Jerin Mutanen da Dangote Ya Yi Wa Godiya bayan Sasanta Rigimarsa da PENGASSAN

Jerin Mutanen da Dangote Ya Yi Wa Godiya bayan Sasanta Rigimarsa da PENGASSAN

  • Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya gode wa Bola Tinubu bisa sasanta rikicinsa da PENGASSAN
  • Dangote ya gode wa wadanda suka taimaka wajen kawo karshen wannan matsala a wata sanarwa da matatarsa ta fitar yau Litinin
  • Wannan dai na zuwa ne bayan sasanta rikicin matatar Dangote da kungiyar manyan ma'aikatar mai da gas ta PENGASSAN

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Matatar Dangote ta bayyana godiyarta ga shugabannin Najeriya da wasu jami’an gwamnati bisa rawar da suka taka wajen kawo karshen rikicinta da kungiyar ma'aikatan mai da gas (PENGASSAN).

Idan ba ku manta ba rigima da ta shiga tsakanin bangarorin biyu ta kusa kawo cikas a harkokin matatar mai ta hamshakin dan kasuwa, Aliko Dangote.

Dangote da Shugaba Tinubu.
Hoton Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da attajiri, Aliko Dangote a Aso Rock. Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Bayan sasanta rikicin, matatar ta mika godiya ga duka wadanda suka shiga tsakani a wata sanarwa da rukunin kamfanonin Dangote ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun fadi mutanen da ke son durkusar da matatar Dangote

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dangote ya gode wa Tinubu da Ribadu

A cikin sanarwar, matatar ta yaba matuka da irin shiga tsakani da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi ta hannun ministocinsa da manyan jami’ai na gwamnati.

Sanarwar ta ce, daga cikin jami’an gwamnati da suka taka rawar gani wajen dakile yunkurin PENGASSAN akwai shugabannin tsaro na kasa, wadanda suka hada da:

  • Mai ba Shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu
  • Darakta Janar na Hukumar DSS, Mr. Adeola Toyin Ajayi
  • Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri, NIA, Mr. Mohammed Mohammed.

Ministoci 4 da Dangote ya yi wa godiya

Haka kuma, sanarwar ta gode waa wasu ministocin da ta ce sun yi aiki tukuru, har cikin dare, domin tabbatar da cewa ba a samu cikas a harkokin makamashin Najeriya ba.

Sun hada da:

  • Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Dr. Mohammed Dingyadi
  • Ministan Kudi da Harkokin Tattalin Arziki, Wale Edun
  • Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Bagudu
  • Karamin Ministan Kwadago da Ayyukan Yi, Hon. Nkeiruka Onyejeocha.

Kara karanta wannan

Tayin da matatar Dangote ta yi wa PENGASSAN kan ma'aikatan da ta kora

Sakon Dangote ga 'yan Najeriya

Matatar Dangote ta kara da cewa tana matukar godiya ga daukacin al’ummar Najeriya da suka nuna goyon baya ga manufarta.

A cewarta, muryoyin ‘yan kasa a kafafen yada labarai da ko’ina cikin kasar nan sun kara mata kwarin gwiwa matuka

Alhaji Aliko Dangote.
Hoton shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote. Hoto: @Dangotegroup
Source: Getty Images

A karshe, kamfanin Dangote ya sha alwashin ci gaba da aiki domin amfanin al’ummar Najeriya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Ya kuma kudiri aniyar kare muradun yan Najeirya daga ‘yan neman riba ba bisa ka’ida ba, masu yi wa tattalin arziki zagon kasa da kuma masu cin moriyar kasa ba tare da cancanta ba.

Dangote zai kafa kamfanin taki a Habasha

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kamfanin Dangote Group, Alhaji Aliko Dangote, ya kaddamar da ginin masana’antar takin zamani a birnin Gode na kasar Habasha.

Masana’antar, wacce za ta kasance ta hadin gwiwa tsakanin Dangote Group da hukumar zuba jari ta Habasha, za ta rika samar da ton miliyan uku na taki a kowace shekara.

Kara karanta wannan

PENGASSAN da hukumomin Najeriya 3 da matatar Dangote ta yi fada da su a shekara 2

Firaministan Habasha, Abiy Ahmed, ya bayyana masana’antar a matsayin wata alama ta hadin kai da ci gaban kasa, inda ya ce za ta kawo sauyi ga al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262