An Kwayewa Minista Zani a Kasuwa kan Gabatar da Digirin Bogi ga Shugaba Tinubu da Majalisa
- Jami’ar a Najeriya ta tabbatar cewa minista a gwamnatin Bola Tinubu bai kammala karatunsa ba kuma ba ta taɓa ba shi takardar digiri ba
- Rahotanni sun gano takardun digiri da NYSC da ministan ya gabatar ga majalisa na ƙarya ne, bayan bincike mai tsawo
- Binciken ya gano cewa ministan ya fadi wasu darussa, bai kammala karatu ba, sannan takardar NYSC ɗinsa na bogi ne
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Enugu - Jami’ar Najeriya da ke Nsukka (UNN) ta nesanta kanta daga takardar digirin da minista a gwamnatin Bola Tinubu ke yawo da shi.
Jami'ar da ke jihar Enugu na zargin ministan Kimiyya da Fasaha da Kirkire-kirkire, Uche Nnaji da rashin kammala karatunsa a jami'ar kamar yadda yake yadawa.

Source: UGC
Jami'a ta musanta ba minista shaidar digiri

Kara karanta wannan
Mamman Shata da wasu fitattun mawaƙan Hausa 4 da aka karrama da digirin girmamawa
Binciken jaridar Premium Times ya tabbatar da cewa Nnaji ya gabatar da takardun digiri da NYSC na ƙarya ga fadar shugaban kasa da majalisar dattawa a lokacin da ake tantance shi.
Har ila yau, jami'ar ta tabbatar da cewa bata taɓa fitar masa da shaidar kammala karatu ba kamar yadda yake fada.
Shugaban jami’ar, Farfesa Simon Ortuanya, ya bayyana a takardar da ya aika ranar 2 ga Oktoba, 2025, cewa dukkan bayanan jami’ar sun tabbatar da cewa Nnaji bai kammala karatu a shekarar 1985 ba.
Jami'a ta barranta kanta da ministan Tinubu
Dalilin haka, jami’ar ta ce bata taɓa ba shi takardar digiri ba kuma ta barranta kanta da duk wasu takardu da zai gabatar a wasu wurare.
Hakan ya fito bayan binciken shekaru biyu da aka yi inda aka gano cewa Nnaji ya kasa haye wasu darussa kamar “Virology (MCB 431AB)”.
Har ila yau, majiyoyi sun tabbatar da cewa ministan bai sake rubuta jarabawar da aka ba shi damar sakewa ba, cewar Sahara Reporters.

Source: UGC
An binciko batun shaidar kammala NYSC
Binciken ya kuma gano cewa takardar NYSC ɗinsa ta ƙarya ce, ta na ɗauke da sa hannun wani hafsan soja da bai zama shugaban NYSC sai bayan shekaru biyu daga ranar da aka ce ya sa hannu.
A yanzu haka, jami’ar Nsukka ta tabbatar da cewa babu wani rahoton kammala karatu da sunan Nnaji, yayin da hukumar NYSC ma ta bayyana cewa babu irin wannan takarda a cikin bayanansu.
Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a fadar gwamnatin Tinubu, yayin da ake kira da a binciki ministan bisa zargin ƙirƙira takardu domin samun mukami a majalisar ministoci.
Ana zargin minista da rashin kammala NYSC
A baya, mun ba ku labarin cewa an taso sabuwar ministar fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira, Hannatu Musa Musawa, a gaba.
Ana zarginta da saɓawa tanadin kundin tsarin mulki wanda hakan ya sanya zamanta minista ya saɓa doka saboda rashin kammala bautar kasa ta NYSC.
Ƙungiyar HURIWA ta yi zargin cewa ministar tana bautar ƙasa ne a jihar Ebonyi, amma ta tsallake ta daina domin zama minista wanda a doka ba ta cancanta ba.
Asali: Legit.ng
