'Yan Bindiga Sun Tare Babbar Hanya a Zamfara, Sun Sace Shugaban Majalisar Malamai

'Yan Bindiga Sun Tare Babbar Hanya a Zamfara, Sun Sace Shugaban Majalisar Malamai

  • Yan bindiga na ci gaba da kai hare-haren a Arewacin Najeriya wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi duk da kokarin sojoji
  • Maharan sun tare babbar hanyar birnin Gusau zuwa Gummi a Zamfara da yammacin jiya Talata 7 ga watan Oktobar 2025
  • Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun dauki lokaci suna binciken motoci kafin su tafi da mutane zuwa dajin Gummi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Yankin Arewa maso Yamma na ci gaba da shan fama da hare-haren yan bindiga babu kakkautawa.

Da yammacin jiya Talata 7 ga watan Oktobar 2024, ‘yan bindiga suka tare hanyar Gusau–Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama.

Yan bindiga sun sace shugaban majalisar malamai a Zamfara
Karamin ministan tsaro, Bello Matawall da shugaban majalisar malamai a Gummi. Hoto: @Dankatsina50, Dr. Bello Matawalle.
Source: Twitter

Shafin Bakatsine da ke kawo ragotanni kan matsalolin tsaro a manhajar X ya ce miyagun sun dakatar da motoci sannan suka sace fasinjoji.

Kara karanta wannan

Labari ya fara sauyawa: Malami ya fadi shirin Ahlus Sunnah kan zaben 2027 a Kano

Wasu yankunan sun zauna da 'yan bindiga

Jihar Zamfara na daga cikin jihohi mafi shan fama da matsalolin hare-haren yan bindiga da ya fi shafar yankunan karkara.

Ba dare, ba rana kullum mahara kara kai hare-hare suke yi cikin sabon salo duk da kokarin da wasu garuruwa musamman a Katsina ke yi na tattaunawa da su.

A jihar Katsina mai makwbtaka da Zamfara, ƙananan hukumomi da dama sun zauna da maharan domin sulhu da kuma dakile yawan hare-hare a yankunansu.

Zamfara: Kalaman Gwamna kan matsalolin tsaro

A kwanakin baya, Gwamna Dauda Lawal na Zamfara ya yi wasu irin maganganu game da rashin tsaro wanda ya sanya shakku a yaki da ta'addanci.

Dauda Lawal ya ce a yanzu haka ya san mabuyar yan bindiga da abubuwa da dama game da ayyukansu amma bai isa ba sojoji da yan sanda umarni ba.

Maganganun sun jawo ce-ce-ku-ce da wasu ke tabbatar da cewa gwamnati ba ta shirya kawo karshen yan ta'adda ba musanman a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe shugaban jami'an tsaro da sace mutane a Neja

Yan bindiga sun kai hari inda suka sace malamin musulunci
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

'Yan bindiga sun dauke shugaban majalisar malamai

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kwashe lokaci suna binciken motoci kafin su tafi da mutane da suka kama.

Cikin wadanda aka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban malaman Musulunci a ƙaramar hukumar Gummi, abin da ya jawo fargaba a yankin.

Sanarwar ta ce:

"Da yammacin jiya Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau–Gummi a Jihar Zamfara.
"Maharan sun dakatar da motoci sannan suka sace fasinjoji da dama, ciki har da Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta karamar hukumar Gummi."

Yan bindiga sun cewa liman, kansiloli 2

A baya, mun kawo muku labarin cewa 'yan bindiga sun kai wani hari a Tsauni da ke birnin Gusau a jihar Zamfara inda suka sace kansiloli biyu yayin farmakin.

Lamarin ya faru ne da dare inda aka dauke kansilolin biyu daga karamar hukumar Maradun da wani liman bayan sallar Magriba.

Kara karanta wannan

'Ka ba mu dama': Mutanen Sokoto sun tura sako ga Tinubu kan harin ƴan bindiga

Shaidu sun ce maharan sun kwace wayoyin ’yan sanda a bakin ofishinsu ba tare da wata turjiya ba, sannan suka yi gaba da mutanen.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.