Labari Mai Dadi: Shugaba Tinubu Ya Umarci a Rage Kudin Kujerar Hajjin 2026 a Najeriya
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugabannin Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) a fadar shugaban kasa yau Litinin
- Matimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda ya wakilci Tinubu ya ba da umarnin rage farashin kowace kujerar Hajjin 2026
- Sakataren NAHCON ya ce za su yi duk mai yiwuwa su rage kudin Hajji saboda fatansu kowane Musulmi ya samu damar sauke farali
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin rage kudin kowace kujerar Hajjin badi ta shekarar 2026 ga musulman Najeriya.
Shugaban Tinubu ya umurci Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) da ta fito da sabon jadawalin farashi kujerar Hajjin 2026 cikin kwana biyu.

Source: Facebook
Tinubu ya ce a rage kudin Hajjin 2026
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya isar da wannan umarni ga hukumar NAHCON a wani taro da ya jagoranta a Aso Rock, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ministan Tinubu zai fito bainar jama'a kan zargin amfani da digirin bogi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima ya bukaci a hada kai tsakanin jami’an gwamnatin tarayya da na jihohi, ciki har da gwamnoni, wajen tsara sabon farashin kujerar hajji .
Haka kuma ya ja hankalin masu ruwa da tsaki da maniyyata su biya kudin hajji da wuri domin mika su Babban Bankin Najeriya (CBN) ta yadda za a samu nasarar aikin ba tare da tangarda ba.
Dalilin ragewa musulmai kudin Hajjin 2026
Da yake magana da ’yan jarida bayan taron, Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Sanata Ibrahim Hadejia, ya ce taron ya gudana ne domin karasa shirin Hajjin 2026, musamman batun kudin kujera.
Ya bayyana cewa manufar gwamnati ita ce saukaka wa maniyyata kudin da za su biya, la’akari da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki.
"Darajar Naira na ci gaba da farfadowa a kasuwar canji sakamakon tsare-tsaren da gwamnati ta kawo.
"Mataimakin shugaban kasa na ganin idan mahajjata sun biya Naira miliyan 8.5 zuwa 8.6 a bara da Naira ta yi mummunar faduwa, yanzu da ta farfado ya kamata a samu sauki.

Kara karanta wannan
Labari mai dadi: Sheikh Abdullahi Pakistan ya samo wa musulmin Najeriya sauki a Hajjin 2026
- Sanata Ibrahim Hadejia.
NAHCON ta hango amfanin rage kudin Hajji
Shi ma Sakataren Hukumar NAHCON, Dr Mustapha Mohammad, ya bayyana cewa umarnin Shugaban Kasa zai ƙara yawan maniyyatan da za su samu damar zuwa sauke farali.
A ruwayar jaridar Guardian, Dr. Mustapha ya ce:
"Wannan labari mai dadi, yanayin arahar kujerar Hajji yanayin yawan musulman da za su daura niyyar zuwa sauke farali.
"Don haka, kamar yadda aka ba mu umarni, za mu yi aiki tuƙuru daga yau zuwa gobe domin rage kuɗin kowace kujera yadda kowa zai iya biya.
"Za mu rage kudin ya yi araha ta yadda kowane musulmi zai samu damar zuwa sauke daya daga cikin ginshikan addinin musulunci."

Source: Getty Images
NAHCON ta samo ragin N19bn a Hajjin 2026
A wani labarin, kun ji cewa shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya samu nasarar samo ragi ga mahajjatan Najeriya a Hajjin badi.
Bayan tattaunawa da hukumomin Saudiyya, Farfesa Abdullahi ya ce san rage akalla N200,000 kan kowace kujerar Hajjin Najeriya.
Ya ce baya ga wannan ragin kuɗi, NAHCON ta kammala wasu daga cikin shirye-shiryen Hajjin 2026, inda aka riga aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
