Jama'an Gari Sun Taimaki 'Yan Sanda, An Fatattaki Mayakan Boko Haram a Borno
- ‘Yan Sanda da jami'an sa-kai na JTF sun yi igiyar gwaji wajen fatattakar harin Boko Haram a Banki, Borno.
- Babban jami'in 'dan sanda (DPO) na garin ya ki tserewa, har ya jagoranci kare al’ummar garin yayin harin
- Gwamna Babagana Zulum ya sake maido da al’ummomi uku zuwa Banki kuma ya sha alwashin tsare garin.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Yan Sanda da ƙungiyar tsaron farar hula (JTF) sun taka rawar gani yayin da su ka yi arangama da mayakan kungiyar ta'addancin Boko Haram.
Hadin jami'an da 'yan gari sun samu nasarar fatattakar Boko Haram da ta kai hari a kan sansanin soja a garin Banki, karamar hukumar Bama, jihar Borno.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wasu daga cikin mazauna garin sun yi ta yabawa baturen 'yan sanda na garin saboda tsaya wa da ya yi a aka fafata a lokacin da Boko Haram ta kai harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram: 'Dan sanda ya tsaya da mutanensa
Rahotanni daga yankin sun bayyana cewa a lokacin da ‘yan ta’adda suka kai hari, an kira Baturen 'dan sandan a kan ya tsere amma ya ki.
Mazauna garin sun ce ya shirya ‘yan sanda da jama’a su ka yi tsayin daka su ka ba ofishin ‘yan sanda da kuma tashar hukumar kwastam da ke kan iyaka da Kamaru tsaro.
A cewar jama'a, wasu sojoji, sun tsere zuwa Kamaru yayin harin, amma DPO ya kira mutane da su tsaya, yana cewa:
“Idan muka bar garin nan, ina za mu koma?”
Mazauna garin sun ce hakan ya nuna karfin gwiwa da ƙwazo wajen kare kai da garin su har Allah Ya ba su nasara.
Ana zargin sojoji sun tsere a Borno
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa sojojin sun ji tsoron adadin ‘yan ta’adda da aka ce suna zuwa Banki, wanda ya sanya su a cikin tashin hankali.
Ya bayyana cewa sun fara samun rahoton cewa mayakan Boko Haram sun taho kai masu hari, amma aka ba su tabbacin cewa an aiko jirgin sojin kasar nan ya taya su yakin.

Source: Facebook
Wani soja ya bayyana wa jaridar cewa:
“Sun ci gaba da gaya wa Kwamanda da ya yi hakuri, wai jirgin yakin sojojin sama na kan hanyarsa don korar su. Sai da mu ka kai makura, sannan ya ba mu umarnin mu fafata da su."
“Mun gode wa Allah da ya tsare rayuwarsa, domin ya yi ƙoƙarin kwace bindiga daga hannun ‘yan ta’addan, amma sun fi mu yawa. Ranar kuwa duhu ya yi sosai har mutum ba zai iya gane wanda ke kusa da shi ba."
Boko Haram ta kona gidan basaraken Borno
A wani labarin, mun wallafa cewa Sarkin Kirawa da ke karamar hukumar Gwoza a jihar Borno, Abdulrahman Abubakar, ya dauki matakin kare rayuwarsa saboda harin Boko Haram.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana cewa babu wani zaɓi da ya rage masa bayan da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai masa hari illa ya tsere zuwa makwabtan kasar nan domin tsira.
Sarkin ya ce hare-haren Boko Haram sun tsananta matuka a garin, wanda hakan ya tilasta masa da sauran mazauna garin su ka sauya matsuguni a cikin tsananin firgici.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


