Ganduje: Mamallaka Tashar Tsandauri Sun Fito da Bayanai a kan Gwamnatin Kano

Ganduje: Mamallaka Tashar Tsandauri Sun Fito da Bayanai a kan Gwamnatin Kano

  • Mamallaka tashar tsandauri ta Kano sun yi bayani a kan ko gwamnatin Kano ta na da hannun jari bayan an sayar masu da ita
  • Sun yi martani ne a kan rahoton da ya bayyana yadda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta mallaka wa yaran tsohon gwamna hannun jari
  • Sun ce a lokacin da su ka sayi tashar, sun yi binciken kwakwaf, amma sun zargi wanda ya kafa tashar Ahmad Rabi'u da rufa-rufa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sababbin masu tashar tsandauri ta Dala da ke jihar Kano sun musanta rahoton da ya danganta gwamnatin jihar Kano da mallakar kaso a tashar.

A cewar su, sun sayi tashar ne a shekarar 2020 daga hannun Ahmad Rabiu, wanda ya ce shi ne cikakken mamallakinta, kuma babu wani abu da ya nuna gwamnatin Kano na da hannu ko kaso a ciki.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya kama kansa a kan zarginsa da takardun karatun bogi

Masu tashar tsandaurin Kano sun ce iyalan Ganduje ba su da hannun jari a cikinta
Hoton tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Twitter

Premium Times ta wallafa cewa masu tashar nun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da suka aika mata bayan zuzzufar bincike a kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin almundahana a tashar tsandaurin Kano

Mamallaka tashar sun kuma zargi Ahmad Rabiu, wanda ya kafa kamfanin, da kirkirar takardun bogi da ke nuna ‘ya’yan tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje na da hannun jari a kamfanin.

Sun kara da cewa sai da su ka duba bayanai daga hukumar CAC kafin sayen tashar, amma ba su samu sunan gwamnatin Kano a matsayin mai hannun jari ba.

Kamfanin ya kuma ce gudummawar da gwamnatin Kano ta bayar — irin su tituna, ruwan sha da lantarki — an ɗauke su a matsayin gudunmawarta ba matsayin mai hannun jari ba.

Rahotanni sun bayyana cewa tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya mallaka wasu kaso na kamfanin zuwa hannun ‘ya’yansa a boye.

Babu gwamnati a mallakar tashar tsandaurin Kano

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama matashin da ake zargi da sace basarake a Kano, ya fara kiran sunaye

Mamallaka tashar a yanzu sun bayyana cewa gwamnati ta ba da kwangilar aikin gina ababen more rayuwa da darajarsu ta haura Naira biliyan 2.3.

Wannan sauyi ya cire gwamnatin Kano daga cikin masu hannun jari ko wani kaso da ke nuna cewa su na da iko a gudanar da tashar.

Sai dai a sabon tsarin mallakar kamfanin da aka tabbatar da shi a CAC a Oktoba 2022, an nuna cewa Abubakar Bawuro ne ke da 80% na hannun jari, yayin da Ahmad Rabiu ke da 20%.

Ana zargin Ahmad Rabi'u da hada takardun bogi a kan yaran Ganduje
Hoton tsohon Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Twitter

Kamfanin ya ce babu wata takarda da ke nuna cewa gwamnatin Kano ko wani daga cikin dangin Ganduje sun taba kasancewa a matsayin masu hannun jari ko daraktoci a hukumance.

Kamfanin ya zargi Rabiu da lalata harkar kasuwanci da kuma haddasa hasarar kudi kafin sayar da tashar, inda bayan ya sayar masu kuma ya nemi ya sayi 20% na hannun jari.

Amma a martaninsa, Ahmad Rabi'u ya bayyana cewa babu yadda zai ruguza ko jawo makarkashiya ga abin da ya kafa da hannunsa.

Gwamnatin Kano ta fara binciken Ganduje

Kara karanta wannan

Abin Fashewa ya tarwatse a tsakiyar kananan yara a cikin birnin Kano, ya yi barna

A baya, kun ji cewa Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Kano (PCACC) ta tabbatar da fara bincike kan tsohon Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Hukumar ta dauko wannan sabon bincike ne bayan wani rahoto da ke alakanta gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje da yaran tsohon gwamnan da mallakar hannun jari ba bisa ka'ida ba.

Ana zargin an karkatar da sama da Naira biliyan huɗu ta hanyar wasu kwangiloli da aka bayar a lokacin mulkin Ganduje, wanda hakan ke ɗauke da alamar cin hanci da almundahana.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng