Yanayin da Aka Gano Gawar Wata Budurwa, Fatima Salihu Ya Tada Hankulan Mutane a Bauchi

Yanayin da Aka Gano Gawar Wata Budurwa, Fatima Salihu Ya Tada Hankulan Mutane a Bauchi

  • An shiga rudani bayan gano gawar wata budurwa yar shekara 24, Fatima Salihu Mohammed a harabar Kwalejin Fasaha ta Bauchi
  • Rundunar yan sanda ta kaddamar da bincike domin gano abin da ya yi sanadin mutuwar Fatima daga fita gida
  • Mahaifin Fatima ya bayyana cewa diyarsa ta bata ne bayan ta fita gida da nufin zuwa sayen kayan miya a Birshin Filani

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Rundunar ‘Yan Sanda ta Bauchi ta fara bincike kan mutuwar wata budurwa mai suna Fatima Salihu Mohammed.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori, ya bayar da umarnin gudanar da bincike na musamman domin gano yadda lamarin ya faru.

Jihar Bauchi.
Hoton taswirar jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta tattaro cewa mai magana da yawun rundunar, CSP Ahmed Wakili, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Bayan rage kudin Hajji, Tinubu ya ba malamin Musulunci kyautar babbar mota

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Fatima ta bar gida a Bauchi

Tun farko dai an gano gawar Fatima ne a cikin gonar da ke cikin harabar Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, ta hannun wani manomi.

A cewar rundunar yan sanda:

“A ranar 25 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na safe, rundunar ta samu rahoton cigiyar wata budurwa da ta ɓace daga wani mutum mai suna Salihu Mohammed Chimo, mai shekaru 62.
"Mutumin, mazaunin unguwar ma’aikatan kwaleji, ya kai rahoton cewa a ranar 24 ga Satumba, da ƙarfe 10:00 na safe, diyarsa Fatima Salihu Mohammed, mai shekaru 24, ta fita sayen kayan miya a Birshin Fulani, amma bata dawo gida ba.”

An gano gawar Fatima a Kwalejin Fasaha

Bayan samun rahoton, rundunar yan sanda ta tura tawagar masu bincike, ciki har da kwararru kan sa ido da fasahar gano mutane domin gano inda ta shiga.

"A ranar 29 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 12:30 na rana, an samu kira daga Sarkin Birshin Fulani, wanda ya sanar da cewa wani matashi, Bashar Adamu ya gano gawar mace."

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke a Majalisar Wakilai a yunƙurin tsige shugaban marasa rinjaye

"An ce matashin na aiki a gonar masara ta mahaifinsa da ke cikin harabar Kwalejin Fasaha, sai ya ji warin gawa. Da ya duba, sai ya gano gawar mace da ta fara ruɓewa.

Tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin CSP Yahaya Yunusa, DPO na ‘E’ Division, suka je wurin kuma suka killace yankin.

Sannan suka tabbatar cewa gawar dai ta kasance ta Fatima Salihu Mohammed da ake ta nema a yan kwanakin da suka gabata.

Rundunar yan sanda ta ce an gano gawar tare da jakunkunta da kuma kayan miya da ta saya kafin ɓacewarta.

'Yan Sandan Najeriya.
Hoton dakarun Rundunar Yan Sandan Najeriya a cikin motar sinitri. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Yan sanda sun fara gudanar da bincike

Daga nan aka kai gawar zuwa asibitin Kwalejin Fasaha, inda likita ya tabbatar da mutuwarta. Daga bisani kuma aka mika ta ga iyalanta domin shirye-shiryen jana’iza.

Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Sani-Omolori Aliyu, ya kafa kwamitin kwararru domin gudanar da cikakken bincike cikin tsari, cewar Daily Post.

Matar aure ta kona gaban kanwar mijinta

A wani labarin, kun ji cewa 'yan sanda sun kama matar aure, Zuwaira Hassan bisa zargin cusankarfe mai zafi a al'aurar kanwar mijinta a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama matashin da ake zargi da sace basarake a Kano, ya fara kiran sunaye

Ana zargin matar ta yi amfani da wani cokalin karfe da ya dauki zafi bayan ta sanya shi a wuta, ta kona wasu sassan al'aurar yarinyar 'yar shekara 10.

Yayin binciken, yan sanda, matar ta amsa laifinta, inda ta ce ta aikata hakan ne bisa umarnin wata mai maganin gargajiya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262