'Rashin Tsaro ba zai Kare Yanzu ba,' Gwamna Ya Fadawa 'Yan Najeriya Gaskiya

'Rashin Tsaro ba zai Kare Yanzu ba,' Gwamna Ya Fadawa 'Yan Najeriya Gaskiya

  • Wani gwamna a Arewacin Najeriya ya bayyana cewa rikicin ta’addanci da ya hada da ‘yan bindiga ba zai ƙare da wuri ba
  • Ya yabawa Shugaba Bola Tinubu da mai ba shi shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, bisa ƙoƙarinsu a yaki da ‘yan ta’adda
  • Gwamnan ya bayyana cewa wasu jami’an tsaro na samun kuɗi daga yaƙin, abin da ke sa wasu su kasa son ganin ƙarshen rikicin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wani gwamna daga Arewa ya bayyana a cikin wata tattaunawa ta sirri cewa, yaƙin da ake yi da ta’addanci da ‘yan bindiga na iya ɗaukar lokaci mai tsawo kafin ya ƙare.

A cewarsa, duk da ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro, matsalar tsaro ta daɗe tana cigaba.

Kara karanta wannan

Matasa sun yi zanga zangar tir da kalaman Gwamnan Kano na a cire kwamishinan 'yan sanda

'Yan bindiga yayin wani zaman sulhu
'Yan bindiga yayin wani zaman sulhu. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

A tattaunawar sirri da wakilin Vanguard, gwamnan ya bayyana damuwarsa cikin yanayi na tausayi, yana mai cewa abubuwan da ke faruwa yanzu suna da hadari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya yabawa Tinubu, Ribadu

Gwamnan ya fara da yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa tallafi da goyon bayan da yake bai wa dakarun tsaro.

Ya ce:

“Duk abin da sojoji suka nema, shugaban kasa yana amincewa kuma yana ba da kuɗi. Shugaban kasa yana son wannan yaƙi ya ƙare.”

Haka kuma, ya yabawa mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, yana mai cewa:

“Gwamnatin tarayya tana ƙoƙari sosai, musamman ofishin NSA.”

Me zai hana yakin karewa a Najeriya?

A yayin da yake bayyana gaskiyar halin da ake ciki kan yaki da 'yan ta'adda a Najeriya, gwamnan ya ce:

“Sojojinmu suna ƙoƙari amma sun gaji. Da yawa daga cikinsu sun dade a fagen yaƙi, kuma makaman da suke da su ba su da ƙarfi kamar na ‘yan ta’adda.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi kira ga 'yan Najeriya a taron da ya hadu da Sanusi II a Legas

Ya kara da cewa:

“Eh, ana kashe su ('Yan ta'adda), amma a duk lokacin da aka kashe wasu, sababbbi suna shiga cikin kungiyar. Hakan ne ke sa wannan rikici ya zama ba mai ƙarewa ne da wuri ba.”

Ya yi tambaya da cewa:

“Ta yaya mai bindigar farauta zai fuskanci wanda ke da AK-47?”
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa da Ribadu
Hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa da Ribadu. Hoto: HQ Nigerian Army|Nuhu Ribadu
Source: Facebook

Bukatar karin sojoji da ’yan sanda

Gwamnan ya jaddada cewa rundunar soji da ‘yan sanda sun yi ƙadan idan aka kwatanta da girman matsalar tsaro a ƙasar.

Ya ce dole ne a yi gaggawar daukar sababbin jami’an tsaro domin ƙara ƙarfi ga yaƙin da ake yi da 'yan ta'adda.

Fargabar cigaba da kai hare hare

Gwamnan ya bayyana damuwarsa cewa, idan ba a ɗauki matakai masu tsauri ba, wannan rikici na iya ci gaba na tsawon shekaru masu zuwa.

A cewarsa:

“Sojoji suna ƙoƙari, Shugaba Tinubu da Ribadu suna aiki tukuru, amma rikicin ya fi ƙarfin abin da ake gani.”

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Muhimman abubuwa 5 da Tinubu ya fada a jawabin ranar samun 'yanci

Ya ƙare da cewa:

“Wannan abu ba zai ƙare da wuri ba,”

An karyata alakar Buhari da Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa hadimin tsohon shugaban kasa, Bashir Ahmad ya karyata ikirarin cewa Boko Haram ta taba zabar Muhammadu Buhari a wakili.

Bashir ya bayyana cewa babu wani lokaci da kungiyar ta taba zabar Buhari ko kuma ya taba shiga tsakani saboda ita.

Ya yi martani ne bayan shugaba Goodluck Jonathan ya ce Boko Haram ta taba zabar Buhari a matsayin wakili a tattaunawar da za su yi da gwamnatinsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng