Rarara da Amaryarsa Sun Sanya Labule da Tinubu, an Ji Abin da Suka Tattauna

Rarara da Amaryarsa Sun Sanya Labule da Tinubu, an Ji Abin da Suka Tattauna

  • Shahararren mawaki a Arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara da matarsa sun kai ziyara fadar shugaban kasa Abuja domin nuna goyon bayansu
  • Yayin ziyarar, Rarara da amaryarsa sun gana da Bola Tinubu inda suka nuna goyon baya ga shugabancinsa a Najeriya da kuma matakan da ake dauka
  • Rarara ya yabawa Tinubu kan jagorancinsa da kokarin hade ‘yan kasa wuri guda don zaman lafiya da cigaba wanda ya ba shi tabbacin goyon

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Mawakin siyasa a Arewa, Dauda Kahutu Rarara, tare da matarsa Hajiya Aishatu Humaira, sun kai ziyarar ban girma ga Bola Ahmed Tinubu.

Rarara da amaryarsa sun nuna matukar goyon baya ga Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, GCFR, a fadar shugaban kasa Abuja.

Rarara da amaryarsa sun gana da Tinubu
Hotunan Bola Tinubu, Rarara da maryarsa a fadar shugaban kasa. Hoto: @ishaqsamaila5.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa a bangaren siyasa, Ishaq Samaila ya wallafa a yau Talata 7 ga watan Octobar 2025 a shafin X.

Kara karanta wannan

Bayan rage kudin Hajji, Tinubu ya ba malamin Musulunci kyautar babbar mota

Gudunmawar da Rarara ya ba Tinubu, APC

Rarara na daga cikin mawaka a Arewacin Najeriya da suka ba jam'iyyar APC gudunmawa tun bayan kirkirarta a 2014.

Wasu na ganin Rarara ma ya fi kowa ba da gudunmawar saboda tun lokacin mulkin Muhammadu Buhari ake fafatawa da shi har yanzu.

Bayan saukar Buhari daga mulki, Rarara ya juyo da wake-wakensa ga Bola Tinubu da mukarrabansa wanda ya sake daga kimar APC.

Rarara ya yabawa salon mulkin Tinubu
Rarara da amaryarsa yayin ganawa da Tinubu a Abuja. Hoto: @ishaqsamaila5.
Source: Twitter

Rarara, amaryarsa sun gana da Tinubu

A cikin sanarwar, hadimin ya ce Rarara da amaryarsa sun gana da shugaban ne a fadar Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja.

Ziyarar ta kasance cike da farin ciki da girmamawa, inda Rarara wanda shahararren mawaki ne kuma jagoran wayar da kan jama’a ya yaba wa Shugaba Tinubu.

Ya kwararawa Tinubu yabon ne bisa gudunmawarsa wajen jagoranci mai hangen nesa, mulki na adalci da kokarinsa wajen hade kan al’umma da cigaban kasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya koma ofis, ya dawo birnin Abuja bayan kwashe kwanaki a Legas

Kalaman Tinubu ga Rarara game da gudunmawarsa

A nasa bangaren, Shugaba Tinubu ya gode wa Rarara bisa rawar da yake takawa wajen fadakar da jama’a ta hanyar waka da al’adu.

Ya bayyana shi a matsayin mawaki mai kishin kasa wanda wakokinsa ke karfafa bege da hadin kai tsakanin ‘yan Najeriya.

Taron ya kara karfafa dangantaka tsakanin fannin fikira da gwamnati, wanda ke nuna yadda wannan gwamnati ke daraja al’adu da fasaha a matsayin ginshikin gina kasa.

Rarara ya ce zai kayar da Atiku a zabe

A wani rahoton, mun ba ku labarin cewa mawaki Dauda Kahutu Rarara ya ce ko shi ma idan ya tsaya takara zai iya kayar da 'yan adawa gaba ɗaya a zaɓen 2027 mai zuwa.

Mawakin ya zargi shugabannin haɗaka a ADC da gazawa, yana mai cewa talakawa ba za su sake amincewa da su ba duba da dukansu mayaudara ne a kasa tun tuni.

Kahutu Rarara ya kare Bola Tinubu, yana mai cewa ya gaji kasar da marigayi Muhammadu Buhari ya lalata tun da ya rufe iyakoki da sauran matakai marasa kan gado.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.