Ana Barazanar Shigar da Gwamnoni 36 da Wike Kotu kan Kudin Tallafin Mai
- SERAP ta umurci gwamnonin jihohi 36 da Nyesom Wike, su bayyana yadda suka kashe kudin da suka samu daga tallafin man fetur
- Kungiyar ta yi barazanar cewa za ta dauki matakin shari’a idan ba su fitar da cikakken bayani ba cikin kwanaki bakwai masu zuwa
- Baya ga haka, SERAP ta bukaci hukumomin yaki da rashawa irin ICPC da EFCC su sa ido kan yadda ake amfani da kudin domin kaucewa karkatarwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kungiyar SERAP ta yi kira ga gwamnonin jihohi 36 da ministan Abuja, Nyesom Wike, su fitar da cikakken bayani kan yadda aka kashe kudin da ake raba musu.
Kungiyar tana bukatar bayani ne kan kudin da suka samu daga asusun rarraba kudi na FAAC bayan cire tallafin man fetur.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa SERAP ta ce an kiyasta cewa jihohi da Abuja sun karbi kusan Naira tiriliyan 14 daga irin wadannan kudi tun daga tsakiyar shekarar 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta ce duk da kudin da suka samu amma babu wani canji da ake gani a fannin ilimi, lafiya da walwalar talakawa.
SERAP ta bukaci bayani daga gwamnoni
A cikin wasikar da ta aika ranar 4 ga Oktoban 2025, kungiyar ta ce akwai bukatar gaggawa ga gwamnonin su fayyace wuraren da aka aiwatar da ayyukan da kudin ya tafi.
SERAP ta ce akwai bukatar jama’a su san yadda ake amfani da kudin da aka samu bayan cire tallafin man fetur.
Kungiyar ta bayyana cewa
“Akwai babban hadari na karkatar da kudin da aka samu daga rabon FAAC zuwa aljihun wasu mutane.”
Ta kara da cewa yawancin jihohi ba su fitar da cikakken bayani ba kan yadda suke amfani da kudin, kuma hakan yana ci gaba da jefa talakawa cikin matsin tattalin arziki.
An nemi ICPC da EFCC su sa ido
SERAP ta bukaci jihohi da FCT su gayyaci hukumomin ICPC da EFCC domin sa ido a yadda ake kashe kudin don tabbatar da gaskiya da bin doka.
Ta ce:
“Sanin gaskiya a yadda ake kashe kudin zai tabbatar da cewa ba a maimaita halin da talakawa ke ciki na shan wahala sau biyu – na cire tallafi da rashin amfanin kudin ba.”
Kungiyar ta gargadi gwamnonin cewa zata kai kara kotu idan ba su bi umarninta ba cikin kwanaki bakwai bayan karbar wasikar.

Source: Facebook
Kungiyar SERAP ta yi magana kan talauci
Kungiyar ta ce duk da karuwar kudin da ake rabawa jihohi a FAAC, miliyoyin ‘yan Najeriya har yanzu suna fama da talauci, rashin albashi da rashin samun ayyukan gwamnati.
Ta bayyana cewa
“Ma'aikata a jihohi da dama suna ci gaba da bin gwamnati bashi, yayin da wasu ke kashe kudi wajen sayen motocin alfarma da yawon kasashen waje.”
Abba ya biya tsofaffin kansilolin Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin Abba Kabir Yusuf ta biya tsofaffin kansiloli wasu hakkokinsu.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta cigaba da biyan tsofaffin ma'aikata da suka biyo jihar bashi a baya.
Sai dai wani abu da ya jawo hankalin jama'a a Kano shi ne yadda wasu tsofaffin kansiloli suka ziyarci Sanata Barau Jibrin a lokacin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


