Jam'iyyun Siyasa Sun Cin Ma Matsaya kan Nada Sabon Shugaban Hukumar INEC
- Ana ci gaba da tattauna batun wanda zai gaji Farfesa Mahmood Yakubu a shugabancin hukumar INEC
- Jam'iyyun siyasa sun nuna damuwarsa kan ikon da shugaban kasa yake da shi na nada shugabannin hukumar zaben
- Sun kawo shawarae da suke ganin za ta zama hanyar tabbatar da adalci wajen nada shugabannin INEC na kasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam'iyyun siyasa da ke da rajista karkashin majalisar Inter-Party Advisory Council (IPAC), sun yi magana kan nada sabon shugaban hukumar INEC.
Kungiyar ta nemi a kafa sabuwar hukuma mai zaman kanta wacce za ta riƙa naɗa shugaban INEC, kwamishinoni da sakatare na hukumar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa shugaban IPAC na kasa, Dakta Yusuf Mamman Dantalle, ne ya gabatar da wannan bukata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakta Yusuf Mamman Dantalle ya gabatar da bukatar ne yayin wani taron tattaunawa tsakanin shugabannin jam’iyyun siyasa da kwamitin majalisar wakilai kan yi wa kundin tsarin mulki garambawul, a ranar Litinin a Abuja.
Me jam'iyyun siyasa suka ce kan INEC?
Shugaban na IPAC wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Dipo Olayoku, ya ce tsarin yanzu da ake amfani da shi wanda shugaban kasa ke nada shugaban INEC, ya take 'yancin da hukumar ke da shi.
Dakta Yusuf Mamman Dantalle ya ce lokaci ya yi da za a cire ikon naɗa shugaban INEC daga hannun fadar shugaban kasa, domin tabbatar da adalci da ‘yancin hukumar daga tasirin siyasa.
“Don tabbatar da rashin son rai a INEC, ya kamata a cire ikon nada shugabanta daga hannun gwamnatin tarayya."
"A kafa kwamitin nadi mai zaman kansa wanda zai kunshi wakilan dukkan jam’iyyun siyasa, kungiyoyin fararen hula, majalisar shari’a ta kasa da wakilan majalisar dokoki ta kasa."
- Dakta Yusuf Muhammad Dantalle
Ya kara da cewa irin wannan tsarin da ke haɗa bangarori daban-daban zai kara aminci da gaskiya wajen zaɓen shugabancin INEC, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar da labarin.
Wannan matsaya ta IPAC ta yi daidai da kiran tsofafffin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, waɗanda suka dade suna neman sauye-sauye don tabbatar da sahihin tsarin zaɓe.
Wa'adin Mahmood Yakubu ya kusa karewa
Ana wannan tattaunawa ne a daidai lokacin da wa’adin Shugaban INEC na yanzu, Farfesa Mahmood Yakubu, ke gab da karewa kafin karshen shekarar nan.

Source: Twitter
Mahmood Yakubu, wanda ya jagoranci zaɓukan 2019 da 2023, ya yi wa’adi biyu, kuma ana ta hasashe game da wanda zai gaje shi.
Da yake ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai nemi wa’adi na biyu a 2027, masana siyasa na ganin cewa wanda za a naɗa a matsayin sabon shugaban INEC zai taka rawar gani wajen tabbatar da sahihin zaɓe a zaben gaba.
Kotu ta umurci cafke shugaban INEC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata kotun tarayya da ke zamanta a Osogbo jihsr Osun, ta ba da umurnin a cafke shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu..
An bada umarnin cafke Farfesa Mahmood Yakubu ne ga Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbrtokun, bisa zargin raina umarnin kotu.
Mai shari'a Funmilola Demi-Ajayi, ce ta ba da umarnin yayin yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar AA da hukumar INEC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


