Ana Shirin Sulhu da Isra'ila, Sheikh Ahmad Gumi Ya Aika Sako ga Kungiyar Falasdinawa
- Rahotanni sun tabbatar da cewa kowane bangare tsakanin Hamas da Isra'ila sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta
- Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, babban malami a Najeriya ya yi kira ga kungiyar Falasdinawa ta saki yahudawan da take tsare da su
- Malamin ya ce kungiyar Hamas na da hakki da hanyar mai tsafta ta kwato kasarta amma garkuwa da wasu fararen hula kuskure ne
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi maraba da shirin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.
Sheikh Ahmad Gumi ya bukaci kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta gaggauta sakin duka yahudawan Isra'ila da ke tsare a hannunta ba tare da wani sharadi ba.

Source: Facebook
Malamin ya yi wannan kira ga Hamas ne a wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook yau Asabar, 4 ga watan Satumba, 2025.

Kara karanta wannan
Gwamna ya lallaba ya gana da Tinubu, za a saki jagoran 'yan ta'adda da Buhari ya kama a 2021
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Gumi ya hango kuskuren Hamas
Dr. Ahmad Gumi ya ce kuskure ne babba kungiyar Hamas ta tsare mutanen Isra'ila da sunan ta na garkuwa da su.
Malamin ya ƙara da cewa kamata ya yi Hamas ta sake tsara dabaru na mayar da ƙasarsu ta asali ta hanyar abin da ya kira “amfani da tsabtaccen ƙarfi.”
Kalaman Sheikh Gumi na zuwa ne bayan da Hamas ta amince da sakin wasu ’yan kasar Isra’ila da take tsare da su a wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya.
An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza
Hamas ta dauki wannan matakin ne a shirin tsagaita wuta da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar a kwanakin baya.
Kungiyar ta kuma yi kira ga Isra'ila ta dakatar da jefa bama-bamai kan Falasdinawa a zirin gaza domin a samu zaman lafiya mai dorewa.
Tun farko dai Shugaba Donald Trump na Amurka ne ya shiga tsakani domin kawo karshen yakin da ya ki ci ya ki cinye wa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.
Isra'ila ta amince da sharuddan tsagaita wutar wanda ya kunshi sako 'yan kasarta da Hamas ta tsare.
A farko kungiyar Hamas ta yi jinkirin bayar da amsa kan shirin wanda ta kai ga Shugaban Amurka ya gindaya wa'adi, amma daga bisani ta fito ta goyi baya.

Source: Facebook
Sakon da Sheikh Gumi ya aika ga Hamas
Bayan kowane bangare ya amince da sharuddan, Sheikh Gumi ya yi kira g Hamas ta gaggauta sakin mutanen Isra'ila da ke hannunta.
Malamain ya rubuta cewa:
"To yanzu, ya kamata Hamas ta saki dukkan fararen hula da take tsare da su ba tare da gindaya wani sharadi ba. Kuskure ne garkuwa da su tun farko.
"Abin da ya kamata shi ne Hamas ta sake tsara dabarunta domin ta dawo da ƙasarta ta asali ta hanyar mai tsafta, wanda haƙƙinsu ne su yi amfani da shi don kare kansu. Sai Allah ya ba su nasara, kuma tana nan zuwa."
Sharuddan zaman lafiya a Gaza
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana shirin zaman lafiya mai matakai 20 domin kawo ƙarshen yaƙi a Gaza.
Trump ya gabatar da shirin ne a Fadar White House tare da Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu domin tsagaita wuta a Gaza.
Za a mayar da Gaza yankin da babu ƙungiyoyin ta’addanci, sannan a fara sake gina gine-gine, asibitoci, makarantu da hanyoyi domin inganta rayuwar al’umma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

