Yau shekaru 4 dai-dai da aka kaiwa Buhari harin Bam a Kaduna, karanta abinda ya faru (Bidiyo)
Zakarar da Allah ya nufa da chara; a dai-dai rana irin ta yau 23 ga watan Yuli 2014, shekaru hudu da suka wuce aka kaiwa motar shugaba Muhammadu Buhari harin Bam a unguwar Kawo, hanyar Kaduna zuwa Zariya cikin garin jihar Kaduna.
Akalla mutane 82 sun hallaka a jihar Kaduna ranan, wasu da yawa kuma sun jikkata yayinda yan kunar bakin waken suka kai harin Bam ga shugaba Muhammadu Buhari da babban malami, Sheik Dahiru Usman Bauchi.
Wannan hari ya faru ne misalin karfe 2:30 na ana bayan shugaba Buhari yayinda shugaba Buhari ya nufi tafiya Daura a karkashin gadar unguwar Kawo.
Akalla mutane 25 ne suka rasa rayukan a wannan hari kadai.
Bayan tsira daga harin, Shugaba Buhari ya bayyana abinda ya gani game da wannan hari da aka kai masa inda yace:
“Ni da kaina na shaida wani harin Bam a yau misalin karfe 2:30 na rana a hanyata na zuwa Daura.”
“Wannan abin takaici ne, kuma ko shakka babu an nufi kasheni ne. Bam din ya zo ne daga wata mota mai gudu da ta dade tana kokarin wuce motocin masu tsarina amma muka hanashi.”
“Yayinda muka kai kasuwar Kawo, sai yayi amfani da damar tsayawa da mukayi yayi kokarin buge mota na inda Bam din ya tashi wanda ya lalata dukkan motocin da muke ciki.”
“Abin takaici da na fito daga cikin motana, na ga gawawwakin mutane da dama a kasa. Wadannan mutane ne da ke harkokin gabansu kawai amma aka kashesu.
Na godewa Allah, na fito na rauni ko daya amma mutane uku daga cikin masu tsarina suna ji kananan raunuka.”
KU KARANTA: Kabilun Taraba 5 sun shiga yarjejeniar zaman lafia da Fulani
Shugaban kasa a lokacin, Goodluck Jonathan, ya godewa Allah da ya kawar da wannan mumunan hadari da ka iya kawo rugujewar kasa ga baki daya.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng