Gwamnatin Kano Ta Fara Binciken Ganduje, an Jero Zunuban da Ake Tuhumarsa da Su
- Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Kano, PCACC ta fara binciken Abdullahi Umar Ganduje
- Ana zargin Ganduje bisa zargin karkatar da sama da Naira biliyan huɗu zuwa aikin tashar tsandauri na Dala da ke jihar
- Rahotanni sun nuna cewa an cire hannun gwamnatin Kano daga cikin masu mallakar kamfanin, inda ’ya’yan Ganduje suka rike mukaman daraktoci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Bayan zargin karkatar da makudan biliyoyi a aikin tashar tsandauri a Dala, an fara binciken Abdullahi Umar Ganduje.
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Kano (PCACC) ta tabbatar da fara bincike kan tsohon gwamnan Kano domin gano bakin zaren.

Source: Facebook
Rahoton Aminiya ya bayyana cewa sama da Naira biliyan huɗu ne ake zargin an karkatar zuwa aikin ta hanyar kwangila da aka bayar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda wasu ke ganin zarge-zarge kan Ganduje
Majiyoyi sun ce an gano yadda aka mayar da wani kaso na kuɗin mallakar jihar zuwa ga iyalan tsohon gwamnan a shekarar 2020.
Saboda haka ne gwamnatin jihar ta rasa mallakar kamfanin, inda aka maye gurbin ’ya’yan Abdullahi Ganduje a matsayin daraktoci da masu hannun jari.
Wannan bincike da aka ya sake jawo maganganu kan yadda ake zargin gwamnatin Ganduje da karkatar da makudan kudi a Kano.
Duk da haka wasu na ganin bita da kulli ne na siyasa domin fakewa da zarge-zargen tsohuwar gwamnati da ake ganin ba abin da ya kamata a yanzu ba kenan.
Musabbabin binciken Ganduje kan zargin badakala
Shugaban hukumar, Saidu Yahya, ya tabbatar da cewa binciken ya samo asali ne daga koke-koken jama’a kan zargin karkatar da kuɗin jihar.
Ya bayyana cewa hukumar ta riga ta gayyaci wasu da ake zargi da hannu a lamarin, inda aka kama mutum ɗaya kuma aka sake shi bisa beli.

Kara karanta wannan
Sokoto: Ƴan bindiga sun tilasta mutane barin gidajensu, garuruwa 17 sun zama kufai

Source: Twitter
Abubuwan da binciken ya bankado kan Ganduje
Binciken ya kuma gano cewa wani daga cikin wadanda ake zargi yanzu yana zaune a Yola, Jihar Adamawa, kuma ana sa ran cafke shi nan kusa.
Saidu Yahya ya ce hukumar za ta kai shari’ar kotu da zarar ta kammala bincike domin akwai isassun shaidu da za su tabbatar da zargin, cewar TheCable.
“Bincikenmu ya kusa zuwa ƙarshe kuma za mu tabbatar an yi adalci ga jama’ar Kano bisa wannan zargi.”
- Saidu Yahya
Lamarin ya sake janyo cece-kuce a Kano, inda jama’a ke kira ga gwamnati da ta tabbatar da gaskiya da bin doka a wannan batu.
Kungiyoyi sun taso Ganduje a gaba
A baya, mun ba ku labarin cewa shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya shiga wata matsala bayan an bukaci EFCC ta cafke shi kan cin hanci.
Kungiyoyin yaki da cin hanci sun shigar da korafi kan EFCC domin daukar mataki kan tsohon gwamnan Kano game da zarge-zargen.
Hakan na zuwa ne yayin da ake zargin Ganduje da badakalar makudan kudi lokacin da yake mulkin Kano daga 2015 zuwa 2023.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

