'Yan Bindiga Sun Karbe Ikon Kananan Hukumomi a Kwara? Gwamnati Ta Yi Bayani

'Yan Bindiga Sun Karbe Ikon Kananan Hukumomi a Kwara? Gwamnati Ta Yi Bayani

  • Gwamnatin Kwara ta yi karin haske kan wasu maganganun da ke cewa 'yan bindiga sun mamaye wasu kananan hukumomi a jihar
  • Ta zargi 'yan adawa a ciki da wajen jihar kan yada labarai na karya dangane da batun matsalar rashin tsaro
  • Gwamnatin ta kuma nuna yatsa ga Peter Obi kan yada abubuwan da ba haka suke ba dangane da rashin tsaron jihar a shafukan sada zumunta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kwara - Gwamnatin jihar Kwara ta bayyana cewa babu wani yankin jihar da ke karkashin ikon ‘yan bindiga.

Gwamnatin ta zargi fitaccen ɗan siyasa, Peter Obi, da amfani da shafinsa wajen yaɗa labaran karya kan halin tsaro a jihar.

Gwamnatin Kwara ta yi bayani kan rashin tsaro
Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq da shugaban sojojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede. Hoto: Abdulrahman Abdulrazaq, HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta ce gwamnatin ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da kwamishiniyar yaɗa labarai ta jihar, Mrs. Bolanle Olukoju, ta sanyawa hannu.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya aika da muhimmin sako ga mutanen Borno kan Boko Haram

Gwamnatin Kwara ta yi bayani mai gamsarwa

An fitar da sanarwar ne domin fayyace gaskiyar maganganun da ake yadawa cewa kananan hukumomi tara na jihar suna karkashin ikon ‘yan bindiga.

"Muna son sanar da jama’a cewa maganganun da ake yadawa cewa kananan hukumomi tara a jihar Kwara suna karkashin hare-haren ‘yan bindiga ba gaskiya ba ne."
"Babu wani yanki a jihar da ke karkashin mamayar ‘yan bindiga.”

- Bolanle Olukoju

Gwamnatin ta kara da cewa kalubalen tsaro da ake fuskanta a wasu 'yan kaɗan din yankuna, ba su kai ga irin wannan karyar da mummunan jita-jita da ‘yan adawa ke yadawa ba.

"Muna da cikakken dalilin zargin cewa waɗannan mutane - 'yan adawa a ciki da wajen jihar sune ‘yan yaɗa labaran karya a yanar gizo."
"Waɗanda ke kokarin tsoratar da jama’a ta hanyar kirkirar labaran da ba su da tushe, kamar cewa ‘yan bindiga suna yawo a yankin karamar hukumar Asa.”

Kara karanta wannan

'Ka ba mu dama': Mutanen Sokoto sun tura sako ga Tinubu kan harin ƴan bindiga

- Bolanle Olukoju

An nuna yatsa ga Peter Obi

Gwamnatin ta bayyana cewa abin takaici ne ganin yadda Peter Obi ya bari shafukansa na sada zumunta, suka zama hanyar yada irin wadannan labaran karya, tana mai cewa hakan bai dace da matsayinsa na dattijon kasa ba.

"Muna roƙon Mr. Peter Obi da ya goge wannan rubutu saboda karya ne kuma bai dace ba.”

- Bolanle Olukoju

Haka kuma, gwamnatin ta yi kira ga jama’a da su guji yada labarai marasa tabbas, saboda hakan na iya haifar da firgici, rudani, da tashin hankali a cikin al’umma, rahoton tashar Channels tv ya zo da zancen.

Gwamnatin Kwara ta karyata Peter Obi
Taswirar jihar Kwara, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original
"Irin wannan dabi'a mara kyau karawa jami’an tsaro wahala, alhali suna kokari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a."

- Bolanle Olukoju

'Yan bindiga sun sace basarake a Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan bindiga sun tilasta mutane barin gidajensu, garuruwa 17 sun zama kufai

'Yan bindigan sun yi awon gaba da Hakimin kauyen Rani da ke karamar hukumar Patigi a yayin harin da suka kai.

Miyagun 'yan bindigan sun kuma hallaka wani fasto na cocin ECWA bayan sun karbi kudaden fansa masu kauri daga hannun iyalansa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng