Jonathan: An Fitar da Dalilai kan Karyata Alakar Buhari da Boko Haram
- Bashir Ahmad ya ce ikirarin Goodluck Jonathan na cewa Boko Haram ta taba zabar Muhammadu Buhari a matsayin mai shiga tsakani ba gaskiya ba ne
- Hadimin tsohon shugaban kasar ya ce kungiyar ta sha yi wa Buhari barazana, tare da yin yunkurin kashe shi a Kaduna a shekarar 2014
- Baya ga harin da aka kai masa, Bashir Ahmad ya bayyana cewa shugaba Buhari bai taba shiga wata tattaunawa da gwamnati a madadin Boko Haram ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Tsohon hadimin shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya yi martani ga Goodluck Jonathan, kan maganarsa da ta danganta Buhari da Boko Haram.
Jonathan ya bayyana a wani bikin kaddamar da littafi cewa a wani lokaci, kungiyar Boko Haram ta taba zabar Buhari don ya wakilce ta a tattaunawa da gwamnatin sa.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, Bashir Ahmad ya karyata wannan batu, yana mai cewa babu wata alaka ko tattaunawa da ta taba gudana tsakanin tsohon shugaban da kungiyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammadu Buhari ya wakilci Boko Haram?
Bashir Ahmad ya bayyana cewa maganar Jonathan ta haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen yada labarai, kuma wajibi ne a fayyace gaskiya.
Ya ce, duk da cewa gwamnatin Jonathan ta bayyana aniyar tattaunawa da Boko Haram, kungiyar ba ta taba zabar Buhari a matsayin wakilinta ba.
A cewarsa:
“Shekau da mabiyansa sun yi barazana ga Buhari a kai a kai, suna kuma kin duk wata akidarsa.”
Ya kara da cewa wannan matsayi ya samu karin tabbaci daga sanarwar da tsohon kakakin Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya fitar da yammacin ranar Juma’a.

Source: Twitter
Sanarwar ta nanata cewa babu wani lokaci da Buhari ya shiga cikin tattaunawa da kungiyar Boko Haram.
Yunkurin Boko Haram na kashe Buhari a 2014
Bashir ya tunatar da cewa a watan Yuli na shekarar 2014, marigayi Buhari ya fuskanci harin bam a Kaduna, wanda aka bayyana a matsayin yunkurin kashe shi.
Ya ce hakan ya nuna cewa tsohon shugaban ma ya kasance cikin jerin mutanen da kungiyar ta tsana saboda sabanin akidunsu.
A cewarsa:
“Idan da akwai wata alaka ta tattaunawa, da ba za a kai hari ga Buhari ba, amma abin da ya faru ya tabbatar da akasin hakan.”
Maganar Buba Galadima kan lamarin
Bashir Ahmad ya kuma tuna cewa a lokacin, Buba Galadima, wanda ke kusa da Buhari, ya bayyana cewa Buhari bai taba samun wani kiran tattaunawa daga gwamnati ko kungiyar ba.
A cewarsa:
“Janar ya ce wannan magana duk jita-jita ce, kuma ba wanda ya taba tuntubarsa kai tsaye.”
2012: Me Buhari ya ce kan Boko Haram?
Jaridar Punch ta tuna cewa a shekarar 2012, an yada cewa kungiyar Boko Haram ta zabi wasu fitattun ’yan Arewa, ciki har da Buhari, don shiga tattaunawa da gwamnati.

Kara karanta wannan
Triumph: An shawarci Abba game da kalaman mataimakinsa, Sagagi kan zargin taba annabi
Amma a lokacin, Buhari ya fito fili ya nesanta kansa da wannan batu, yana zargin gwamnatin Jonathan da yunkurin shafa masa kashin kaji don dalilan siyasa.
Maganar takarar Jonathan a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa an fara magana kan yiwuwar takarar shugaba Goodluck Jonathan a zaben 2027.
Fadar shugaban kasa ta yi martani da cewa kotu ce kawai za ta iya tabbatar da sahihancin takarar Goodluck Jonathan.
Lauyoyi sun yi sabani kan ko Jonathan na da damar yin takara a 2027 bayan an rantsar da shi sau biyu a baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

