cewa yana aikin ci gaban al'umma
  • A wannan karon, gwamnatin jihar ta ninka kudin shiga da ta ke samu da 100% a shekarar 2024 saboda wasu sauye-sauye a hukumar haraji
  • Gwamnati ta ce ba ta ƙara wa talakawa haraji ba, amma ta toshe kafar da ake zubda kuɗin baitul mali don samar da kuɗin ayyukan jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A yayin da jihohi da dama ke fama wajen ƙara yawan kuɗin shiga, Kano ta yi abin a yaba domin ta ninka abin da ta ke samu da sama da 100%.

Wannan na cikin rahoton da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar tare da tabbatarwar Statista, babban cibiyar tattara bayanai a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ecuador: Matasa kusan 500 sun rufe shugaban kasa da jifa da duwatsu

Gwamnatin Kano ta yi zarra a tara kudin shiga
Hoton Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa an ga sakamakon karin kudin shiga ne saboda jajircewar gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Ibrahim Adam, mai bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf shawara kan harkokin yada labarai ya bayyana haka.

Yadda gwamnatin Kano ta tara kudin haraji

Jaridar Punch ta wallafa cewa Ibrahim Adam ya ce tun bayan rantsuwar kama aiki da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yu, ya fara daukar matakan gyara hukumar haraji.

Wannan sauyi, a cewarsa, ya kawo babban ci gaba da ya sanya Kano ta zama ta biyu a jerin jihohin da suka fi samun kuɗin shiga a 2024.

Rahoton NBS ya nuna cewa jihohin da suka fi samun karin kudin shiga sun hada da: Enugu ₦180.50bn, Kano ₦74.77bn da Cross River ₦47.02bn.

Gwamnatin Kano ta ce an toshe kafar zurarewar kudi
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A cewar kiddiddigar NBS ta nuna yadda sauran jihohin su ka tara kudin shiga, inda Anambra ta samu ₦42.69bn, sai Ekiti ₦35.21bn, Bauchi ₦32.43bn da Ebonyi da ta tatso ₦13.18bn.

Kara karanta wannan

Mai Wushirya: Bayan tsawon lokaci yana bidiyon fitsara da wadarsa, kotu ta dauki mataki

A shekarar 2023, Kano ta tara ₦37.38bn, wanda ke nuna cewa kuɗin shiga da jihar ta samu sun ninka da 100% a shekara ɗaya kacal.

Kano: An toshe hanyar asarar kudin shiga

Ibrahim Adam ya bayyana cewa gwamnatin Kano ba ta taɓa ƙara wa talakawa haraji ba, musamman masu Keke Napep, wadanda ake ce wa an danne su a mulkin baya.

Ya ce:

“Mutane da dama suna tambaya daga ina gwamnati ke samo kuɗin da ake gina manyan ayyukan ci gaba—ga amsar.”

Ya ƙara da cewa daga cikin dabarun da aka ɗauka akwai toshe hanyoyin zurarewar kuɗi da kuma inganta tsarin karɓar kudin.

A cewarsa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna godiyarsa ga al’ummar Kano bisa haɗin kan da suke bai wa gwamnati.

Gwamnan Kano: "Da Allah SWT na dogara"

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayyana cewa yana dogara ga Allah dangane da barazanar da ake yi masa game da zaben 2027 mai zuwa.

Wannan magana ta zo ne a lokacin da Gwamna Abba yake rabon tallafin ₦150,000 ga wasu marasa ƙarfi a jihar, inda ya yi kira ga al’umma su guji yada jita-jita marasa tushe.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Abba ta shirya kashe N1.6bn don auren gata a jihar Kano

Ya ƙara da cewa gwamnati ba za ta yi jinkiri wajen mayar da hankali kan inganta rayuwar talakawa ba, duk da yadda wasu ke ƙoƙarin bata masa suna ko tada zaune tsaye.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng