Abu Ya Girma: Batun Takarar Jonathan a Zaben 2027 Ya Je gaban Kotu
- Hasashen da ke yi cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, zai yi takara a zaben 2027 bai yi wa wani lauya dadi
- Lauyan ya garzaya gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ya gabatar da wasu bukatun da yake so a biya masa
- Daga cikin bukatun akwai neman kotun ta hana Dr. Jonathan sake yin takara a zaben shugaban kasa na 2027
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - An shigar da kara a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja kan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.
An shigar da karar ne don hana Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a 2027 ko nan gaba a Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce wani lauya mai suna Jonmary Jideobi ne ya shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/2102/2025, a gaban kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace bukata aka nema a gaban kotu?
Johnmary Jideobi ya nemi kotu ta bayar da umarnin da zai hana Jonathan gabatar kansa ga kowace jam'iyya don takarar shugaban kasa a 2027 ko nan gaba.
Lauyan ya kuma roki kotu ta hana hukumar zaɓe ta INEC karɓa ko wallafa sunan Jonathan a matsayin ɗan takara, tare da neman babban lauyan gwamnati (AGF) ya tabbatar da bin umarnin kotun.
An saka hukumar INEC da AGF a matsayin na biyu da na uku cikin waɗanda ake kara, jaridar The Punch ta tabbatar da labarin.
Lauyan ya kafa hujjar cewa Jonathan ya riga ya kammala iyakar wa’adin mulki biyu da doka ta kayyade, bayan ya gaji marigayi Umaru Musa Yar’Adua a 2010 sannan ya ci gaba da mulki bayan nasararsa a zaɓen 2011.
A cewarsa, ya shigar da karar ne bayan ya karanta rahotanni a kafafen yaɗa labarai cewa Jonathan na iya shirin sake tsayawa takara a 2027.
Ya jingina hujjarsa da sashe na 137(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya, yana mai cewa barin Jonathan ya sake tsayawa takara zai zama karya tsarin doka.
An rantsar da Jonathan har sau biyu
Lauyan ya tunatar da cewa an rantsar da Jonathan a ranar 6 ga Mayu, 2010, don kammala wa’adin marigayi Shugaba Yar’Adua, wanda ya rasu a ranar 5 ga Mayu, 2010.

Source: Facebook
Daga bisani ya lashe zaɓen 2011 kuma aka rantsar da shi a ranar 27 ga Mayu, 2011, inda ya yi mulki har zuwa 2015.
“Ina sane cewa idan wanda ake kara na farko (Jonathan) ya ci zaɓen shugaban kasa na 2027, wanda zai kare a 2031, hakan zai wuce shekaru takwas da kundin tsarin mulki ya amince shugaban kasa zai yi a ofis."
- Johnmary Jideobi
Meyasa aka shigar da kara kan Jonathan?
Ya kara da cewa karar da ya shigar ta kasance don kare muradun jama’a, yana neman kotu ta ayyana cewa Jonathan bai cancanci sake tsayawa takarar shugaban kasa ba, kuma INEC ba ta da ikon karɓar sunansa ko wallafa shi a matsayin ɗan takara.
Haka kuma, ya roki kotu ta ba da umarni ga AGF da ya tabbatar da aiwatar da duk wani hukunci da kotun za ta yanke a kan lamarin.
“Zai kasance cikin maslahar adalci idan wannan kotu mai girma ta amince da bukatun da ke cikin wannan karar."
- Johnmary Jideobi
Har yanzu ba a saka ranar sauraron karar ba.
Oshiomwhole ya ba Jonathan shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Edo, Sanata Adams Oshiomwhole, ya yi kira da babbar murya ga Goodluck Jonathan.
Sanata Oshiomwhole ya shawarci da kada ya fito takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Tsohon gwamnan ya bayyana makiyan tsohon shugaban kasan ne kawai za su ba shi shawarar ya sake fitowa takara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


