NAHCON Ta Fitar da Sanarwa kan Umarnin Rage Kudin Hajjin 2026 da Tinubu Ya Yi

NAHCON Ta Fitar da Sanarwa kan Umarnin Rage Kudin Hajjin 2026 da Tinubu Ya Yi

  • Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta gode wa Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, bisa umarnin rage kuɗin Hajjin 2026
  • Hakan na zuwa ne bayan an umarci hukumar da ta sake duba farashin cikin kwanaki biyu domin sauƙaƙa wa maniyyata yin ibadar a bana
  • NAHCON ta ce matakin shugaba Tinubu ya nuna gwamnatinsa na sauraron ƙorafe-ƙorafen jama’a tare da samar da sauƙin rayuwa ga Musulmai

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana godiyarta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, bisa rage kuɗin aikin Hajjin shekarar 2026.

Wannan na zuwa ne bayan taron da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Litinin, inda Shettima ya bayar da umarnin a rage kuɗin cikin kwana biyu.

Kara karanta wannan

Shettima ya ba da mamaki da ya kira Sanusi II da Sarkin Kano a taro a Abuja

Shettima, Shugaban NAHCON da Bola Tinubu
Kashim Shettima, Shugaban NAHCON da Bola Tinubu. Hoto: Kashim Shettima|Jibwis Nigeria|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan sanarwar da NAHCON ta fitar ne cikin wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun a makon da ya gabata ne hukumar NAHCON ta sanar da kuɗin aikin Hajji na 2026, inda maniyyata daga Arewa za su biya N8.2m yayin da na Kudu za su biya N8.5m.

NAHCON ta yaba da kulawar Tinubu

A wata sanarwa da jami'ar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, hukumar ta ce umarnin shugaba Tinubu na rage kuɗin Hajji alama ce ta gwamnati na sauraro da kulawa da jama’arta.

Leadership ta wallafa cewa hukumar ta ce:

“Wannan mataki ya nuna fahimtar gwamnati game da ƙalubalen tattalin arzikin da Musulmai ke fuskanta wajen shirye-shiryen zuwa aikin Hajji.”

Fa’idar biyan kuɗin Hajji da wuri

Bayan taron da aka yi a Fadar Shugaban Ƙasa karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ma’aikata, Alhaji Ibrahim Hadeja, an fadi fa'idar biyan kudi da wuri.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Shugaba Tinubu ya umarci a rage kudin kujerar Hajjin 2026 a Najeriya

An jaddada cewa biyan kuɗi da wuri zai taimaka wajen cin gajiyar ƙara darajar da Naira ta yi a yanzu da kuma rage tasirin hauhawar farashi.

Mataimakin shugaban kasa, Shettima a wani taro
Mataimakin shugaban kasa, Shettima a wani taro. Hoto: Kashim Shettima
Source: Twitter

NAHCON ta bayyana cewa wannan matakin ya nuna yadda gwamnatin Tinubu ke kula da al’amuran da jin daɗin jama’a, musamman a bangaren addini.

Fa'idar rage kudin aikin Hajji

Hukumar ta bayyana cewa wannan matakin zai ba ta damar shawo kan ƙalubalen da take fuskanta wajen shiryawa aikin Hajji tare da inganta tsari na gaskiya da samar da sauƙi.

NAHCON ta ce za ta yi aiki kafada da kafada da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da aiwatar da umarni rage kudin yadda ya kamata.

Hukumar alhazai ta yi kira ga maniyyata da su hanzarta biyan kuɗinsu kuma za a sanar da sabon farashin nan ba da jimawa ba.

Tinubu ya ba limami kyautar mota

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya yi kyautar mota ga babban limamin jihar Oyo.

Mutane da dama sun yaba da kyautar da shugaban kasar ya yi wa malamin, suna cewa lamarin ya yi matukar dacewa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fara binciken Ganduje, an jero zunuban da ake tuhumarsa da su

Sai dai wasu masu sharhi sun bayyana cewa hakan bai dace ba domin jin tsoron kyautar ta kasance siyasa ce zalla.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng