Ana Wata ga Wata: ASUU Ta Fara Tattaro kan Malamai, za a Rufe Jami'o'in Najeriya

Ana Wata ga Wata: ASUU Ta Fara Tattaro kan Malamai, za a Rufe Jami'o'in Najeriya

  • ASUU ta fara wayar da kan mambobinta yayin da take shirye-shiryen tsunduma yajin aikin kasa baki daya a mako mai zuwa
  • Kungiyar ta ce gwamnatin tarayya ta ki daukar wani matakin a zo a gani game da jerin bukatunta duk da gargadinta na mako biyu
  • Farfesa Chris Piwuna, ya ce tsawon shekaru takwas gwamnati ke jan kafa kan bukatunsa, yana mai fadin shirin da suka yi wannan karo
  • Sanusi Ya'u Mani, wakilin daliban Hakimin Mani , ya shaidawa Legit Hausa cewa akwai bukatar a samar da mafita ta dindindin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya (ASUU) ta tsananta shirye-shiryen tsunduma yajin aikin kasa baki daya.

Za a shiga yajin aikin ne bayan ASUU ta zargi gwamnati da yin shiru kan bukatun ta duk da gargadin da ta sha yi a baya.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, ASUU ta tsunduma yajin aiki a dukkanin jami'o'in Najeriya

Kungiyar ASUU ta shirya tsunduma yajin aikin kasa baki daya
Hoton shugaban kungiyar ASUU, Chris Piwuna da tambarin ASUU. Hoto: @ASUU_UNILAG
Source: Twitter

Kungiyar ASUU ta shirya shiga yajin aiki

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mako guda kafin fara yajin aikin, ASUU ta fara wayar da kan malaman jami’o’i domin tabbatar da cikakken hadin kai.

A cewar kungiyar, gwamnatin tarayya ta nuna halin ko-in-kula da bukatunta duk da cewa an aika mata da takardar gargaɗi tun daga 28 ga Satumba, 2025.

A cikin takardar, ASUU ta ce za ta fara yajin aikin gargadi na makonni biyu, sannan ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani idan babu wata hobbasa daga gwamnati.

Amma a sabuwar wasika da shugaban kungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ya aikawa dukkan rassan ASUU, a ranar 5 ga Oktoba, 2025, ya ce yanzu za a shiga yajin aikin gama-gari ne kawai.

A cewar sanarwar Farfesa Piwuna:

“Majalisar zartaswa ta kasa (NEC) ta ASUU ta yanke shawarar ba gwamnati kwanaki 14 don ta aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla tun watan Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan

Ana batun zargin kisan Kiristoci, yan bindiga sun yi ta'asa a masallacin Katsina

"Idan ta gaza cika alkawurran da ta dauka, za mu fara yajin aiki na makonni biyu kafin mu shiga cikakke da ba tare da iyaka ba.”

Ya ce an riga an sanar da Ministan Kwadago, Maigari Dingyadi, da ministan ilimi da kuma kungiyar kwadago ta kasa (NLC).

“Ba wani ci gaba da gwamnati” — ASUU

Shugaban kungiyar ya bayyana cewa duk da shekaru takwas na tattaunawa, babu wani ci gaba da za a iya cewa an samu daga bangaren gwamnati, inji rahoton Tribune.

“Yanzu muna cikin makon ƙarshe na gargaɗin da muka bayar. Mun yi haƙuri sosai, amma gwamnati ba ta nuna niyyar warware matsalolin ba, don haka ba mu da zabi sai na shiga yajin aiki kai tsaye."

- Farfesa Chris Piwuna.

Ya ce manufar yajin aikin yanzu ita ce tilasta gwamnati ta sanya hannu da aiwatar da sabuwar yarjejeniyar da suka kulla, tare da gyara tsarin jami’o’in Najeriya don su dace da ka’idodin duniya.

ASUU ta zargi gwamnatin tarayya da kin biyan bukatun kungiyar na tsawon lokaci.
Hoton Shugaba Bola Tinubu da shugaban ASUU, Chris Piwuna. Hoto: @officialAVAT, @ASUU_UNILAG
Source: Getty Images

ASUU ta nemi haɗin kan malaman jami'o'i

Farfesa Piwuna ya umurci mambobin kungiyar da su kasance tsintsiya madaurinki ɗaya a cikin wannan fafutukar, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Durkusa wa wada: Gwamnatin Tinubu ta roki ASUU, ta dauki sabon alkawarin hana yajin aiki

“Muna da ƙarfi idan mun shirya tare, amma muna rauni idan muka zargi juna. Duk wani mamba ya saurari jagoransa kawai kuma ya halarci taron ƙungiya don samun sabbin bayanai.”

Ya jaddada cewa wannan yajin aikin ba sabon abu ba ne, domin ASUU tana yin haka don kare muradun malamai da inganta tsarin ilimin jami’a a ƙasar.

Ya kamata a samar da mafita ta dindindin

A zantawar Legit Hausa da Sanusi Ya'u Mani, wakilin daliban Hakimin Mani a jihar Katsina, ya ce akwai bukatar a samar da mafita ta dindindin.

Sanusi Ya'u Mani ya ce:

"Ba na tunanin wannan yajin aikin na gargadi an shige shi don cutar da tsarin karatu, ya fi kama da tunatarwa ga gwamnati kan cika alkawuran da ta dauka tun da dadewa.
"Ya kamata gwamnati ta gane cewa jinkiri wajen biyan hakkokin malamai da inganta jami’o’i yana rage musu kwarin gwiwa, kuma yana lalata ingancin karatu.
"Ita kuma ASUU ta gane cewa abin da hakuri bai bayar ba, rashin hakuri ba zai samar da shi ba, kawai ta ci gaba da tattaunawa da gwamnati domin kada dalibai su sake zama wadanda rikicin zai fi shafa."

Kara karanta wannan

Zargin takardun bogi: Za a maka hadimin ministan Tinubu da ya yi murabus a kotu

Sanusi Ya'u ya ce abin da ake nema a yanzu shi ne mafita mai dorewa, saboda yajin aiki kadai ba zai magance matsalolin jami'o'i gaba daya ba.

"Ina rokon gwamnati da ASUU su zauna teburin tattaunawa cikin gaggawa, domin ceton tsarin ilimi da makomar matasan Najeriya."

- Sanusi Ya'u Mani.

Sakon ASUU ga dalibai da iyaye

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ASUU ta gargadi dalibai da iyaye kan tsaikon karatu da za a iya fuskanta idan ta shiga yajin aikin kasa baki daya.

Kungiyar malaman jami'o'in ta zargi gwamnatin tarayya da kin aiwatar da yarjejeniyar 2009, tana mai cewa gwamnati ce abar zargi idan ilimi ya tabarbare.

ASUU ta bukaci 'yan Najeriya da ka da su ga laifinsu a abin da zai faru, su tuhumi gwamnatin tarayya idan har ilimi ya lalace a nan gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com