PENGASSAN da Hukumomin Najeriya 3 da Matatar Dangote Ta Yi Fada da Su a Shekara 2
- Matatar man Dangote ta fuskanci sabani da hukumomin gwamnati kan ingancin man fetur, takardun izini da samar da danyen mai
- Rigimar ba ta tsaya kan hukumomin gwamnati ba, Dangote ya kuma shiga takun saka da kungiyoyin kwadago kan sallamar ma'aikata
- A wannan rahoton, mun jero hukumomi da kungiyoyin kwadago da Dangote ya yi rigima dasu daga Mayun 2023 da tasirin hakan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Matatar man Dangote, wacce Alhaji Aliko Dangote ke jagoranta, ta zama wata babbar hanyar Najeriya na kawar da dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje.
Matatar ta na samar da dizal, fetur, man jirgin sama da sauran kayayyakin mai, kuma ta taimaka wajen rage kashe biliyoyin daloli da ake yi wajen shigo da mai daga waje.

Source: UGC
Sai dai, matatar ta fuskanci kalubale da dama daga kafuwarta zuwa yanzu, domin ta gamu da matsaloli da dama daga hukumomin gwamnati uku da 'yan kwadago, inji rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wannan rahoto, Legit Hausa ta jero hukumomi da kungiyoyin kwadago da Dangote ya yi rigima dasu daga Mayun 2023 zuwa Satumbar 2025.
Matashiya kan gina matatar Dangote
Kafin mu tsunduma cikin rahoton, bari mu fara bitar tasirin gina matatar Dangote da kuma kalubalen farko da ta fuskanta bayan fara aiki.
Rahoton BBC ya nuna cewa Alhaji Aliko Dangote ya sanar da shirin gina matatar mansa a 2013, tare da fatan canza tsarin man Najeriya gaba ɗaya.
Domin duk da albarkatun man da ƙasar ke da shi, ana shigo da sama da kashi 80 cikin 100 na mai da ake amfani da shi daga waje.
An fara aikin gina matatar ne da dala biliyan 3.3, daga bisani kudin ya kai biliyan 19, bayan an haɗa da masana’antar sinadarai da takin zamani a fili mai faɗin hektar 2,635.
A watan Satumba 2024, matatar Dangote ta fara fitar da fetur, bayan dizal da iskar jirgi. Amma ta fara fuskantar matsalar ƙarancin danyen mai a gida.
Wannan ya faru sakamakon lalacewar bututun mai da ƙarancin zuba jari, wanda hakan ya tilasta mata sayen danyen mai daga Amurka a farashi mai tsada.
Dangote ya zargi wasu masu ruwa da tsaki a harkar mai da ƙoƙarin hana matatar cin gajiyar kasuwarta, yana kiran su da “oil cabal” a turance.
Hukumomi da suka yi rigima da Dangote
Yanzu bari mu tsunduma cikin rahoton, inda za mu fara duba hukumomin gwamnati da Dangote ya yi rigima da su kan matatarsa da ke Legas:
1. Rigima tsakanin Dangote da hukumar NMDPRA
Rikicin da ya fi fice shi ne wanda ya shiga tsakanin Dangote da hukumar NMDPRA, wacce ke kula da wani bangare na ayyukan man fetur a Najeriya.
A watan Yulin 2024, shugaban NMDPRA, Farouk Ahmed, ya yi ikirarin cewa dizal ɗin da matatar Dangote ke samarwa na dauke da sinadarin sulfur mai yawa (650–1,200 ppm), fiye da ƙa’idar 50 ppm da gwamnati ta tanada daga 2025.

Kara karanta wannan
'Yan Boko Haram sun yi ta'addanci a Borno, an kona fadar basarake, an kashe mutane
Dangote ya karyata hakan, ya gabatar da rahoton gwajin dizal din matatarsa da ke nuna 87 ppm kacal, inda ya nemi ’yan majalisar tarayya su tabbatar, inji rahoton The Cable.
Ya zargi NMDPRA da karɓar rashawa daga masu shigo da 'gurbataccen dizal daga kasashen Turai da Asiya, yana mai cewa hakan ya saba wa dokar masana'antar fetur ta PIA.
Da farko, NMDPRA ta hana Dangote cikakken lasisi, lamarin da ya sa ya kai ƙara kotu, inda yake neman diyyar Naira biliyan 100, yayin da ya zargi hukumar da bada lasisin shigo da mai kasar ba bisa ka’ida ba.
A watan Yuli 2025, bayan shiga tsakani daga gwamnati, Dangote ya janye ƙarar, sannan NMDPRA da hukumar SON suka ba shi lasisi, sannan aka ci gaba da gwaje-gwaje.
2. Rikicin kasuwanci da kamfanin NNPCL
Kamfanin NNPCL, mallakar gwamnati, shi ma ya shiga cikin rigima da Dangote kan rabon hannun jari da kuma samar da danyen mai.
A 2021, NNPCL ya mallaki 20% na hannun jari a matatar, amma ya kasa biyan dala biliyan 1.76 daga cikin dala biliyan 2.76 da aka tanada. Wannan ya rage hannayen jarinsa zuwa 7.2% a 2024, inji rahoton Reuters.
Haka kuma, NNPCL ya gaza samar da ganga 300,000 zuwa 325,000 na danyen mai a rana da aka yi alkawari da shi, abin da ya tilasta wa matatar Dangote sayen mai daga kasashen waje.
A watan Oktoba 2024, NNPCL ya rasa damar mallakar hakkin saye da sayar da mai daga matatar, wanda ya ba 'yan kasuwa damar yin kasuwanci kai tsaye da Dangote ba tare da shigar kamfanin ba.
Duk da haka, yarjejeniyar sayen danyen mai da Naira aka fara a watan Oktobar 2024 ta samar da ganga miliyan 48 ga matatar.
3. Rashin tsari a ɓangaren NUPRC
Jaridar Business Day ta rahoto hukumar NUPRC da ke da alhakin tabbatar da wadatar danyen mai ga masu tacewa ta gaza cika alkawarin da dokar PIA ta tanada.
A watan Agustar 2024, Dangote ya yi kira ga hukumar da ta tabbatar da cewa matatun gida suna da fifiko wajen samun danyen mai.
Amma rashin samar da isasshen mai, da kuma raguwar fitar da mai daga ƙasar, ya sa matatar Dangote ke aikin tace kashi 50 kacal na burinta a rana.

Kara karanta wannan
Gwamna ya shiga rikicin Dangote da PENGASSAN, ya fadi abin kunyar da zai faru ga Najeriya
Hakan ya kawo tasiri ga tattalin arzikin ƙasa, inda masana suka yi kira da gwamnati ta sake duba tsarin samar da mai a cikin gida domin kare jarin da Dangote ya zuba.

Source: UGC
Rikicin Dangote da kungiyoyin kwadago
A watan Satumba 2025, ƙungiyar PENGASSAN, da ke wakiltar manyan ma'aikatan fetur da gas ta fara yajin aiki bayan Dangote ya kori ma’aikata 800 bisa zarginsu da yiwa matatarsa zagon kasa.
Yajin aikin ya shafi ofisoshin NMDPRA, NUPRC da NNPCL, tare da rage wutar lantarki da megawatt 1,000 a kasar.
Ita ma NUPENG, wacce ke wakiltar ma'aikatan fetur da gas, ta bi sahun kungiyar PENGASSAN a yin adawa da sallamar ma'aikata 800 daga matatar Dangote saboda sun shiga kungiya.
Kungiyoyin biyu sun fito fili, sun nuna takaicinsu kan yadda Dangote ya hana ma'aikata shiga kungiyoyinsu, inda suka ce hakan ya take hakkokin ma'aikatan.
Sun zargi Dangote da fifita ma'aikatan da ya dauko daga kasashen waje, kuma yana gallazawa na Najeriya, wanda ya kara rura rikicin, inji rahoton The Guardian.
Amma dai, Dangote ya dage cewa ya sallami ma'aikatan 800, wadanda duk 'yan Najeriya ne a Satumbar 2025 don yin garambawul a matatarsa.
Ma’aikatar kwadago karkashin Minista Muhammad Dingyadi ta shiga tsakani, inda ta tabbatar da dawo da ma’aikatan da aka sallama, ba tare da asarar albashi ba.
Dangote ya yi wa PENGASSAN ta yi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, sababbin bayanai sun fito kan tattaunawar da aka yi tsakanin matatar Dangote da kungiyar PENGASSAN.
Sababbin bayanai sun bayyana cewa matatar Dangote ta amince da biyan ma’aikatan da aka kora albashin shekara biyar ba tare da yin aikin komai ba.
An yi wannan tayin ne saboda damuwar da matatar ke da ita game da yiwuwar samun zagon kasa daga wasu daga cikin ma’aikatan da aka sallama.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng



