A Mako 1 kacal, Farashin Gas ɗin Girki Ya Ƙaru da N7,500 a Legas da Wasu Jihohi
- Farashin da ake cika 12.5kg na gas din girki ya tashi daga ₦17,500 zuwa ₦25,000 a cikin mako guda kacal a Najeriya
- 'Yan Najeriya sun nuna matukar damuwa kan yadda aka samu sauyin farashin, inda wata ta ce zai shafi sana'arsu kai tsaye
- Dillallan gas na girki, sun bayyana yadda rikicin Dangote da PENGASSAN ya jawo karanci da tsadar gas din a karamin lokaci
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Farashin tukunyar gas ɗin girki mai cin 12.5kg ya tashi zuwa ₦25,000 daga ₦17,500 da aka sayar da shi a makon da ya gabata.
Masana na ganin cewa ƙarin farashin gas ɗin girki, zai sake jefa 'yan Najeriya a mawuyacin hali, yayin da fetur ya ƙi sauka zuwa N820.

Source: Getty Images
Gas din girki ya kara tsada a Najeriya

Kara karanta wannan
Sabon albashi: An shiga farin ciki yayin da gwamna ya fara biyan ma'aikata N104000
Rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar da cewa yanzu ana sayar da 1kg na gas ɗin girki tsakanin ₦1,500 zuwa ₦2,000.
Wannan ƙarin farashi ya jawo ƙorafi daga masu amfani da gas din girki, musamman a birnin Legas da yankin Kudu maso Yamma.
An kuma rahoto cewa an rufe da dama daga cikin tashoshin sayar da gas din girkin saboda rashin isasshen kaya, lamarin da ya tilasta masu saye yawo daga wuri zuwa wuri.
Tashin gas ya taba masu abinci
Amina Lawal daga Kaduna, a zantawarta da Legit Hausa ta ce ta yi mamakin yadda farashin gas din ya karu, tana mai cewa:
"Idan ban manta ba, a satin da ya gabata, na sayo 11.5kg a kan ₦12,650 (wanda ke nufin ₦1100 kan duk 1kg), amma a ce wannan makon ya kara kudi har zuwa ₦2000.
"Mu da muke sana'ar sayar da abinci, kuma muke amfani da gas din sosai, mu ne muka san illar hakan, don ka ga abinci zai kara tsada tun da kayan hada shi sun kara kudi."
Tasirin yajin aikin PENGASSAN ga rarraba gas
Shugaban kungiyar dillalan gas ɗin girki ta Najeriya (NALPGAM), Mista Bassey Essien, ya bayyana cewa wannan hauhawar farashin ya samo asali ne daga yajin aikin PENGASSAN.
“Matatar Dangote ce mafi girman mai samar da gas ɗin girki a cikin gida a yanzu. Rikicin PENGASSAN ya kawo tsaiko a rarraba kaya, lamarin da ya sa gas din ya yanke, kuma ya jawo tsadarsa."
- Mista Bassey Essien.
Ya kara da cewa da zarar an kammala warware rikicin, farashin gas din girki zai iya daidaituwa a cikin kwanaki masu zuwa.

Source: Getty Images
Ƙoƙarin Dangote da NLNG na samar da gas
A cewar shugaban kamfanin Dangote Group, Aliko Dangote, matatar ta na samar da ton 2,000 na gas ɗin girki a kowace rana, kuma tana shirin ƙara yawansa domin biyan bukatun ƙasa baki ɗaya.
“Idan masu rarraba gas ba su rage farashi ba, za mu sayar kai tsaye ga 'yan Najeriya, domin mutane su daina amfani da itace da fetur wajen girki,” in ji Dangote.
Kafin shigar matatar Dangote cikin kasuwar gas din girki, kamfanin NLNG Limited ne ke samar da mafi yawan gas ɗin da ake amfani da shi a gidaje.
Farashin fetur ya ki sauka a gidajen mai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan kasuwa sun ki sauke farashin fetur a gidajen mansu duk da cewa matatar Dangote ta rage nata farashin zuwa N820.
Dangote ya ce ya sauke farashin lita zuwa N820 tare da raba fetur kyauta ga dillalai domin su sauke nasu farashin, amma da alama, hakarsa ba ta cimma ruwa ba.
Yayin da MRS a Legas ya rage farashin zuwa N841, an ce akwai gidajen man Heyden da Ardova da ke sayar da lita sama da N865.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

