'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kusa da Barikin Sojojin Najeriya, an Rasa Rayuka

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kusa da Barikin Sojojin Najeriya, an Rasa Rayuka

  • An kashe mutane huɗu, an kuma jikkata yaro mai shekara 14 yayin da 'yan bindiga suka kai hari kusa da barikin sojoji a Lagos
  • Shaidu sun ce maharan sun zo wurin taron matasa ne da misalin karfe 9:00 na dare, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi
  • Rundunar ‘yan sandan Lagos ta kama mutane biyar da ake zargi da hannu a harin, wanda aka ce rikicin kungiyoyin asiri ne

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Mutane huɗu sun rasa rayukansu yayin da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta a wani wurin wasan snooker a daren Asabar.

An rahoto cewa wurin wasan na kusa da barikin sojojin Najeriya a yankin Ojo, jihar Lagos, amma 'yan bindigar suka kai harin.

An tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun kashe mutane 4 a harin da suka kai Legas
'Yan sandan Najeriya na rangadi a kan titi. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan bindiga sun kashe mutum 4 a Legas

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe shugaban jami'an tsaro da sace mutane a Neja

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na dare, inda maharan suka bude wuta kan mutanen da ke wasa da masu kallon wasan, cewar rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidu sun ce harbin ya haifar da firgici, yayin da mutane suka fara gudu domin ceton rayukansu.

Wani mai sayar da taliyar indomie, wanda ke kusa da wurin, ya mutu nan take bayan harsashen bindiga ya same shi.

Wani mazaunin yankin da ya bayyana sunansa da Akogun, ya ce:

“Mutanen sun zo wurin da ake buga wasan snooker da misalin karfe 9:00 na dare. Wurin yana dab da barikin soja na Ojo, kuma wurin na cike da mutane lokacin.
"Sun shigo kamar wadanda suka zo buga wasa. Kafin a ankara, sai suka fito da bindigogi masu kama da AK-47 suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
"Mutane suka fara neman hanyar guduwa, yayin da harsasai suka samu wasu. Wani mai sayar da taliyar indomie shi ne mutum na farko da ya mutu."

Wasu mutane 3 sun mutu sakamakon harin

Kara karanta wannan

Bayan yi wa matar Sarki tsirara, an kama mutum 10 da zargin yunƙurin hallaka basarake

Wani jami’in ‘yan sanda da ke yankin ya tabbatar da cewa mutum ɗaya ya mutu nan take, yayin da wasu uku suka mutu daga baya, sakamakon raunukan da suka samu.

Ya kara da cewa wani yaro dan shekara 14 da ake zargin ya je sayen taliyar indomie shi ma ya ji rauni bayan harsashe ya same shi.

Jami'in ya ce:

“Da safe, wasu suka zo suka ba da rahoton cewa ‘yan uwansu da aka harba sun mutu. Jimillar mutanen da suka mutu daga harin sun kai huɗu yanzu."
'Yan sanda sun cafke mutane 5 da ake zargi da kai hari a kusa da barikin sojojin Legas
Taswirar jihar Lagos da ke a Kudancin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargi

Sai dai rahotanni daga yankin sun nuna cewa maharan na iya kasancewa ‘yan ta’addar kungiyoyin asiri ko kuma ‘yan fashi, domin wasu mazauna yankin sun ce an yi sata yayin harin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Lagos, SP Abimbola Adebisi, ta tabbatar da cewa an kama mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin.

Ta bayyana cewa bincike na farko ya nuna cewa rikicin kungiyoyin asiri ne ya haddasa harin da ya hallaka mutane huɗu .

“An kai wasu daga cikin wadanda suka jikkata asibiti, amma an tabbatar da mutuwar mutum daya daga cikinsu a babban asibitin Badagry."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna bayan tare matafiya a Zamfara

- SP Abimbola Adebisi.

'Yan sanda sun fafata da 'yan bindiga

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sanda sun kama 'yan bindiga uku sannan sun ceto mutane 29 a ayyukan da suka gudanar a Kogi, Legas da Katsina.

A jihar Kogi, an ceto mutane 24 bayan musayar wuta da masu garkuwa da mutane, tare da kuma kama bindigogi da alburusai a wata mota.

'Yan sanda sun kuma kama masu garkuwa uku a Legas bayan sun sace wani matashi ta WhatsApp, yayin da a Katsina 'yan sanda suka ceto mutane huɗu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com