Abin da Tinubu Ya Fada da Shugaban INEC Ya Ajiye Aiki, Ya Ba Shi Kyautar Sallama

Abin da Tinubu Ya Fada da Shugaban INEC Ya Ajiye Aiki, Ya Ba Shi Kyautar Sallama

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi magana bayan shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ajiye aiki
  • Tinubu ya amince da barin Farfesa Yakubu mukamin shugaban INEC bayan karewar wa’adinsa na biyu tun da ya hau kujerar a 2015
  • Shugaban ya yaba da jajircewar Yakubu wajen gudanar da zabubbuka masu tsafta tare da ba shi lambar yabo ta CON saboda hidimarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya magantu bayan shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ya ajiye aiki a matsayin jagora a hukumar.

A yau Talata ne 7 ga watan Oktoban 2025, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi murabus daga shugabancin hukumar bayan shafe shekaru 10 a kan kujerar.

Tinubu ya amince da murabus din Mahmood Yakubu
Tsohon shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: INEC Nigeria, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ya wallafa a shafin X, ya ce Bola Tinubu ya amince da ajiye aiki da Farfesa Yakubu ya yi bayan karewar wa'adinsa.

Kara karanta wannan

Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga mukamin shugaban INEC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekarar da aka nada Farfesa Mahmood Yakubu

An nada Farfesa Yakubu a karo na farko a Nuwambar 2015 a farkon mulkin marigayi Muhammadu Buhari, ya rike mukamin na tsawon shekara biyar.

Har ila yau, marigayi Buhari ya sake sabunta wa’adin Mahmood Yakubu a 2020, wanda yanzu ya kare bayan cikar lokaci.

Farfesa Yakubu ya karbi ragamar shugabancin hukumar ne daga Farfesa Attahiru Jega wanda ya jagoranci zaben 2015 da ya ba Muhammadu Buhari nasara kan Goodluck Jonathan.

Tinubu ya yabawa kokatin Mahmood Yakubu bayan murabus dinsa
Shugaban kasa, Bola Tinubu yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Tinubu ya amince da tafiyar Farfesa Yakubu

Tinubu ya amince da ajiye aiki da Farfesa Yakubu ya yi a matsayin Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) bayan karewar wa’adinsa na biyu.

Shugaba Tinubu ya gode wa Farfesa Yakubu bisa irin gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da dimokuradiyya a Najeriya.

Tinubu ya yaba masa ne musamman ta hanyar shirya zabubbuka da ya kira masu tsafta da gaskiya a lokacin mulkinsa na shekaru 10.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya tabo batun tazarcen Tinubu, ya hango abin da mutanen Kano za su yi a 2027

Karramawar da Tinubu ya yi wa Yakubu

A matsayin girmamawa ga ayyukansa na kishin kasa, Shugaban kasa ya ba shi lambar yabo ta Commander of the Order of the Niger (CON).

Haka kuma ya umarci Farfesa Yakubu da ya mika ragamar ofis ga May Agbamuche-Mbu, wacce ita ce mamba mafi girman matsayi a hukumar.

Agbamuche-Mbu za ta jagoranci INEC har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban.

A cikin wasikar da aka sanya wa hannu a 3 ga Oktoba, 2025, Farfesa Yakubu ya gode wa Shugaban kasa bisa damar da aka ba shi ya yi wa kasa hidima tun daga shekarar 2015.

Kotu ta bukaci cafke shugaban INEC

A wani labarin, kun ji cewa babbar kotun tarayya mai zama a Osogbo, babban birnin jihar Osun ta zargi shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da saba umarninta.

Alkalin kotun, Mai Shari'a Funmilola Demi-Ajayi ta umarcci Sufeto Janar na rundunar 'yan sanda ya kamo Yakubu idan ya ki aiwatar da hukuncinta.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Tinubu ya umarci a rage kudin kujerar Hajjin 2026 a Najeriya

Kotun ta bai wa INEC da Yakubu kwanaki bakwai su wallafa sunayen shugabannin jam'iyyar AA a shafin yanar gizo na hukumar domin tabbaar da gaskiya da kuma cire kokwanto.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.