Zargin Kisan Kiristoci: Kungiyar CAN Ta Fadi Matsayarta kan Rade Radin a Najeriya
- Kungiyar Kiristoci ta Najeriya, CAN ta yi magana kan zargin da ake yadawa cewa ana kashe mabiyanta wanda ya jawo maganganu
- CAN ta karyata zargin cewa ana kisan Kiristoci, tana cewa hare-haren ‘yan ta’adda bai shafi addini ba kwata-kwata sabanin yadda ake yadawa
- Jami’in CAN ya ce kasashen waje na amfani da halin tsaro don siyasa, ya bukaci ‘yan Najeriya su kai korafi majalisar dokoki, ba Amurka ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar
Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, ta yi karin haske kan rade-radin cewa wai ana kashe mafi yawan Kiristoci a Najeriya.
Kungiyar ta karyata rahotannin da ke cewa ana kisan kare dangi kan Kiristoci a Najeriya, kamar yadda wasu ‘yan kasashen waje ke yadawa.

Source: Facebook
Jami’in kungiyar, Abimbola Ayuba shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da hadimin Bola Tinubu, Dada Olusegun ya wallafa a shafin X a yau Talata 7 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin kisan Kiristoci a Najeriya ya jawo maganganu
A baya-bayan nan, wani dan wasan barkwanci na Amurka, Bill Maher, da kuma Sanata Ted Cruz, sun zargi gwamnatin Najeriya da kisan Kiristoci.
Yayin wata ganawa, Maher ya ce Kiristoci na fuskantar zalunci daga ‘yan ta’adda wanda ake kokarin shafe su daga doron kasa.
Wannan zarge-zarge ya jawo suka daga bangarorin kasar inda wasu ke ganin ana neman ta da rigima ne a Najeriya da cewa dukan addinan biyu na fuskantar kashe-kashe.

Source: Facebook
Martanin CAN kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
Sai dai kungiyar CAN ta ce, gaskiya ba haka take ba, domin hare-haren da ake yi a Najeriya ba su da tsarin addini, inda ta ce har Musulmi na mutuwa yayin sallar Asuba ko a masallatai.
Ayuba ya ce ba wai ana kisan Kiristoci kadai ba, domin ‘yan ta’adda suna kai hari ne a kasuwanni, gidaje, da wuraren ibada ba tare da bambancin addini ba.

Kara karanta wannan
Hankali ya kwanta: Babban alkawari da Tinubu ya yi ga Kiristocin Arewacin Najeriya
Ya kara da cewa akwai kasashen waje da ke amfani da halin rashin tsaro domin cimma muradunsu, yana mai gargadin ‘yan Najeriya da kar su rika biyewa kasashen waje, saboda hakan kan jawo wa kasa cikas.
Ayuba ya jaddada cewa maimakon su kai kuka Amurka, ya kamata su kai bukatunsu ga majalisar dokoki ta Najeriya, domin duk wata takura daga kasashen waje za ta shafi kowa – Musulmi da Kirista.
Zargin kisan Kiristoci: Majalisa za ta buga muhawara
A baya, mun ba ku labarin cewa majalisun Najeriya za su dawo domin ci gaba da aikin samar da dokokin da za su kawo ci gaban kasa da kuma tattauna wasu batutuwa na musamman.
Daga batutuwan da za a saka a gaba shi ne yadda wasu tsirarun mutane a kasashen waje, musamman Amurka ke cewa an taso kiristocin Najeriya a gaba da yi musu kisan kiyashi.
Sanata Ali Ndume da wasu Sanatoci sun dauki nauyin kudurin domin kare sunan kasar a idon duniya bayan yada jita-jitar da ke neman farraka Najeriya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
