Rashin Imani: Yadda Harin 'Yan Bindiga Ya Maida Wani Gari zuwa Kufai a Kwara

Rashin Imani: Yadda Harin 'Yan Bindiga Ya Maida Wani Gari zuwa Kufai a Kwara

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara
  • Miyagun sun kashe mutane, yin garkuwa da wasu zuwa cikin daji tare da kona gidaje masu yawa
  • Wasu daga cikin mutanen garin sun yi zargin cewa akwai wata kullalliya da jami'an tsaro suka shirya kafin harin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kwara - 'Yan bindiga sun kai wani hari ranar Lahadi, 28 ga Satumba 2025, a kauyen Oke-Ode, da ke karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara.

Harin na ‘yan bindigan ba kamar yadda aka saba gani ba, ya kasance kisan kiyashi ne da ya girgiza zuciyar al’umma.

'Yan bindiga sun yi barna a jihar Kwara
Jami'an 'yan sandan Najeriya a bakin aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce bayan kura ta lafa daga harin, an tabbatar da mutuwar akalla mutane 15.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun yi barna a garin Kwara

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna bayan tare matafiya a Zamfara

Daga cikin mutanen da suka rasu har da mafarauta, jami’an tsaro na 'yan sa-kai, ‘yan kasuwa, wani basarake, da matasa da suka fito kare al’ummarsu.

An sace mutane, an lalata gidaje baki ɗaya, yayin da daruruwan mazauna kauyen suka tsere cike da fargaba.

Mutane sun bar gonakinsu, shagunansu, da makarantu a kauyen Oke-Ode, wanda a baya ake ɗauka a matsayin gari mafi aminci a yankin Igbomina.

Abin da ya rage a garin yanzu shi ne tsoro, wanda ya zama abin da yake cikin zukatan jama'a.

Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai, Baale na Ogba Ayo, Abdulwasiu Abdulkareem, ɗan’uwansa, Fatai Abdulkareem, wani yarima daga Agunjin, Ishola Muhammed da Abdulfatai Elemosho daga Babaloma.

Sauran sun haɗa da Salaudeen Bashir daga Babaloma, Saheed daga Abayan, Olowo-Ila daga Oke-Ode, Oluode Ologomo, Oji, da Saheed Matubi, rahoton Daily Trust ya tabbatar da hakan.

An nuna yatsa kan jami'an tsaro

Wata mata mai jimamin rasa mijinta ce ta fara zargin cewa jami’an hukumar DSS suna da hannu cikin lamarin, inda ta ce sun kwace bindigogin mafarauta, sannan suka mika su ga makiyaya.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: 'Yan bindiga sun tilasta rufe makarantu 180 a Arewa

Sai dai Rafiu Ajakaye, mai magana da yawun Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya karyata zargin, yana mai cewa babu gaskiya a cikinsa.

Ya kara da cewa jami’an tsaron da ke kula da dazuzzuka suma sun musanta wannan zargi.

Mafarauta sun fafata da 'yan bindiga

Duk da haka, wani mafarauci da ya tsira da kyar, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya dage cewa an kwace musu bindigoginsu kafin harin ya faru.

Ya bayyana yadda suka yi kokarin kare kansu daga ‘yan bindigan da suka yi amfani da makamai masu karfi sosai.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Kwara
Taswirar jihar Kwara, tarayyar Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original
“Waɗannan mutanen sun zo da makamai masu karfi. Mun yi iya kokarinmu, amma sun rinjaye mu. Mun ba su wuta da wuta, amma sun fi mu yawa.”
"Wani jami’in soja ne ya kwashe yawancin bindigoginmu kafin ranar, yana cewa zai kai su gyara. Bayan ya karɓe su da alburusai, sai ya kwana a Ajase."
"Watakila ɗaya daga cikin masu kawo musu bindigogi ne ya sanar da su cewa an karɓe bindigoginmu, shi ya sa suka kawo harin da gaggawa.”
"Na yi wannan zato ne saboda tun da aka ba mu bindigogi, babu wanda ya sake kawo hari. Amma ranar da ya karɓe bindigogi da alburusan don gyarawa, sai waɗannan mutanen suka kawo hari. Wannan abu gaskiya yana da ban mamaki."

Kara karanta wannan

DSS sun kwace makaman yan sa kai kafin harin yan bindiga? Gwamnati ta magantu

- Wani mafarauci

Jami'an tsaro sun kashe dan ta'adda a Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka wani tantirin dan ta'adda a jihar Kwara.

Jami'an tsaro sun samu nasarar hallaka Maidawa ne wanda ya dade yana garkuwa da mutane, yayin wani artabu.

Hakazalika, jami'an tsaro sun yi nasarar hallaka wasu daga cikin abokan aikinsa da ke gallazawa bayin Allah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng