Wata Sabuwa: Ministan Tinubu Zai Fito Bainar Jama'a kan Zargin Amfani da Digirin Bogi
- Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan zargin Ministan Kimiyya da Fasaha, Cif Uche Nnaji da amfani da takardun digiri da NYSC na bogi
- Wannan ya sa Ministan ya kira taron manema labarai a babban birnin Tarayya Abuja yau Litinin, 6 ga watan Oktoba, 2025 domin kare kansa
- Tun farko, binciken da aka shafe shekaru biyu ana yi ya bankado cewa satifiket na digirin UNN da ministan ke amfani da shi na bogi ne
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, zai fito bainar jama'a ya yi jawabi a yau Litinin, 6 ga Oktoba 2025, kan zargin da ake masa na amfani da takardun bogi.
Idan ba ku manta ba a yan kwanakin nan, an fara rade-radin cewa Nnaji na amfani takardar shedar kammla digiri da ta bautar kasa watau NYSC na bogi.

Source: UGC
Hakan na cikin wani rahoton bincike da jaridar Premium Times ta fitar ranar Asabar da ta gabata, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda Minista ya gabatar da takardun bogi
Binciken da aka gudanar tsawon shekaru biyu, ya gano cewa Nnaji ya gabatar da takardun bogi ga Shugaba Bola Tinubu da majalisar dattawan Najeriya lokacin da ake tantance shi a matsayin minista a 2023.
Tuhumar amfani da takardun bogi ta faro ne tun a watan Yuli 2023, lokacin da Shugaba Tinubu ya hada sunan Nnaji a cikin jerin ministoci 28 na farko da aka tura majalisar dattawa.
Tun lokacin ake zargin Nnaji bai kammala jami’a ba, kuma takardar digirin da ya gabatar da takardar kammala NYSC da aka kai ofishin Shugaban Kasa, ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Hukumar DSS da kuma majalisar dattawa duk na bogi ne.
Sakamakon binciken da aka yi ya tabbatar da hakan, inda aka bayyana a fili cewa takardun digiri da NYSC da ke hannun ministan na bogi ne gaba daya

Kara karanta wannan
Uche Nnaji: Ministan Tinubu da ake zargi da amfani da takardun bogi, ya fito ya yi bayani
Nnaji ya shirya magana da manema labarai
A jiya Lahadi, ministan ya amince cewa Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) bata taba ba shi takardar shaidar kammala digiri ba.

Source: Twitter
Bayanai sun nuna cewa Nnaji zai yi magana kan lamarin a taron manema labarai a yau Litinin, 6 ga watan Oktoba, 2025 a Abuja.
An samu kwafin gayyatar taron manema labarai da ke nuna Uche Nnaji zai yi jawabi kan batun da karfe 2:00 na rana, a cibiyar Raw Material Research and Development Council da ke unguwar Maitama, Abuja.
ADC ta soki Tinubu kan rike Uche Nnaji
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar hadaka watau ADC ta tsoma baki kan zargin da ake yi wa ministan Shugaba Bola Tinubu na yin amfani da takardun bogi.
ADC ta ce ba abin mamaki ba ne da Shugaba Tinubu ya ci gaba da rike Ministan kimiyya da fasaha, Uche Nnaji duk da zarge-zargen da ke kansa.

Kara karanta wannan
An bazo wa Minista wuta, Hadimin Atiku ya bukaci Shugaba Tinubu ya tsige shi nan take
A cewar ADC, rashin daukar mataki cikin gaggawa kan lamarin ya nuna cewa gwamnatin Tinubu na amince da harkokin rashawa da rashin gaskiya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
