Kotu Ta Rufe Asusun Kamfanin Jiragen Sama kan Zargin Hannu a Badakalar NNPCL
- Binciken da hukumar EFCC ke yi kan almundahana a kamfanin mai na kasa (NNPC) ya tabo kamfanin jiragen sama
- Babbar Kotun Tarayya ta amince da bukatar rufe asusun kamfanin Mars Aviation Ltd a bankin Fidelity na dan lokaci
- An dauki matakin ne domin ba jami'an EFCC damar bincike mai zurfi kan wasu kudi da aka ga sun shiga asusun daga NNPCL
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bada umarnin rufe asusun kamfanin sufurin jiragen Mars Aviation Ltd a bankin Fidelity Bank Plc na ɗan lokaci.
Kotun ta dauki wannan matakin ne bisa zargin asusun da alaka da badakalar karkatar kudade a Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL).

Source: Getty Images
Mai shari’a Musa Liman ne ya bayar da wannan umarni, bayan lauyan hukumar EFCC, Geraldine Ofulue, ta shigar da bukata kan wannan batu, in ji rahoton 21st Century Chronicle.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta rufe asusun kamfanin Mars Aviation Ltd
Ofulue ta shaida wa kotu cewa an fara bincike kan asusun kan zargin hannu a almundahana, bisa haka ta roƙi kotu da ta ba da umarnin garkame shi har sai an kammala bincike.
Bayan sauraron bukatar, Mai shari’a Liman ya ce bukatar da hukumar EFCC ta shigar tana da hujja, don haka ya amince da ita.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, duk da cewa umarnin an bayar da shi tun ranar 22 ga Satumba, an ga takardar tabbatarwa a ranar Litinin.
Hukukar EFCC ta shigar da bukatar rufe asusun a kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1299/2025, da ta shigar ranar 1 ga Yuli, 2025.
Abubuwan da EFCC ta bukata daga kotu
A cikin bukatar, hukumar ta nemi a ba Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ko wani jami’i da aka amince da shi izinin tura umarnin rufe asusun ga daraktan Fidelity Bank.
EFCC ta kuma bayyana lambar asusun, 5250350283 (C03651082) mai suna: Mars Aviation Limited, cewar rahoton The Nation.
A shaidar da ya bayar don goyon bayan bukatar, wani mai bincike na EFCC daga sashen ayyuka na musamman, Abdulganiyu Olayide, ya ce tawagarsu aka dora wa alhakin wannan bincike.
Abin da binciken hukumar EFCC ya gano
Olayide ya bayyana cewa EFCC ta samu bayanan sirri cewa NNPCL ya biya kamfanin sufurin jiragen sama na Mars Aviation Ltd wasu kuɗi kan kwangiloli na bogi.
Ya ce binciken ya gano cewa NNPCL ya aika wa kamfanin kuɗaɗe masu yawa a cikin asusun a lokuta daban-daban.

Source: Twitter
Ya ƙara da cewa samun umarnin kotu na rufe asusun zai ba da damar ci gaba da bincike tare da hana duk wata mu’amala da za a yi da kuɗin.
Olayide ya ce wannan bukatar ta wucin gadi ce kawai domin a adana kuɗin a asusun har sai an kammala bincike.
EFCC ta sake gurfanar da tsohon Minista
A wani labarin, kun ji cewa hukumar EFCC ta kara gurfanar da tsohon Ministan Wuta da Karafa, Dr. Olu Agunloye, a gaban kotu.
EFCC ta mayar da shi gaban babbar kotun birnin tarayya da ke Apo, Abuja, bisa zargin aikata laifuffuka bakwai da suka shafi karɓar rashawa.
Sai dai tsohon ministan ya musanta aikata duka laifuffukan da aka karanto masa a zaman kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Jude Onwuegbuzie.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


