Labari Mai Dadi: Sheikh Abdullahi Pakistan Ya Samo Wa Musulmin Najeriya Sauki a Hajjin 2026
- Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya samu nasarar samo ragi ga mahajjatan Najeriya a Hajjin badi
- Farfesa Abdullahi Saleh ya kai ziyarar gaggawa Saudiyya a watan Satumba, 2025, inda ya karasa wasu shirye-shirye na aikin Hajjin 2026
- Ya ce a zaman da NAHCON ta yi da hukumomin Saudiyya, mahajjatan Najeriya za su samu ragin kudi sama da Naira biliyan 19
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman (Pakistan) ya ce su na ci gaba da kokarin samar da sauki a Hajjin badi.
Sheikh Abdullahi Pakistan ya bayyana cewa hukumar ta samu nasarar rage wa mahajjatan Najeriya kuɗi fiye da Naira biliyan 19 a shirin gudanar da aikin Hajjin 2026.

Source: Twitter
Shugaban NAHCON ya bayyana hakan ne a Kano, ranar Juma’a, bayan dawowarsa daga Saudiyya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Farfesa Pakistan ya kai ziyarar gaggawa Saudiyya a ranar 22 ga Satumba 2025 domin tattaunawa kan inganta ayyuka da kuma rage farashi ga mahajjatan Najeriya.
NACHON ta samo ragi ga 'yan Najeriya
A cewarsa, wannan nasara ta biyo bayan tattaunawa da abokan hulɗa a Saudiyya da shugabannin hukumar jin daɗin alhazai na jihohi.
Abdullahi Pakistan ya ce sun cimma matsaya ta rage wa kowanne mahajjaci fiye da N200,000 daga cikin kujeru 66,910 da aka ware wa Najeriya.
"Ba tattaunawa kadai muka yi ba, mun dawo da sakamako mai kyau. Ragin da aka samu ya yi daidai da manufar Renewed Hope ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wacce ke kokarin rage wa al’umma nauyi,” in ji Pakistan.
Ya ce baya ga wannan ragin kuɗi, NAHCON ta kammata wasu daga cikin shirye-shiryen Hajjin 2026, inda aka riga aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da dama, in ji Guardian.
NAHCON ta fara kulla yarjejeniyoyi
Daga cikin yarjejeniyoyin akwai ayyukan hidima ga alhazan Najeriya tare da kamfanin Mashariq Dhahabiyya, sufuri tare da Daleel Al-Ma’aleem da masauki da abinci a yankin Markaziyya na Madina a farashi mai sauƙi.

Kara karanta wannan
Da kusan mutane miliyan 100, Najeriya ta zama kasa ta 2 mafi yawan talakawa a Duniya
Farfesa Abdullahi ya ce NAHCON ta zauna da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya, ta gabatar da shawarwari daga darussan da aka dauka a Hajjin 2025 domin kauce masu a 2026.

Source: Facebook
Nawa ne kudin kujerar Hajjin 2026?
Dangane da farashin kujerar Hajji, Farfesa Abdullahi Usman ya ce an sanar kudin da aka yanke da wuri domin bai wa maniyyatadamar biya a kan 'okaci.
Ya kara ambatar kudin kujerar hajji mai zuwa a 2026 kamar haka;
Maiduguri/Yola – N8,118,333.67
Jihohin Arewa – N8,244,813.67
Jihohin Kudu – N8,561,013.67
NAHCON ta koka kan rashin biyan kudin Hajji
A wani labarin, kun ji cewa hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta nuna damuwa kan jinkirin biyan kuɗin aikin Hajjin 2026 daga maniyyatan da ke shirin sauke farali a badi.
Shugaban NAHCON na kasa, Farfesa Abdullahi Pakistan ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawa da Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina.
Ya ce tawagar NAHCON ta ziyarci Dikko Radda ne a matsayinsa na shugaban gwamnonin Arewa maso Yamma domin ya jawo hankalin maniyyata su biya kudi da wuri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
