Dubu Ta Cika: An Kama Matashin da Ake Zargi da Sace Basarake a Kano, Ya Fara Kiran Sunaye
- Yan sanda sun kama matashi dan shekara 27 da ake zargi da hannu a garkuwa da Dagacin Garun Babba a shekarar 2023
- Matashin wanda aka fi sani da Yellow ya amsa cewa su suka sace basaraken, ya fara jero sunayen duka masu hannu a lamarin
- Rundunar Yan Sandan Kano ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Bayan tsawon shekaru biyu da faruwar lamarin, 'yan sanda sun cafke wanda ake zargi da hannu a garkuwa da Dagacin Garun Babba, Alhaji Abdulmumini Mudi Zakari.
Rundunar ‘Yan Sanda ta Kano ta tabbatar da kama wani matashi mai shekara 27 , Usman Lawan Baba, wanda aka fi sani da “Yellow”, bisa zargin hannu a sace basaraken a 2023.

Kara karanta wannan
Bayan yi wa matar Sarki tsirara, an kama mutum 10 da zargin yunƙurin hallaka basarake

Source: Facebook
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar. Kamar yadda Leadership ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yan sanda sun kama wanda ya sace basarake
Ya bayyana cewa an cafke wanda ake zargi ne a ranar 2 ga Oktoba, 2025 a garin Dakatsalle, karamar hukumar Bebeji ta Jihar Kano, bayan shekaru biyu da aikata laifin.
“An kama shi ne bisa zargin hannu a garkuwa da mutane da kuma fashi da makami da ya kunshi Dagacin Garun Babba, wanda ya faru a ranar 9 ga Agusta, 2023,” in ji sanarwar.
Idan ba ku manta ba, miyagu sun yi garkuwa da basaraken tare da sace masa kudi har ₦2,750,000, wayar Tecno Kevo 4 da agogo, kafin jami’an 'yan sanda su ceto shi.
SP Abdullahi Kiyawa ya ce wanda ake zargi ya amsa laifinsa, inda ya bayyana cewa ya samu ₦6,000 a matsayin rabonsa daga abin da suka sace.

Kara karanta wannan
Abin Fashewa ya tarwatse a tsakiyar kananan yara a cikin birnin Kano, ya yi barna
Yellow ya jero sunayen masu hannu a lamarin
Haka kuma ya fallasa sunayen wasu abokan aikinsa, ciki har da wadanda aka kashe a samamen ‘yan sanda da kuma wadanda suke hannun hukuma.
Sanarwar ta kara da cewa:
“Wanda aka kama, Usman Lawan Baba, ya amsa laifin tare da bayyana sunayen abokan harkallarsa, wadanda suka hada da: Bello Kici-Kici na kauyen Falgore, wanda yan sanda suka kashe a samame.
“Mallam Sale na karamar hukumar Gezawa, wanda shi ma aka kashe yayin wani fashi da makami. Shehu Ruwa na kauyen Gafan, wanda ke gidan gyaran hali bisa wani laifi na garkuwa da mutane.
Sauran sun hada da Ibrahim Gwanja, Sule Naye da wani mutum da ba a bayyana sunansa ba, wadanda ake ci gaba da bincike a kansu.”

Source: Twitter
Rundunar ta tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike, cewar rahoton Punch.
Kwalbar barkonon tsohuwa ta fashe a Kano
A wani labarin, kun ji cewa kwalbar barkonon tsohuwada yan sanda ke amfani da ita ta fashe a hannun yara a yankin Sharada, cikin birnin Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa yara hudu yan gida daya sun ji raunuka sakamakon fashewar kwalbar a unguwar Bakin Kwata da ke Sharada.
Tuni dai yan sanda suka kai dauki wurin da lamarin ya faru, tare da killace shi domin tabbatar da babu sauran abubuwa masu hadari.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
