Tashin Hankali: An Hangi 'Yan Ta'adda Suna Tafiya a Wasu Yankuna na Jihar Neja

Tashin Hankali: An Hangi 'Yan Ta'adda Suna Tafiya a Wasu Yankuna na Jihar Neja

  • Mazauna wasu kananan hukumomin jihar Neja sun shiga firgici bayan da suka hangi 'yan ta'adda suna tafiya a yammacin Asabar
  • Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta’addar da ake zargin sun ketare tafkin Gwabtai, sun bulla a yankunan Jaluwe, Tashan-Kade da Nandubo
  • Dakarun sojoji karkashin Operation Whirl Punch da Forest Sanity, sun kara kaimi wajen kaddamar da samame don dakile barazanar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Tsoro da firigici ya mamaye mazauna wasu garuruwan kananan hukumumomin Rafi da Wushishi da ke jihar Neja a ranar Asabar.

An rahoto cewa, mazauna wadannan garuruwa sun ga wasu 'yan ta'adda dauke da makamai suna yawo a yankin a yammacin ranar.

An hango 'yan ta'dda suna tafiya a cikin ayari a wasu sassa na jihar Neja
Dakarun sojojin Najeriya suna rangadi a wani yanki na Najeriya. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

An hangi 'yan ta'adda a garuruwan Neja

A cewar rahoton Zagazola Makama, ana zargin cewa wadannan 'yan ta'addar ne suka farmaki kauyukan da ke kusa da tafkin Gwabtai.

Kara karanta wannan

Bayan yi wa matar Sarki tsirara, an kama mutum 10 da zargin yunƙurin hallaka basarake

Wasu sahihan majiyoyi sun ba da bayani cewa an hango 'yan ta'addar, wadanda suka ketare tafkin Gwabtai da tsakiyar dare, a yankin Jaluwe, Tashan-Kade da Nandubo.

Rahoton ya nuna cewa wadannan yankuna suna kan hanyar da ke zuwa Pangu-Gari, a can gabashin babban titin Tegina zuwa Zungeru.

Mazauna wadannan yankuna sun ce sun ji karar harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya tilasta iyalai da dama tserewa daga gidajensu zuwa wurin buya.

Sojoji sun kara kaimi wajen dakile 'yan ta'adda

Har zuwa karshe 9:50 na safiyar Lahadi, babu wata sanarwa daga hukumar gwamnati ko jami'an tsaro game da wannan harin.

Ba a iya tantance cewa ko an kashe mutane ko an yi garkuwa da su a yayin harbe-harben ba, amma dai an ce mutane na cikin tashin hankali.

An samu rahoto cewa jami'an tsaro da suka hada da kungiyoyin sa-kai da kuma dakarun soji da ke karkashin Operation Whirl Punch da Forest Sanity sun kara kaimi da kai samame a yankunan.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda harin 'yan bindiga ya maida wani gari zuwa kufai a Kwara

Sai dai, ana ganin cewa har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, domin 'yan ta'addar, da ake zargin suna tafiya ne a kafa, suna ci gaba da sauya hanyoyi, suna farmakar garuruwa.

'Yan gudun hijira sun roki gwamnatin Neja

Wani babban jami'in tsaro da ke da masaniya kan lamarin, ya shaida wa manema labarai cewa an tura karin dakaru daga Tegina da Zungeru domin shan gaban 'yan ta'addar.

Dakarun sojoji sun ce suna kan bin diddigin 'yan ta'addar da aka ce an gani a wasu garuruwan Neja
Taswirar jihar Neja da ke a Arewa ta Tsakiya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce rundunar sojin tana ci gaba da sa ido kan motsin miyagun, kuma sojoji za su kakkabe su kafin ma su kara yin wani yunkuri na kai hari.

"Yankin na da yawan bishiyoyi da duwatsu, sannan hanyoyinsa ba su da fari, wanda ya sanya dakaru ke shan wuya wajen kai dauki," cewar majiyar sojin.

A hannu daya kuma, an ji cewa mutanen da suke gudun hijira daga Jaluwe da garuruwan makota sun nemi gwamantin Neja ta kara kai jami'an tsaro a hanyar Tegina zuwa Zungeru.

Yayin da 'yan gudun hijirar ke rokon a samar da tsaro domin su koma gidajensu, an rahoto cewa ana ci gaba da neman 'yan ta'addar da aka gani a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Matasa sun yi zanga zangar tir da kalaman Gwamnan Kano na a cire kwamishinan 'yan sanda

Basaraken Borno ya tsere zuwa Kamaru

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sarkin Kirawa a Borno, Abdulrahman Abubakar, ya tsere zuwa Kamaru bayan Boko Haram ta ƙone fadarsa.

Sarki Abdulrahman Abubakar ya bayyana cewa babu wani zaɓi da ya rage masa da wuce ya gudu zuwa Kamaru don tsira da rayuwarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa, fiye da mutane 5,000 suka tsere Kamaru bayan hare-haren Boko Haram sun tsananta a yankin Gwoza da ke Borno.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com