Bayan Yi Wa Matar Sarki Tsirara, an Kama Mutum 10 da Zargin Yunƙurin Hallaka Basarake

Bayan Yi Wa Matar Sarki Tsirara, an Kama Mutum 10 da Zargin Yunƙurin Hallaka Basarake

  • 'Yan sanda sun kama mutane 10 da ake zargi da shirin kashe babban basarake a Najeriya wanda ya tsira da kyar daga harin
  • An kama mutanen ne da yunkurin kisan Oba Adinlewa John, Sarkin Igoba a Akure ta Arewa a jihar Ondo
  • Kwamishinan ‘yan sanda, Adebowale Lawal, ya ce an samu bindigogi, harsasai da magungunan tsafi daga hannun wadanda ake zargi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Akure, Ondo - Rundunar yan sanda ta yi nasarar cafke wasu da ake zargi da yunkurin kisan babban basarake.

An kama mutane 10 bisa zargin shirin kashe Sarkin Igoba a Akure ta Arewa da ke jihar Ondo.

Yan sanda sun kama mutum 10 kan yunkurin kashe Sarki
Sarki Adinlewa John da Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Oba Adinlewa John, Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Yadda aka farmaki babban Sarki a Ondo

Rahoton Vanguard ta tabbatar da cewa ana zargin mutanen sun shirya makarkashiya don ganin bayan Oba Adinlewa John.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda harin 'yan bindiga ya maida wani gari zuwa kufai a Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun ce mutanen sun kutsa garin da bindigogi, adduna, takubba da magungunan tsafi suna barazana ga mazauna yankin.

An ce sun fara kai hari kan wata mata mai suna Mrs. Ogunoye Oluomo, suka ji mata rauni sannan suka karbe kayanta kafin su nufi fadar Sarki.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa:

“Oba Adinlewa John ya sha da kyar bayan kai masa farmaki da aka yi, al’ummar garin sun firgita da lamarin."
Ana zargin wasu da yunkurin kashe Sarki a Ondo
Taswirar jihar Ondo da ke Kudu maso Yamma a Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Ondo: Martanin yan sanda game da lamarin

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar, Olushola Ayanlade, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Asabar a Akure.

A cewar Ayanlade, an kama waɗanda ake zargi ne bayan wani hari da aka kai wa wata mata mai suna Mrs. Ogunoye Oluomo, da kuma yunƙurin kashe Sarkin al’ummar Igoba, Oba Adinlewa John, a ranar 2 ga Oktoba da misalin 11:30 na safe.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Tankar mai ta yi tsiya a cikin mutane ranar Juma'a, an rasa rayuka da yawa

Ya ce, a ranar da lamarin ya faru, wasu ‘yan daba dauke da makamai irin su bindigogi, wukake, da kayan sihiri, sun mamaye al’ummar Igoba da nufin haddasa tashin hankali da barna.

Kakakin rundunar ya ƙara da cewa, yayin harin, Mrs. Oluomo ta gamu da rauni mai tsanani bayan an kai mata hari tare da kwace mata kayanta.

Bayan haka, maharan suka nufi fadar Sarki Oba Adinlewa John domin kisan kai, amma ya tsira da ransa da ƙyar, cewar PM News.

“Bayan rundunar ta samu kira na gaggawa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Ondo, Adebowale Lawal, ya bayar da umarnin a aika da duka jami’an tsaro da kayan aiki zuwa yankin nan take."

- Olushola Ayanlade

Ayanlade ya bayyana cewa, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da harkokin aiki ne ya jagoranci samamen, inda aka damke mutum 10 da ake zargi da hannu a harin.

An ci mutuncin Sarki da iyalansa

A wani lamari daban, an ji cewa an kai hari kan Oba Moses Bakare, Sarkin Idogun, matarsa da ɗansa Prince Victor kafin bikin gargajiya a yankin.

Kara karanta wannan

Hare hare da kona fadarsa ya tilastawa Sarki tserewa Kamaru, mutanensa sun bi shi

Prince Victor ya ce maharan sun yi wa mahaifiyarsa tsirara da cin mutunci bayan yi musu fitsari a jikinsu.

Ya nuna raunukan da aka ji masa, inda ya ce sun sha azaba sosai kafin jami’an tsaro su isa wajen domin kawo musu dauki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.